Sashe 114
Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau kwanan ta sittin da uku da haihuwa, hankalinta gabad'aya yana kansu Mmn Sajida dan kullum sai sunyi waya ita Mmn Sajida har fushi tayi saboda dukkaninsu suna lissafe da kwanakin haihuwarta tace saboda taga suna so su ganta da abunda ta haifa shiyasa take ja musu rai shikkenan zasu cireta daga rayuwarsu kamar yanda ta watsar dasu.
Wannan maganar da mmn sajida tayi ta tayar mata da hankali sosai taji tana sha'awar zuwa gurinsu, sai ta yanke shawarar sanar da Abbah Abbas din domin taji me zaice akan tafiyar.
Lokacin data kira wayarsa yana tare da Zainab da cikinta ya tsufa dan kamar ma naquda take a tsaitsaye dan dai haihuwar fari ce shiyasa basu gane ba amma dai bata da cikakkiyar lafiya.......Zainab ta dauki wayar tana dubawa, My dota ta gani na yawo a fuskar wayar, tasan Najaatu ce sai tace"Abbah Mufida Najaatu na kiran wayarka......Domin ya sake nuna mata babu wata alaqa a tsakaninsa da ita yace "Dauka mana." Da sauri ta daga wayar tana sallama, Najaatu taji rashin dadin jin muryar Zainab sai dai ta daure tace"Dan Allah ki bawa Abbah wayar zanyi magana dashi.
Zainab tace"Kada ki damu shine yace na dauka ina sauraranki." Najaatu taji kanta ya sara! da kyar tace"Aa ki dai bashi wayar." Zainab murmushi tayi cikin sigar kuntatawa tace"Wallahi da gaske nake miki gashi ma yana kimtsawa zai fita kuma da umarninsa nake magana dake ki fad'i maganarki dani dashi duk daya ne." Najaatu ta dinga jin kamar ba'a guri guda take ba dan wani irin jiri ne ya shiga d'ibanta, sai kawai ta kashe wayar ta jefar da ita lafiyayyun hawaye suka shiga zobowa a kumatunta, wannan wulakanci dame yay kama?
Lallai Abbah Na shirin ya dasa mata ciwo a cikin zuciyarta, ashe bai san yanda take bala'in jin kishin matarsa ba zai ce ta daga mata waya aikuwa ba zata qara kiransa ba, kuma tafiyarta zatayi tunda dama ba zamansa take ba
Sai da taci kunanta ta qoshi tukkuna taje ta sanar da hajia maganar zuwa jos din Hajia tace'' Hakan yana da kyau sai ta fara shiri.
Bangaransa kuwa koda ya gama shirinsa bai tambayi zainab komai ba tunda hands free wayar take duk yaji komai ya kar'bi wayarsa yayi tafiyarsa harkokinsa, ita kuwa Zainab a ranar yini tayi cikin farin ciki da annushuwa dan duk ciwo ciwon da take ji a jikinta daina ji tayi sabida abunda tayiwa Najaatu na quntatawa kuma taji dadin yanda ya bata goyon baya d'ari bisa d'ari.
Bayan kwana uku Naja'atu ta shirya kayanta tsaf hajia ta shirya mata tsaraba mai yawa, tace ta kai musu domin sun cancanci abinda yafi haka, a ranar da zata tafi ta shiga gidan Baba Malam da wurwuri tayi musu sallama itama Baba Talatu ta bata abubuwan tsaraba tace ta kai musu, sannan tayi mata fatan dawowa lafiya.
Sai da zata tafi hajia tace"Kinga ikon Allah ko na sha'afa wallahi duk zuwan da Abbansu Saddiqa keyi ban fada masa ba ko kin kirashi a waya ne."?
Da sauri tace"Eh shekaran jiya na fada masa." Hajia tace"To shikkenan dama dan dai kada ya samu labarin tafiyar daga baya ne yasa nayi maganar to Allah ya saukeku lafiya a gaishe mana dasu da kyau.
