Sashe 122
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zainab ta shigo falon rugume da 'yarta ganin Halisa da Najaatu na hira cikin fahimtar juna yasa taji haushin hakan, dauke kanta tayi ta nufi gurun mijinta....Baby Ummi ya kar'ba daga hannuta ya rungumeta a gefan hannunsa na hagu sai ya janyo zainab din ya d'ora a cinyarsa, ya rike kungunta da hannunsa na dama wayarsa ya bata yace tayi musu hoto.......Wannan al'amari ya duguzunma zuciyar Najaatu da Halisa ba kamar najaatu da taji gurin na juyawa da ita, Ita kuwa Halisa d'aga murya tayi tace"Me yasa ba kaje can gurinta kunyi hoton ba ai ina ganin kamar hakan sai yafi armashi."
Yace."Akwai jamaa a gurun ne ko banda ikon nayi abinda nake so a inda na gada dama." Ta'be bakinta tayi tace"Aa kayi komai babu damuwa ai."
Ya kalli su Saddiqa da fad'in su taso suzo gurinsa, yaran suka kewaye shi Zainab na zaune daram! a cinyarsa tana ta daukarsu a hoto farin ciki kamar ya kasheta hakika tayi farin ciki da yanda ya nuna musu cewa ita mai muhimanci ce a rayuwarsa, in da shi kuma anasa bangaran da biyu yake haka duk dan ya cuzguna musu, aikuwa ya hango tsantsar kishi da tashin hankali a idanun Najaatu dan har ja idanunta sukayi saboda tsabar bacin rai da takaici......Sai da suka gama dauke dauke hotonsu sannan yazo inda suke zaune da yake duguwar kujera ce sai ya shiga tsakaninsu, Najaatu kamar ta miqe ta bar gurin haka taji sai dai ta daure ta matsa gefe saboda jin yanda ya takureta....Baby Ummi ya kar'ba ya riqe yasa su Saddiqa suka shigo kowa ya tsaya, sannan ya umarci Zainab din ta daukesu, hakan be mata ciwo ba saboda tasan ita ya fara nunawa muhimanci.....Zainab tayi musu kusan biyar ta miqa masa wayar, tare da fad'in "Zata koma gurin 'yan uwanta!
Babyn ya miqa mata tare da fatan a tashi taro lafiya.....Ta 'karbi 'yarta ta tafi ba tare da ta kula kowa a gurin ba.....Shima tana fita ya miqe daga tsakiyarsu ya kama hanyar futa, babu wanda ya kulashi sai yaransa sune sukayi masa adawo lafiya.
Ya amsa cike da walwala da farin ciki yasan yau da Halisa Da Najaatu dukkaninsu ba zasu yini cikin farin ciki ba, wato harshi zasu sa a gaba sunawa dariya sun mayar dashi sakarai shiyasa yay musu haka. bayan fitarsa Najaatu mamaki take sosai da yanda Halisa tayi sanyi yanzu gabadaya ta mayar da rayuwa ba wani abuba, idan da lokacin baya ne ai bai isa yayi mata irin wannan rashin kyautawa a falonta ba gaskiya kamar da akwai cin fuska a ciki sai taga kamar ma ita ta fita jin haushin al'amarin amma dai yanda ta dauke kanta daga kan abunda yayi yasa taji ta burgeta mutuka
Taron sunan Zainab yayi kyau ya kuma k'ayatar anci ansha maijego ta fito sosai dan sai da tayi shigar kaya kala goma cikinsu duk babu na yarwa abunda yay musu cikas kawai rashin Dan Asharrale amma dai duk da haka ba suyi bikin Lami ba sai da suka saka (Mp) mai kid'an tsiya suka dinga jin wakokin *Gwanja* suna cashewa sai rawa suke suna murguda mazaunai maijego dadi ya isheta ta dinga yi musu liki.....Gabadaya d'abi'un 'yan uwan Zainab na banza ne 'ya'yan malam ne amma kuma sunqi halin malam rashin arziki kawai suke yanda ransu yake so.
