← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 218

Sashe 154

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Am i ur Bodyguard?" Jin tayi shiru ya juya ya kalleta, hawaye ya gani a idonta, ta kai hannunta tana goge hawayen, bai sake cewa komai ba idonsa a kan grape din gabansa, after almost 30 seconds ya kalleta yace "Ya ma kike da suna, Yaushe zaku fara exams?" Bata dago kanta ba cikin sanyin murya tace "In less than a month time" Yace "Amma kinga silly frnd din nan taki wataran sai ta jefa kanta masifar da bazata iya fita ba, har ke sai ta jefa cikin matsala, shi tout din ta tsaya take exchanging words da saboda rashin kamun kai...." Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Ajay bai sake cewa komai ba a parlon yana nazarin how to tackle the issue, shi ya dade bai ga
an iska kamar Abdul ba, amma zai yi maganinsa, shafa kansa yayi still thinking of where to start from, a yanxu dai baza su fara cewa ta zauna a gidan nasu ba don Mai martaba went on a trip to Toronto, kwanansa hudu kenan a can kuma basu san ko zai biyo ta Amurka ba, infact zai ma biyo don in dai ya taho overseas komin nisan inda yaje da Amurka dole sai ya zo Maryland in har suna kasar to check on them, so they won't take the risk of accommodating her in the house, assuming the semester isn't late da kawai sun mata applying for On-campus residence halls a cikin makarantar ta zauna, Ajay ya daga kai yana kallon Cousin brother dinsa Mukhtar that was coming towards the parlor, Mukhtar yayi kasa da murya yace "Tare mu ke da Mai martaba...." Ajay bai san sanda ya mike tsaye ba dai dai sanda yayi ido hudu da Abbansa dake biye da Mukhtar a baya,
amewa yayi a inda yake tsaye with surprise, what a bad coincidences this is, Mai martaba ya shigo parlon with a broad smile on his face yayi kamar ma bai ga Khaleesat ba, Ajay ya sauke kansa kamar wanda ruwa ya cinye a wajen, at first ya ma rasa abun cewa, can kuma yayi karfin halin cewa "Barka da zuwa ranka shi dade....." Khaleesat ta daga kai tana kallon Mai martaba sai kuma ta sunkuyar da kanta ta zamo kasan carpet ta gaishesa cikin sanyin murya, sai a sannan mai martaba ya kalleta still smiling ya amsa gaisuwarta, Mukhtar yayi offering masa kujera ganin bai zauna ba, Mai martaba yace "I am fine Mukhtar..." Sai kuma ya kalli Ajay da ya kasa kallonsa har sannan yace "Ina Jawwad?" A hankali Ajay yace "I think he went out just now..." Mai martaba yace "Ohk" Mikewa Khaleesat tayi da niyyar barin parlon, Mai martaba ya kalleta yace "No yi zamanki yarinya, ya sunanki?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta koma ta zauna a hankali tace "Sunana Jiddah" Yayi nodding kai yace "Maa sha Allah, ke er Nijar ce?" Khaleesat ta
an yi murmushi tana wasa da gyalenta tace "A'a, er Nigeria ce" Mai martaba yace "That's good, Nigeria wani state?" Tace "Kano" Ajay dai yaki daga kansa yana jin zufa na karyo masa a forehead, can kawai ya juya ya bar parlon yana tafiya a hankali, Mai martaba ya zauna saman kujera still looking at Khaleesat yace "Karatu kike a kasar nan Jiddah?" Khaleesat tace "Eh karatu nake" Yace "That's good, wace makarantar?" A hankali Khaleesat tace "John Hopkins university..." Mai martaba na jinjina kai yace "Maa sha Allah, kano a wani unguwa iyayenki suke?" Khaleesat tace "Muna mariri ne" Shi dai Mukhtar na ta tsaye a parlon yana mamakin yanda Mai martaba ya tsaya ya bada lokaci yana conversing da Khaleesat bringing her down to his level, Ita kanta Khaleesat bata yi tunanin sarki bane shi duk zaton ta ko dai brother din babansu ne shi din, Mai martaba yace "Maa sha Allah Jiddah, Allah ya bada sa'an karatu" Tace "Ameen Abba Nagode" Mikewa tayi zata bar parlon ya kalli Mukhtar yace "A bata dala dubu biyar Mukhtar" Mukhtar ya
an risina kai da ladabi yace "To ranka shi dade" Khaleesat na kallon Mai martaba a hankali tace "Abba Nagode, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara girma" Daga mata hannu kawai yayi with smile, sannan ta mike ta bi bayan Mukhtar, tun basu fita parlon ba sai ga Jay ya shigo, kasa karasowa yayi bayan yayi ido hudu da Khaleesat ga Mai martaba zaune a parlon, can ya kalli Mukhtar da ya daga masa hannu alamar gaisuwa, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam ya sunkuyar da kai walking slowly, a hankali tace "Sai anjima" Murmushin karfin hali kawai yayi mata without saying anything, ta bi bayan Mukhtar suka bar parlon, Jay ya karasa har cikin parlon ya zauna kasan carpet yana gaida Mai martaba da ladabi, Mai martaba ya amsa yace "Ina Ahmad din?" Jay ya mike ya bar parlon zai kira Ajay, ba a dau lokaci ba suka dawo tare, shi dai Ajay ya kasa hada ido da mahaifin nasa, ya zauna kan carpet gefen Jay, sae kuma yayi karfin halin cewa "Ya hanya ranka shi dade?" Cikin nutsuwa Mai martaba yace "Alhamdulillah...." Daga haka mai martaba bai sake cewa komai ba, Jay da Ajay ma duk suka yi shiru kamar masu jiran hukunci a gabansa, after a while Mai martaba ya kalli Ajay yace "Ita ce yarinyar da za aje gidansu kenan..." Ajay ya
aga kai yana kallon Abban nasa, can ya
an sosa kai yana murmushin karfin hali yace "Abba ai budurwar Jawwad ce, wajensa ta zo ba wajena ba" Mai martaba ya kalli Jay da bai dago kai ba, Can Abba yace "Budurwar Jawwad kuma na gan ku zaune tare a parlor" Ajay ya gyara zama yace "Ranka shi dade abinda na fada gaskiya ne, ba wajena ta zo ba wajensa ta zo" Mai martaba ya kalli Jay, cikin nutsuwa yace "Jawwad" Jay ya dago kai amma ya kasa hada ido da mai martaba, jin mai martaba yayi shiru yasan bayani yake jiran ji daga garesa, hakan yasa ya fara magana with calm yace "Gaskiya ya fada Abba, haka ne..." Mai martaba yayi shiru na kusan minti daya kafin yace "Ita Hadiyar fa?" Jay ya kasa cewa komai, Mai martaba sam bai yarda da abinda suka ce masa ba don gani yake kamar Jay is covering for Ajay, after some minutes cikin hikima Mai martaba yace "Ko hakan yasa kake ta jan maganar Hadiyah?" Jay ya gyada masa kai still not looking at him, Mai martaba ya numfasa speaking with calmness yace "So ta yaya zan yarda da ku yanxu?

