← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 143

Sashe 110

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kanta kawai tayi tace."Shikkenan ai tunda kaki daukar shawara." Miqewa yay ya kama hanya ya fita, kai tsaye ya hau sabon babur dinsa wanda ya siya dubu dari biyu da hamsin, sannan yayi sabbanin d'unkuna ya kuma bibbiya bashin da ake binsa, daga haka sai kawai ya cigaba da facakarsa da kudin, dan ita kanta wacce tayi sanadiyar samuwar kudin da kyar yake bata wani abu, Naburago ya tattare kudin yayi bukatarsa dasu yanzu saura dubu dari takwas dasu yake so ya fara sanar cah-cah dan yana ganin yanda sana'ar take sanya mutane da yawa suyi mahaukanta kud'i to shima dama rashin kudi a hannu ne yasa bai fad'a harkar ba tunda yanzu ya samu dama to zai shiga a dama dashi, babur dinsa ya hau ya nufi mahad'arta su.
*****
'Bangaran 'Yar Sa'adu kuwa sai da tayi sati a barikin sojoji suna azabtar da ita sannan suka saketa ta dawo gidanta a mutukar galabaice jikinta duk yayi rud'u rud'u da shatin bulala abinka da farar mace ko'ina yayi tabo a jikinta, haka ta kwanta ciwo duk a cikin matan dake mata fadanci a kara rasa wacce zata zauna tayi jinyarta, sai da ta dan samu sauqi ta tattara komatsanta ta tafi garinsu tana ganin ba zata iya cigaba da zama ba haka kawai tana zaune wata ta sake janyo mata masifa gwara ta koma garinsu ta cigaba da harkokinta a can.
****
To kwanaki na tafiya wattani na shiga suna mutuwa, komai na tafiya ne da ikon Allah da kuma amincewarsa Naja'atu al'amuranta sun tsananta dan dab take da haihuwa cikinta ya shiga wata na tara har yayi kwanaki! gabadaya hankalin wanda yake kusanci da ita ya tashi saboda tunda cikin ya shiga wattanin haihuwarsa ta kumbura mussaman qafafunta, duk da Likita ya dubata ya tabbatar musu da cewar babu matsala hankalinsu bai kwanta ba.

Abbah Abbas da hajia sunfi kowa tada hankalinsu a kan al'amarin....Baba malam da baba talatu kawaici da alkunya yasa duk damuwar da suke ciki game da 'Yar tasu sun kasa nunawa gabad'aya ma Baba talatu d'auke kanta tayi da kanta sai dai kullum cikin yi mata addua take......B'angaran Abbah Abbas kuwa gudun zargin da mutane ke masa yasa yake boye damuwarsa akan halin da Naja'atu take ciki amma zahirin gaskiya yana cikin tsanani da damuwa mussaman idan yazo gidan ya ganta a jibge a kan kujera! sai dik jikinsa ya mutu kullum haka yake yini ya kwana cikin alhini da jiran tsammani yanda ma ya damu da haihuwar Naja'atu kamar bai damu data Zainab ba su kansu matansa sun fahimci hakan sai dai kowacce na kokarin dauke kanta akai amma hakikanin gaskiya abun yana damunsu mutukar aka cigaba da tafiya a haka to suna cikin matsala gwara ya dawo da ita gidan hankalinsu zaifi kwanciya akan ya dinga shiga halin damuwa akanta.

Ranar Alhamis da daddare ta farka da ciwon haihuwa mai tsanani dama tun sanda cikin nata ya tsufa Yaya Ramlatu take kwana da ita a daki, jin motsinta yasa ta tashi da sauri tana tambayarta, Naja'atu na zufa tana kiran sunan Allah tace"Watakila haihuwa zanyi dan ciwon da nake ji yafi na kullum." Ya Ramlatu tace"To ikon Allah bari na kira hajia sannu kinji ko." Fita tayi daga dakin da saurin gaske..........Tare suka dawo dakin da hajia da sauri ta d'ago ta ta rungumeta a jikinta, tana mata sannu!