*BAYAN SATI BIYU*
Al'amura suna ta gudanawa yanda ya kamata, ta bangaran Najaatu ta bude wuta sosai da ado da kwalliya da ta daidaici lokacin zuwansa gidan zata fito ta zauna kan kujera tana baza kamshi tururuka...Ita kanta hajia sai da taji dad'in salon da yarinyar ta tsiro dashi tasan tabbas yin hakan zai sake janyo hankalinsa kanta, aikuwa dai a tsakankanin kwanakin daurewa kawa
i yake yi amma yarinyar na mutukar galabaitar da zuciyarsa dan dai kawai mutum ne mai dauriya da dauke kansa a kan abu shiyasa baya bari kowa ya gane halin da yake ciki, duk sanda zai shiga gidan yakan sakaye idanunsa da gilashi gudun kada kwayoyin idonsa su nuna abinda yake zuciyarsa.....Najaatu halin ko'in kulan da yake nuna mata bai dameta ba kwalliya da sauran abubuwa ba zata daina ba tunda ta fahimci suna tasiri a tare dashi.....
Da yake tana da yawan gashi mai kitso har gida take zuwa ta 'bata lokaci gurin tsantsara mata kunshi kuwa da ya goge zatayi wani........Al'amarin daya sanya shi tunanin sanja shawara akan wacce sukayi da hajia yana ganin kamar d'aura auran a kurkusa shine kwanciyar hankalinsa idan yace zai cigaba da zama tsayin watanni yana ganin yarinyar hankalinsa na tashi to babu shakka zai iya shiga halin ni 'yasu dalilin daya sa ya yanke shawarar tunkarar abokinsa da maganar.....Abbah Magaji yace"To tunda kana ganin hakan yayi maka shikkenan sai kawai ka sanya a ranar da kakeso a daura auran." Yace."Yau insha Allah idan na shiga unguwar zan zauna da Malam da Alhaji a kan maganar." Abbah Magaji yace."To shikkenan Allah ya sanya alkairi yasa anyi kenan." Ya amsa da ameen ameen.
Najaatu duk wani abu da ake bata da labarinsa dan tunda aka tsayar da maganar daurin aure shi bai kirata ya fada mata ba kuma har yanzu babu wata kyakkyawar alaka a tsakaninsu, tana dai jin maganar sama sama a gurun hajia da Yaya Ramlatu suma kuma babu wacce tace mata komai a kan al'amarin.......Ranar Lahadi da safe yazo gidan, Hajia na sama tana sallar walha Yaya Ramlatu da Hajia Rabi sun tafi asibiti duba Salim ashe tun ranar da Naburago ya watsa masa kudin auransa ya kwanta ciwo kamar ba zaiyi rai ba, sai da aka kwantar dashi a asibiti sannan Sakina ta aiko aka sanar da mahaifiyarsa shine fa Alhaji yace maza maza suje su duba jikin nasa ai hannunka baya ru'bewa ka yanke ka yar........Tana daki tana gyara jakar kayanta yay sallama a dakin, gabanta ya fadi dajin miryarsa, daidaita nutsuwarta tayi ta dan juya tana amsawa .....Idonsa kuri kan gashinta wanda akayi mata wani irin kitso mai kyau jelolin gashin sun dan sauka bayanta, Najaatu nada gashi daidai gwargwado gashi baki mai daukar ido......Ganin yana mata wani irin kallo ne yasa ta lalubi dankwalinta ta daura, a sanyaye tace"Abbah sannu da zuwa."
Da sassauci a tare dashi ya amsa tare da neman guri ya zauna yana kallonta, gaishe tayi ta dan gyara zamanta tana jira taji da abinda yazo dashi.
Gyaran mirya yay as'usul yace."Naji gidan shuru tunda na shigo banji motsin mutum ba ina fata dai lafiya."?
