← Book details Madadi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 143

Sashe 128

Madadi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallo ta kunna ta kama tashar Arewa 24 lokacin suna maimaicin dadin kowa, sai film din ya dauki hankalinta sosai ta dinga dariyar (Adama da Kamaye)
film din ya d'ebe mata kewa sosai wanda har yasa ta d'an samu sassauci a cikin zuciyarta, wannan karon ba ta sake tunanin kiran wayarsa ba text ta tura masa kamar haka.....
_"Assalam Annuri barka da yamma na kira wayarka domin na tambayi jikin Ummi baka dauka ba to ina fatan Allah yasa lafiya, ka dawo lafiya."_
Tana tura masa ta miqe ta nufi kicin domin shirya abincin dare, tuwon semo tayi ta shirya miyar agushi da busheshshen kifi sannan tayi miyar nama daidai misali ta gyara kicin din tsaf ta shirya gurin cin abincin ta nufi bedroom domin duba d'anta dake bacci!

Daukarsa tayi ta goya a bayanta ina dalili tayi ado da kwalliya shi wanda tayi dominsa yaki ya dawo ya gani, yamma tayi ba zata bar d'anta a kwance ba, dalili kenan daya sa ta goya shi a bayanta ta fito falo ta zauna, sai dai tana zama yaron ya fara motsi yana kuka da alama baya son goyon sauko dashi tayi tana dubashi, hannu yake sawa a baki yana kama rigarta nono yake so.....Haka ta cire after dressing din ta fito da nono tasa masa a baki....Fuskarsa ta tsirawa ido tana kallo yaron kammaninsa da ubansa sai sake fitowa yake, taji zuciyarta na karyewa, idanunta ya cicciko da kwalla kawai sai ta shiga kiran innalilihi wa'ina ilahi raji'iun!

Hakika tana fargabar zuwan ranar da Daddy zai san waye ubansa me yayi a kashe shi.

'Bangaran Zainab kuwa yini sukayi cikin farin ciki ita da 'yan uwanta su d'ora su sauke a rana sai suyi girki kusan kala biyar 'barna sukeyi sosai a gidan nama komai yawansa aka kawo baya kwana uku sun cinye al'amarin nasu sai gyaran Allah haka kawai bayan sunci sun koshi sai su tsiri had'a tea da tsakiyar rana suyi ta 'barnar madara da sauran kayan tea babu abinda ya damesu.....Zainab tace"Wallahi aunty Balaraba kin iya tsara makirci ki duba dai ki gani lokaci guda al'amura sun dagule babban abinda ya sake sani cikin farin ciki shine muna dawowa yana niyyar ya koma gidanta aka kirashi a kasuwa cewa yana da b'aki nasan kuwa ba zai koma gidan ba sai lokacin tashi daga kasuwar yayi ai naji dadi da hakan ta kasance nasan tana can tana jin bakin ciki a zuciyarta." Aunty Balaraba wacce suke shan farfesun kaji tace." Ai na fad'a miki dole hankalinsa ya tashi tunda mutum ne mai son 'ya'ya yau da daddare misalin sha biyu ko sha daya kafin dai ya kashe wayarsa ya kwanta sai ki sake kiransa kina kuka na tashin hankali ki sheda masa cewa jikin Zainab ya rikice a guje zai zo sai kawai ki yaudareshi ya kwana a gurinki na tabbata sai ta kusa mutuwa dan takaici."
Zainab mirmushi tayi tace"To aunty haka za'ayi Dariya suka fashe da ita tare da fad'in "Shegiya mutsiyaciya da kafarta zata gudu." A daidai lokacin Halisa ta shigo ta samesu sai shewa suke, itama maigidan ne ya kirata a waya yake fada mata rashin lafiyar yarinyar dalilin daya sanya kenan ta shigo ta dubata.

