← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 218

Sashe 85

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ingantattun turaruka daga
asashen waje
Farashi mai sau
i da rangwamen Sallah
Kyaututtuka da aka shirya cikin kwali na alfarma
Nationwide delivery
*Scent Palace* ba kawai turare ba ne
amshi ne da ke
arfafa soyayya, da
i, da kima
Tuntube mu yau don odar ki:
Gombe
08038888936
Instagram/Facebook/WhatsApp:08038888936,08154812224
*Scent Palace*
amshin da ke bayyanar da
ima!
amshi ba wai kawai
amshi ba magana ce ta zuciya
HALYSAAH 41
Aunty Farida ta share hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsu Ajay da kyar tace "Wallahi ban san ko har su nawa bane a motar, ban ma san ya motar take ba tunda ina cikin gida sanda abun ya faru, yaran makota dake diban ruwa a bakin rijiyar tare da ita ne suke cewa kawai suna diban ruwa sai ga motar ta shigo street din, wasu mutane suka sauka a motar suka ja ta zuwa cikin motar suka tafi da ita, a sannan an idar da sallahn subahi kenan kun ga gari bai waye ba ai" Ajay was speechless, bai ta
a zama confuse haka a rayuwar sa ba don ya ma rasa abun cewa, likewise Jay dake jingine jikin mota tun da suka iso unguwan dama shi bai ce komai ba, Ajay ya daga kai after some seconds ya kalli Aunty Farida a hankali yace "Amma yana da number ki ne Aunty?" Aunty Farida tace "Ba shi da wannan number tawa gaskiya sai tsohon layi na, kwanaki Maman Khaleesat tayi rashin lafiya sai na tafi kano dubata to a hanya na yar da wayata, da na zo kano sai na siya sabon layi kafin inyi welcome back din tsohon layin, to har yanxu ban yi welcome back din ba" Ajay yayi shiru yana nazari, Aunty Farida na hawaye tace "Tsautsayi yasa ta fita deban ruwan yau, amma tunda ta xo wallahi ni ke diban ruwana bana barin ta dibar min tunda har yanxu gata nan ne dai bata dawo dai dai ba, wani lkcn ma da daddare idan na dawo kasuwa nake yi tunda ana wahalar ruwa a season din nan don yawanci rijiyoyi kafewa suke yi sai ana bari ruwan na taruwa sannan a diba, gashi ba a samun wuta balle a samu ruwan pampo, a jiyan nayi girki me yawa ne na wani biki duk sai na gaji ban deba ruwan da daddare ba, da na tashi kuma sai nake jin zazzabi, kun ji dalilin fitarta ta debo mana ruwa kenan" Ajay ya jingina da motarsa ya lumshe ido ya bude, gaba daya
ansa ya gama kullewa, bai yi zaton Abdul ya wuce yanda yayi zatonsa ba, the guy is really something else ko wani salon tactics na mugunta ya san sa gashi har yau yaki kunna wayarsa balle a san inda yake, ko by mistake baya kunna layin, shi dai Jay dama bai ta
a underrating Abdul ba dai dai da rana daya duba da irin actions din da ya dinga portraying, kawai dai tracing din Halysaah har zuwa Lagos is the least thing da yayi zaton Abdul zai yi, tunda bashi da access da Aunt dinta, but like seriously how did he even find his way, bayan bashi da active line din Aunty Farida sannan bai san unguwan da take ba, ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yana tunanin ta inda za su fara billo ma wannan lamari, tunda dai babu ta yanda za su ce yayi kidnapping Halysaah da ke a matsayin matarsa ta sunna.