Tace"Wallahi tun safe Alhaji da Hajia Rabi yaya
Ramlatu suka tafi asibitin gadon kaya wai ashe Salim ne bai da lafiya yana can a kwance, ita kuma hajia na sama tana sallar walha." shuru yay na minti biyu kafin yace."Tun yaushe ne baida lafiyar.''?
Tace"Wallahi ban sani ba jiya Matar babansa ta aiko aka fad'a."
Allah ya sawwake." yafada yana me tsurawa yatsun hannunta ido....Dakin yay shuru kowa na tunani, Abbah tunanin ta inda zai fara yake, da kyar ya iya kiran sunanta.
Ta daga kanta ta kalleshi kafin ta mayar dashi kasa
"Kina da labarin maganar daurin auramu ranar jumaa mai zuwa kuwa."?
Gabanta ya fadi tayi saurin kallonsa, girarsa ya daga mata ya lumshe idonsa, a hankali yace." Naso na bari yaronki ya kara kwari amma na kasa saboda ni kadai nasan yanda nake jinki a cikin zuciyata, Halisa tace ba zan ta'ba samun nutsuwa ba sai dake sai nake kokarin k'aryata maganarta saboda ina ganin ke baki isa ki tauyemin rayuwata ta kowane fanni ba, ashe so ba haka yake ba, dalilin yin hakan da nayi yasa ya mayar dani sakarai mara nutsuwa gami da saninan muhumacinsa, hakika a cikin 'yan kwanakin nan ni kadai nasan irin azabtuwar da nake a kanki Najaatu zan sake auranki a karo na biyu inaso ki bani hankalinki da nutsuwarki da dukkanin kulawarki bana so a yanzu dani dake muyi auran Madadi inaso muyi aure naso da kauna wanda zamu rayu a cikinsa cikin farin ciki da walwala har karshen rayuwarmu."
Wani irin farin ciki ya ciki mata zuciyarta hawayen farin ciki ya shiga sauka akan kumatunta, mirya na rawa tace"Abbah ka daina kokwanto akaina a yanzu zan aureka na zauna da kai tsakani na da Allah, Wallahi ban ta'ba kaunar wani namiji ba kamar ka, Abbah bani da za'bi sai naka bani da bakin godiya a gareka kayi min dukkanin sadaukarwa a rayuwata inaso yau na fad'a maka da bakina cewar ina sonka wanda ban san iya adadinsa ba, ina rokonka daka yafe min abubuwan da suka faru a baya kuruciya ce da kuma qaddara yanzu zan zauna zaman aure da kai tsakani da Allah da kuma so da kauna insha Allah."
Ya dinga wani murmushin farin ciki da jin dadi yana wani lumshe idanunsa a kanta, mirmushi tayi ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da hannayenta yace."Nayi farin cikin jin wannan magana taki Najaatu ashe yanzu ina da babban matsayi a cikin zuciyarki ban sani ba, a gaskiya dole wannan karon nayi shiri mai kyau inaso na nuna miki ni daban nake da sauran maza sai kin kasance a matsayin matata zaki gazgata hakan." Yakare maganar yana jifanta da wani shu'umin kallo...Kunya ce ta rufe ta da sauri ta rufe fuskarta tana dariya.
*ALHAMDULLILAHI FAD'AN MASOYA HUTU NE INJI BAHAUSHE*
Salim zazza'bi typoid ne yaci karfinsa inda har ya ta'ba masa hanjin jikinsa,wannan bayanin likitan dake kula dashi yayiwa Alhaji hankalinsa ya tashi Yaya Ramlatu kuwa kuka kawai take tana fad'in ''Yanzu wata da wattani d'anta yana kwance yana ciwo a kasa fada mata wato da sai dai taji labarin mutuwarsa kenan, babu shakka abunda Sakina tayi mata bata kyauta ba
Ita dai Sakina hakuri kawai take bata dan gabadayan su Hankalinsu ya tashi jin cewar hanjin cikinsa ya 'bule dole sai anyi masa aiki.