A nutse suka gaisa tace"Ashe Ummi ba taji dadi ba wallahi sai yanzu ya kira ni a waya ya fad'a min Allah sarki Allah y bata lafiya."
Aunty Balaraba tace"Ameen ya Allah wallahi jiya munsha fama da yarinyar kamar ba zatayi rai ba ta dinga suma gashi taki kar'bar nono wai ashe rashin abinci ne ya janyo mata kasancewar nono zainab baida kyau da inganci yasa dr ya bata magani da madara kinga tunda aka dama mata madarar aka bata maganin take bacci lafiya lau."
Halisa tace"Allah sarki ai ciwon yaro da akwai abun tausayi Allah dai ya sawwake." Suka amsa da ameeen." Halisa na kokarin miqewa Zainab tace"Aunty Halisa ina amaryarki."?

Aunty Halisa ta kalleta tana mamakin maganarta...Tace"Najaatu wai."?

Zainab ta d'aga kanta tana ta'be bakinta.....Aunty Halisa murmushi tayi tana mamakin yanda Zainab ta damu da Najaatu babu shakka idan tace zata damu akanta akan Najaatu to zata jefa kanta a masifa dan Najaatu itace ruhin mijinsu shiyasa itama tunda ta fahimci haka ta watsar da makamanta tana ganin duk wani abu da ya dace tayi tayi akan Najaatun amma bata samu nasara ba karshe ma nadama da dana sani ne ya biyo bayan abinda tayi, kuma gashi Najaatun na nan nata rayuwarta sannan mijinta bai fasa so da kaunarta ba, tana ganin da zata bawa Zainab shawara ta dauka to da tace ta watsar da makamanta ta zauna lafiya da Najaatu domun ta samu soyayyar mijinta........murmushi tayi tace.''Ki shiyar ki dai aini tuntuni anyi min kishiya Najaatu ba kishiya ta bace taki ce."
Aunt Balaraba tace"Kwarai kuwa aike kam yar kallo ce sai ki sakar musu su fafata.'' Halisa tace"Shine abinda nagani nima to ni daina zan shiga gurina Allah ya kara lafiya.'' Tana gama maganarta ta fita daga dakin, tana futa suka dasa gulmarta sai zaginta suke Zainab na cewa ai dama tuntuni ta fahimci so take ta had'a kai da Najaatun to duk zata iya dasu wallahi.

Abbah Abbas bai samu kansa ba sai yamma likis ganinsa a kasuwar yasa Jamaa suka riqeshi sai da yay da gaske sannan ya samu nasarar fitowa daga kasuwar, a hanya magariba tayi masa sai ya shiga tunanin ina zai fara nufa gidan Alhaji ko kuma zuwa duba jikin Ummi ko kawai ya wuce gidan Najaatu dan gabadaya hankalinsa na kanta yaga kiranta da text dinta amma rashin nutsuwa ya hana shi ya bata amsa, yanke shawarar zuwa gidan alhaji yay ya gaisa dasu bayan ya fito sai ya duba Ummi d'in....A gurguje suka gaisa da mahaifiyar tasa nan yake sheda mata rashin lafiyar Ummin tace insha Allahu gobe zasuje su dubata, da zai tafi ta bashi wata leda viva da kayan mata a ciki wai ya kaiwa Najaatu kar'ba yay tare dayi musu sallama ya tafi.

Yaji dadi daya shiga gurin Zainab ya ganta a zaune tana cin abinci ga Ummi din a cinyarta tana bata nono ya zauna yana tambayarta yanayin jikin yarinyar, tace"Alhamdullhi jiki yay sauki yini tayi bacci yanzu data tashi shine nake bata noni............Yace."To Alhamdullhi sai ki mayar da hankali gurin bata abincinta da kuma maganinta." Tace"Insha Allahu." Sallama yay mata ya miqe da niyyar tafiya taji tamkar taje ta janyo shi, kwafa tayi tare da jan tsaki kasa kasa......Abbah gurin Halisa ya shiga suka gaisa sosai ya tsaya ya duba yaransa yaji matsalarsu kafin yayi musu sallama ya tafi.........Najaatu ta sake sabon wanka tayi gayu sosai tai kyau jikinta da gidanta sai kamshin turare yake.