Don na fara kokonton ka yanxu Jawwad, a da dai baka min karya amma yanxu ka fara" Jay yayi karfin halin cewa "Allah ya taimake ka, believe me ba karya nayi maka ba" Mai martaba yace "Ai shi ne nake tambayarka ta yaya zan yarda da hakan?

Yanxu nema maka auren yarinyar zan sa ayi idan na koma Nigeria so i can clear away my doubt?" Jay ya daga idanuwansa ya kallesa, a hankali yace "Da zan yi farin ciki da hakan ranka shi dade" Mai martaba yace "To batun Hadiyah fa?" Jay ya rasa abinda zai ce, after few seconds yace "I will be glad idan aka amince min na janye daga batun auren Hadiyah" Mai martaba ya
an yi murmushi yace "Ai bazan maka dole ba Jawwad, ya rage naka kayi ma iyayenka mata bayani su bar maganar Hadiyah tunda kana da yarinyar da kake so da aure, don wa
a a bakin me ita tafi dadi, in kuma kaga zaka hadasu su biyun it's fine, as far as zaka yi adalci...

By so doing iyayenka mata baza su dau lamarin da zafi ba tunda duk sun saka ran auren ka da Hadiyah" A hankali Jay yace "But i am afraid za su yi shunning batun idan na kai masu ranka shi dade" Mai martaba yace "Not when i am alive Jawwad, duk abinda kake so shi zan maka in sha Allah" A hankali Jay yace "Allah ya kara girma ranka shi dade...." Mai martaba ya kalli Ajay yace "Kai kuma ina sauraron ka har yanzu" Mikewa Mai martaba yayi ya bar parlon, bayan tafiyarsa suna ta zaune kamar wa enda aka yi planting a wajen sai dai ko wannensu akwai abinda yake tunani a ransa, Ajay ya
an kalli Jay sai kuma yayi breaking silence din yace "Allah ya sanya alkhairi me mata biyu" Jay ya wani kallesa, Mikewa Ajay yayi zai bar wajen Jay ya sa masa kafa sai gashi timmm ya fada kan kujera, juyowa yayi ya hade rai yana kallon Jay da ya fara dariya, yaushe rabon su zauna waje daya a gidan, har magana ma sama sama suke yi...

Jay ya dakata da dariyan da yake, sai kuma yayi kasa da murya yace "So what did you think about all this?" Ajay yace "About what?" Jay ya juya ya kallesa bai ce komai ba, Ajay yace "Getting married to ur Ward?" Jay dai kallonsa kawai yake, Ajay ya
an yi murmushi yace "All this while ka zata wataran zan so ta ne da kake creating attitude a gidan nan?

Saboda me ma zan so ta?

Dama shi son haka yake very cheap?

Ai ba class dita bace yarinyar nan, i like nothing about her most especially her silly cry, duk abinda nake mata saboda kai nake mata, if not because you bazan ta
a saninta from anywhere ba, ba ma abinda zai sa nayi crossing path da ita, so chill bruh....

Just that har na fara hango maka challenges din da zaka yi facing a wannan familyn naka, considering the fact that ta ta
a aure, sannan she is a nobody, familynka kuwa basa son someone that is a nobody not to talk of bazawara, kaga you have to tighten up ur belt kayi facing all the up and downs that will approach you....
Chapter 154 · 0% Book details