Naja'atu tace zasuji insha Allahu Hajia......Tare suka fito harabar gidan suna tsaye suna kallonta ta shiga mota direba yaja suka fita daga gidan............Abbah Abbas lokacin daya samu labarin tafiyar ranshi yayi masifar 'baci! ya za'ayi saboda rashin hankali ta dauki yaro karami a lokacin sanyi tayi tafiya mai tsayi dashi, shifa gabad'aya garin jos bai masa ba shiyasa bai ta'ba yi mata zancan zuwa ba, ashe jira take ta haihu ta dauki kafa ta tafi ba tare da ta sanar masa ba(Matarka ce ita da zata tsaya fad'a maka
) Hajia ta dinga tausarsa da fadin ita bata san bai sani ba wallahi amma ai ba wani abu bane dan taje ta nunawa mutanan abunda ta haifa saboda sun cancanci hakan......Yace."Hajia ba hana zuwa anyi ba a qalla dai ta bari yaron bayanta yayi kwari ki duba kiga yanda ake busa iska a gari tana iya zuwa da yaron ya samu wata matsalar yanayin gidan da zataje bashi da kyau da tsayin katanga akwai matsala sosai." Hajia ta dinga mamakin maganarsa tace"To ai lalura a ko'ina ma daukarta akeyi kuma ta tafi da kayan sanyi nasan zata kula dashi.
Shuru kawai yay ya miqe tare da fadin shi zai tafi.Hajia tace to a sauka lafiya, hanyar futa ya kama ta bishi da kallo tana mamakin son 'ya'yansa.
Kasa hakuri yay yana driving ya shiga kiran wayarta, lokacin har ta sauka tana tare dasu Mmn Sajida sai gaishe da juna sukeyi, su Walid da 'Ya'yan Mmn Ladi sun kewayeta tana ta basu tsarabar da taje musu da ita.
Koda ta duba wayar taga number sa ce sai ta cigaba da abunda takeyi, taki dauka sai da ya kira sau uku tukkuna ta daga, tana kokarin gaisheshi ya dakatar da ita......"Ashe baki da hankali Najaatu wa kika tambaya wanda ya baki izinin tafiya wani gari? ashe kina nan da halinki na taurin kai ko."
Kai tsaye tace"Abbah yi hakuri dan Allah kwana hudu da suka wuce na kira wayarka na tambayaka sai dai idan mantawa kayi."
Yace."Ke bana son karya yaushe kika kira ni kika tambaye ni ai saboda kin san bazan bari ba shiyasa kika 'ki sanar dani." (Takwara zo kiga karfin hali
Tace"Wallahi na kira wayarka Zainab ta dauka kuma na fad'a mata maganar sai dai idan itace bata fad'a maka ba."
Shuru yay yana tunanin maganar......." To Gobe Dan Azimi zai zo ya dauke ki dan haka duk wanda kika san zaki gaisa dashi a garin kiyi kokarin gaisawa dashi kafin gobe." Yana gama maganarsa ya kashe wayarsa..........
*Littafin na kudi ne...!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake Vip group #600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank...idan katim waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
_Abbah Abbas ka janyo 'yan group yau na caccakar ka
Mum Basma tace idan ka tsaya kallon ruwa kwado zaiyi maka kafa, ita kuma Sakina tace" Kana ruwa
sistar Habiba tace Dantalle ya shigo kawai ayi dashi tunda kai ka tsaya wasa!
To nima dai nace ka ajiye makaman ka dan idan ka tsaya jan aji za'ayi maka shigar sauri Najaatu dai a yanzu allura cikin ruwa ce (mai rabo ka dauka)_
*MADADI74*
Najaatu shuru kawai tayi tana bin wayar da kallo, mamakin maganarsa take wai zai turo Dan Azimi gobe ya dauketa lallai aikuwa yanda yazo haka zai koma domin kuwa bata tunanin zata bishi to wai nauyin waye a kanta da zaice lallai sai ta dawo gida me za tayi masa bayan baya kulata sannan kullum yana tare da iyalinsa ita kuma sai ya hanata zuwa inda zata ji sassauci zuwanta gidan Mmn Sajida ya saukar mata da nutsuwar zuciya ko babu komai zatai kwana biyu bata saka shi a idonta ba, domin watarana ganinsa yana janyo mata abubuwa da dama hakuri kawai takeyi tana bin rayuwa a yanda tazo mata.