Khaleesat na zaune at the far end of the large room ta hade kanta da gwiwa, zuwa sannan ta hakura da kukan da take don ba ma ta da strength din kukan amma tana jin zuciyarta na mata zafi ga wani azababben ciwon kan da take ji da kishin ruwa da ya dameta, tafi awa sha biyu zaune a dakin ba ci ba sha, don tunda aka shigo da ita har zuwa sannan babu wanda ya sake zuwa dakin, infact bata ji motsin kowa a gidan ba alamar ita kadai ce a ciki, bandakin dake cikin dakin take shiga tayi alwala ta fito tayi sallah duk da ba sanin lokaci tayi ba kawai tana amfani da instinct dinta ne, at this point in time tasan bata da wani sauran gata sai wajen Allah, domin kuwa tasan Abdallah ne kawai zai sa a zo ayi mata irin wannan daukan, wasu hawaye masu zafi suka zubo idonta tana tausayin rayuwarta, all she could remember vividly was that tana bakin rijiyan dake kusa da gidansu Aunty Farida tana diban ruwa wasu mutane biyu suka zo a mota, lokaci daya kuma suka yi leading dinta zuwa motar tasu, at first turje masu tayi ta fara kokarin raising alarm tana ihu, yaran dake bakin rijiyan duk suka gudu suka shige gidajensu, tana kururuwa daya mutumin ya rufe fuskarta da wani Handkerchief da sauri, taji ta sha
i wani abu kamar dust, lkci daya kuma ya cire handkerchief din a fuskarta, daga nan kuma ko kokarin ihun bata sake yi ba cause she became weak, ita dai tasan all through the ride she was conscious but not fully, gashi ta kasa tabuka komai don duk jikinta ya mutu, kanta yayi mata nauyi idonta suka dinga juya mata....

Da sauri Khaleesat ta dago kanta ta mike tsaye jin ana
arin bude kofar dakin ta waje da makulli, gabanta ya dinga bugawa da karfi idonta na kan kofar har ya bude ya shigo, she wasn't expecting anyone but him dama, ta sauke kanta bayan sun hada ido, wasu sabbin hawayen suka fara zuba idonta, muryarsa taji ya daki kunnenta cike da isa da gadara yace "Har yanxu Body guards din naki basu biyo bayanki bane?

Ai yaci ace sun iso zuwa yanxu don naga It's almost 12 hours now, how comes basu zo cecen ki ba duk capacity din su" Sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kallesa cikin rawar murya tace "Ka ji tsoron Allah...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da matsanancin kukan takaici, shi dai yana tsaye yana kallonta da wani murmushin mugunta kwance fuskarsa, ta dago kai da sauri jin yana takowa har zuwa inda take tsaye, mannewa tayi da bango tana jin kamar bangon ya tsage kawai ta shige gabanta na bugawa da karfi, sai da ya zo dab da ita cikin kwantar da murya yace "Me kika ce?" Ta girgiza masa kai da kyar gabanta na ci gaba da faduwa muryarta na rawa tace "Kaji tsoron Allah Ya Abdul, kaji tsoron...." Bata rufe baki ba taji saukan lafiyayyen mari a fuskarta wanda sai da taga taurari, ta dafe kuncinta tana kallonsa babu ko kiftawa, cikin husky voice dinsa yace "You still have the guts to repeat what u just said saboda baki da kunya ko?

Ni zaki gaya ma in ji tsoron Allah?

To tsoronki zan ji ko tsoron uban ki dake Mariri idan ban ji tsoron Allah ba?" Da kyar Khaleesat ta dake tace "Ka zageni amma kar ka sake zagar min uba" Still bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani wawan marin a other side of her face, this time around sai da dakin ya juya mata don ba marin wasa yayi mata ba, ya fixgota yana mata wani irin kallon da ya gigitata don tuni idonsa yayi jajur yana huci yace "Ina magana kina mayar min how dare you poor wretched girl?" Ta fashe da matsanancin kuka tana jin dama Allah ya dau ranta kawai ta huta a wannan lokacin, zata durkusa kasa ya hadeta da bango yace "Yau ina body Guards din naki dake goya maki baya kina min iskanci?

Tell me where they are today?

Da aurena a kanki kike hulda da wasu banzayen gardawa saboda ke jahila ce warce bata san me take ba" Tana kuka sosai bata san sanda tace "To wai ana aure dole ne dama Abdul?

Nace bana son auren, bana son ka, gwara kawai ka kasheni duk mu huta" Da karfi ya bugata da bango har sai da taji numfashinta ya dauke na few seconds, yana mata wani mugun kallo yana huci yace "Dama ke baki san aurena wajibi ne a gare ki ba ko kina so ko ba kya so?

Dama shi ubanki bai gaya maki hakan ba ko mantawa kika yi saboda kin fara bin maza?

Wallahil Azeem kin ji rantsuwar musulmi ko?
Chapter 85 · 0% Book details