Yaya Ramlatu ta shiga hada kayan haihuwa!

Hajia t"Ta kalli Ramlatu da fadin''Ki sanar da hajia Rabi Naja'atu na kan gwiwa." Ya Ramlatu da sauri ta futa daga dakin...Hajia ta rike ta sosai tana tofa mata adduoi.... lokacin ita Naja'atu, ciwon ya tsananta dan dab take da haihuwa, shiyasa ta kasa tsugunawa sai kawai ta silale a gurin ta kwanta tana wani irin kifkif da idanunta! hannunta tasa ta janyo na hajian tana jan salati!

Hajia ta shiga tashin hankali ganin irin abinda Naja'atun takeyi sai hawaye ya soma zubo mata addua take Allah y yanke mata wahala.....Hajia Rabi da Ramlatu na shigowa faya ta fashe! sai yunkuri kawai sukaji tana wani irin nishi!! da sauri suka rufu a kanta kowanne na iya bakin kokarinsa.....Naja'atu Ganin Yaya Ramlatu itace mai kwari a cikinsu sai kawai ta d'amko ta ri'keta gam! gam! a tare suka dinga nakud'ar suna nishi! tare!

Sosai Ramlatu taji jiki ta kuma tabbatar riqon bana Naja'atu bane na mala'iku ne.......Cikin ikon Allah da hukuncinsa yaro ya fad'o a cikin zanin da suka rufa mata, sai kawai kukansa sukaji....Ajiyar zuciya suka sauke dukkaninsu suka had'a baki gurin fad'ar "Alhamdullhi."
*Littafin na kudi ne......!*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin littafin ga yanda abin yake.....Vip group #600 normal group #300...account... 0542382124...Binta umar gtbank...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*BA HARAM BANE!*
71 Yaya Ramlatu ce tayi dubarar d'auko babyn dake ta tsanyara kuka alamu sun nuna cewar yaron yana da qoshin lafiya dan tunda ya sauka ya cika musu kunne da kuka.........Hajia Rabi tace"Namiji ne ko mace."?

Yaya Ramaltu na murmushi tana sake riqe yaron a hannunta tace."Namiji ne gashinan tubarkallah masha Allah." Hajia ta rike Naja'atu sosai a jikinta tana fad'in "To Allah ya raya shi tafarkin addinin musulunci." Suka amsa da amin amin........Yaya Ramlatu ta nad'e yaron a towel ta ajiyeshi kan gado da sauri tazo ta taimakawa hajia
Rabi gurin rirriqe Naja'atun dake ta wani irin nishi!!!

'Yan dabaru suka shiga yi mata domin mahaifa ta fad'o amma abun yaci tura
Hajia ganin lokaci yana ja mahaifar taqi ta fad'o sai kawai ta yanke shawara akan su tafi asibiti zaifi kwanciyar hankali.........

Hankali a tashe Ramlatu ta bude wardrobe cikin sauri ta dauko riga da zani na atampa, hajian ta kar'ba tana kokarin sanya mata Allah sarki Naja'atu Idan kuka ga Naja'atu a lokacin sai kun tausaya mata dan tayi masifar galabaita kokarin kwanciya ma takeyi hajia na hana ta.........Hajia Rabi ce ta shigo d'akin da sauri ta kalli Ramlatu da fadin " Taimaka mu kamata yanzu nasa 'Dan Azimi ya fito da mota." Sai suka fara kokarin miqar da ita, tana lanjarewa kuka take da fad'in su yafe mata mutuwa za tayi, lokacin da take wannan maganar gabad'ayansu jikinsu mutuwa yay Hajia kuwa da yake mai saurin kuka ce tuni hawaye sun 'balle mata.

Ya Ramlatu tace"Ba zaki mutu ba Naja'atu insha Allah zakiyi dogon zango a duniya kiyi hakuri kinji ko ita haihuwa haka take da sammatsi muna zuwa asibiti zasu taimaka miki."
Girgiza kanta kawai take tana karanto sunayen Allah dari ba d'aya a zuciyarta.