Mmn Sajida ta kalleta a sanyaye tace"Najaatu naga jikinki yay sanyi ashe ba'a sani ba kika zo.''?
Kallonta tayi tace"Waye ya fad'a miki haka."?
Kai tsaye tace"Gashinan mahaifinki ya kira waya yana miki fad'a." Mmn Ladi tace"Eh ai nima shiyasa kika ga jikina yay sanyi wallahi.
Najaatu murmushi tayi a nutse tace"Wai ku waye ya fad'a muku Abbah Abbas mahaifina ne."? bude baki sukayi suna kallonta, ta sunkuyar da kanta tana dan murmushi wanda ya tsaya iyakacin lebenta.
Mmn Sajida tace ''To idan bashi ya haife ki ba waye shi a cikin rayuwarki."?
Tana girgiza kanta tace"Shine mijina na fari wanda na baku labarinsa farkon zuwana garin nan.
Suka tsira mata ido suna mamakin maganarta, kwallah ta cika mata ido tace"Kuna mamaki ko? ni kaina ina mamakin kyautayi da tausayi da kyautatawa irin nasa dukkanin irin abubuwan da nayi masa bai sa ya watsar dani da al'amurana ba, yana tsaye a kaina da dukkanin bukatuna." Mmn Sajida tace"Lallai Najaatu kin tafka babban kuskure a baya waye ya fada miki ana samun nagartattun mutane irin wannan mutumin? yanzu dama a kan an aura miki shi kika gudo garin nan yanzu dan Allah meye aibunsa meye kuma abun'ki a tattare dashi."?
Tana kuka tace"qaddara Mmn Sajida qaddarar wannan yaron dake hannuna ce ta kawo ni garin nan har na had'u daku....Wallahi har bana so na tuno abubuwan da suka faru a baya Mmn Sajida ni da kaina nasan na tafka kuskure babba! wanda yanzu nake nadamar aikatashi, yanzu gashi inaji ina gani Abbah yafi karfina sai dai na kalleshi da ido Mmn Sajida a yanzu ne nake masifar so nayi zaman aure dashi shi kuma yana nuna baya so, wallahi bansan iya adadain son da nake masa ba a cikin zuciyata saboda mutumin ya cancanci a soshi duk wata sadaukarwa yayi min yana kanyi min babu namijin da zan aura na samu nutsuwar da nake bukata, Mmn Sajida ba zan 'boye muku halin dana ke ciki ba wallahi saboda halin ko in kula da yake nuna min yasa naji zaman garin ya gundureni na tattaro na tawo nan kuma bana tunanin zan koma a kurkusa sai na huta tukkuna."
Mmn Ladi ta sauke ajiyar zuciya tace"Gaskiya Najaatu naji miki haushi da takaicin rasa wannan mutumin to amma tunda kin jingina al'amarin a matsayin qaddara muma zamu jingina shi a hakan ammafa wallahi kema da akwai son zuciyarki wanda shine ya kara sanyawa kika kai kanki ga wahala! saboda haka ni dai shawarar da zan baki wallahi ki lalla'ba da wayo da siyasa ya mayar dake dan nima na tabbatar da cewar a gurinsa ne kadai zaki fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali saboda yanzu duniya kowa kansa ba kowane namiji ne zai yarda kije masa da d'anki ba.
"Mmn Ladi wane dabaru zanyi ya mayar dani ni bazan iya fada masa baki da baki ba, na hakura zan cigaba da rainon yarona har Allah yasa ya girma, shikkenan idan na samu daidai dani sai na aura.