Ganinta a nutse da yaronta yasa yaji wata nutsuwa ta saukar masa, yasan Najaatunsa ta wani gefan tana da hankali da nutsuwa zata kar'bi uzirinsa kuma ba zatayi masa hauka ba, hakika yaji dadin yanda ta tar'beshi ta bashi abincinta mai dad'i ya cika cikinsa.

Sai da ya nutsu tukunna tazo ta zauna kusa dashi tare da ri'ke hannunsa cikin alhini tace" Wallahi tunda ka fita na kasa samu nutsuwa sai sa'ke-sake nake a zuciyata na abubuwa marasa kyau amma naji dad'i da naji kace jikin yarinyar da sauqi ina rokon Allah ya bata lafiya."
Abbah yana kallonta da kyakkyawan murmushi a fuskarsa yace." Ameeen ya Allah nagode sosai da kika fahimce ni, ni kaina banyi tunanin yau zan zama busy ba wallahi naci burin na zauna a tare dake na gwangwaje amarcina sai wannan matsalar ta shigo ciwo ya wuce komai mussaman na k'aramin yaro bayan mun dawo daga asibiti ina kokarin dawowa gareki aka sanar dani ina da 'baki a kasuwa wannan dalilin ne yasa kikaga ban shigo da wuri ba ina fata dai ranki bai 'baci ba."
Murmushi tayi tace"Haba dai raina bai 'baci ba wallahi nasan ai duk inda kake ina cikin zuciyarka kuma dole aiyi maka uziri duba da yanayin yanda kake hurd'a da jamaa.'' Yay mirmushi mai kyatarwa, yace."Jeki dauki min abokina mu gaisa.

A hankali ta miqe ta isa inda Daddy ke kwance ta daukoshi, Abbah ya kar'bi yaron yana dariya tare da daga shi sama yana masa wasa, yaron ya dinga dariya yana cilla kafafunsa, Ya kalleta da da mirmushi a fuskarsa yace."Yaron nan wai zaiyi wata nawa yanzu." ?

"Watanshi takwas da 'yan kwanaki." Ya shiga girgiza kansa da fad'in abin babu wuya to Allah ya raya mana shi.'' Ta amsa da ameen tare da kar'ba yaron daga hannunsa....Abbah loptop d'insa ya janyo ya shiga dubawa kamar yanda ya saba, Tana kusa dashi suna hira sama- sama har ya d'an duba abunda zai duba ya rufe loptp din idanu a lumshe ta kalleta, tana kokarin miqewa dady za taje ta gyarawa shimfida, sai kawai ya bita da kallo har ta shiga bedroom din.....Minti biyar ya miqe yabi bayanta, lokaci har tasawa yaron pampars tasa shi a net tana kokarin miqewa ya shigo, hannunta ya rike suka zauna gefan gado, ta kalleshi taga yanayin da yake ciki sai ta sunkuyar da kanta tana murmushi...Yace."Ina tunanin cikin satin nan zamuje miyi umara mu dan huta dan idan banyi da gaske ba jamaa na iya hanani na more amarcina so ki zauna cikin shiri insha Allah acikin satin nan zan shirya mana tafiya zuwa kasa mai tsarki."
Da murmushi a fuskarta tace"To shikkenan amma sai nake ganin anan din ma za'aka iya amarcinka." Girgiza kansa yay yana wasa da hannayesa a jikinta yace."Nafi so nayi nesa da gari sai nafi samun nutsuwa.....shuru tayi tana jin yanda tsigar jikinta ke tashi, ya riga ya zuge mata zif din rigarta yana ta cakuda mata nonowa! gabadaya jikinta ya saki gashi wanka take so tayi....A hankali tace"Abbah ka bari nayi wanka." Fuskarsa yake goga mata a wuyanta gemunsa sai tsikararta yake yace."Ba sai kinyi wanka a haka ma kina kamshi ." shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya..........Abbah rikita mata lissafi ya shiga yi da kalolin soyayyarsa wanda yasa ta hautsine ta dinga mayar masa da martani tana kesses din fuskarsa tare da shasshafa jikinsa.....Maqale junansu sukayi bayan sun raba jikinsu da kaya suka dinga wasanni da jikinsu.
Chapter 128 · 0% Book details