Hajia tace"Yana da kyau aje a sanar da iyayenta halin da ake ciki." Ya Ramlatu tace"Hakane bari nasa Dan Azimi ya buga musu kofa."
Naja'atu riqe hannunta tayi tana girgiza mata kai magana takeso tayi amma bakinta yayi nauyi wani irin ciwo mararta yake mata, Hajia Rabi ta riqeta a jikinta tana tofa mata Addua duk sun rasa yanda zasuyi ita ba miji ba ballantana a kirasa yazo ya dauketa yasa a mota........Cigaba sukayi dayi mata taimako irin na gida, cikin ikon Allah ta dinga wani irin yunkuri kamar wacce zata sake sabuwar haihuwa mahaifar ce ta fad'o kafin wani uban jini ya biyo bayanta.

Gabad'ayansu suka shiga godewa Allah dan ganin yanda ya gajarta musu wahala basu sha wahalar zuwa asibiti ba amma a zahirin gaskiya haihuwar tazo da tangard'a! amma dai tunda Allah ya raba lafiya sai su gode masa........Kafin gari ya waye komai yayi tsaf!

Hajia Rabi da Yaya Ramlatu sun gyara maijego da babynta mai kama da ubansa, dakin yayi tsaf dashi sai qamshin turaran wuta yakeyi.....Da Asubah Hajia ta sanar da Alhaji haihuwar ya dinga murna da farin ciki yana Allah Allah a idar da Sallar ya sanar da Mahaifin yarinyar, to shima Malam yayi farin ciki dajin cewa yarinyar shi ta haihu cikin koshin lafiya, cike da farin ciki ya shiga gida domin ya sanarwa da matarsa halin da ake ciki.

Yaya Ramlatu itake tsaye a kan Naja'atu da yaronta dan da gari ya waye ma itace tayi wa yaron wanka ta shiryashi cikin kayan sanyi sannan ta kai Naja'atu toilet ta gasa mata jikinta sosai tasa ta ta zauna a cikin ruwan d'umi!

Naja'atu ta dinga mamakin irin dawainiyar da Ramlatu keyi mata ko a mafarki bata ta'ba tunanin hakan na iya faruwa ba.

Kafin takwas na safe Naja'atu tasha gayu tayi kyau tamkar ba ita ba, Ya ramlatu ta taimaka mata ta shirya jikinta cikin wani Swiss les mai kyau!

Hajia kuwa da kanta ta shiga kicin tayi mata abun kari na mussaman sannan ta zauna a kusa da ita sai data tabbatar da taci ta koshi tukkuna ta fita daga dakin......Bayan kowa ya gama shige da ficensa a dakin, Naja'atu a hankali ta kai hannu inda yaron yake ta daukoshi ta riqe a hannunta, tsira masa ido tayi kawai tana kallonsa, yaron kamar sa daya da ubansa tamkar Bash yayi kaki! ya tofar, wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga zobo mata, wai yau itace ke dauke da d'an Bash a hannunta, ashe dai sai ta fara haifawa Bash d'a kafin ta haifawa Abbah Abbas, gabanta ne ya fad'i Data tuna irin kauce kaucen da Abbah Abbas din ke mata, to yanzu dai gashi ta haihu lafiya kome zai biyo baya oho! itakam idan Abbah bai mai da ita gidansa ba to tana jin ita da aure har abadah!

Hawayen take sharewa wasu na sake kwararowa, cikin wannan halin ya shiga dakin ya sameta.

Bata san ma ya shigo ba sai qamshin turaransa ne ya sanar mata shigowar tasa, da sauri ta dago kanta tana kallonsa suka tsirawa juna ido.........Dauke kansa yayi daga kallonta cikin nutsuwa ya zauna gefanta tare dasa hannunsa ya kar'bi yaron yana dubashi.

Tausayinsa da tsantsar kaunarsa suka sake karya mata zuciya sai kawai ta dukufar da kanta ta cigaba da rera kuka wanda na rasa ko na menene!
Chapter 110 · 0% Book details