← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 217 OF 218

Sashe 217

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Nenne tace
Kwarai kuwa, dan sarki ne mijin nata
Hajiya Zaliha tace
Ikon Allah
Mamaki ba kadan ba Hajiya Zaliha tayi, daga baya kuma taga meye ma abun mamaki a dai yanda Khaleesat take wanda ya fi dan sarki ma zai iya fitowa yace yana sonta don haka ba abun mamaki bane, ita kanta tana admiring komai na Khaleesat, tun da Hajiya Zaliha ta ji gidan da za a kai Khaleesat ta kebance da Aunty Farida tace
Farida ina ga gaskiya baza a fara taba masu duk abinda suka saka a lefe ba, probably idan aka kai ta Bauchin in suna da wani event da za ayi a can sai tayi using na lefen, in ma da event din definitely an ajiye mata kayan da zata yi using, amma dai daga nan gwara a canza kudin nan da suka sako a shiga kasuwa a siyo mata duk abinda zata yi amfani da shi na kece raini in za a kai ta, hakan ma kamar an kara kankaro mata mutunci ne, hatta Alkyabba baza a taba na lefen ba tunda ga kudi gwara a siya kawai, amma dai ban san yanda ku kuka tsara ba gaskiya, ina magana ne bayan na duba gidan da za a kai ta Kinsan irin wannan babban gida ba dai kananun zance ba, gwara su ga bata taba komai a kayansu ba hakan zai fi armashi
Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace
Wannan gaskiya ne Aunty, sai a je kasuwan kawai, nima nayi wannan tunanin wallahi, duk da akwai lapaya uku da na siyo mata da takalma da jaka, sannan akwal kayan dinkin ta da aka kawo jiya, amma gwara a karo mata wasu masu tsadan
Hajiya Zaliha tace
Amma sai kin yi shawara da Nenne da mahaifiyarta, wannan abu dai abu ne sau daya in a life time, so gwara ayi mata abinda ya kamata duba da inda za a kai ta ma
Aunty Farida tace
Toh ba damuwa bari in masu magana Aunty Ajay ya kira Jay for the countless time but he still can
t reach him, shi damuwarsa kawai yasan inda yake so they can talk, he needs to speak to him badly, shi dai yasan bai san ta yaya ba but probably they might arrive at a solution together idan suka hadu duk da bai ma san wani irin solution din ba at this point, gaba daya kansa a kulle yake tun jiya yake nazarin yanda zai billo ma al
amarin amma ya kasa arriving at any solution, duk tunanin da yayi sae yaga ba mafita bane cause he might end up disappointing his father, ko baccin kirki bai samu yayi daren jiya ba, har yanxu kuma kamar mafarki yake ganin al
amarin, ya kasa gane ta yaya Mai martaba ya iya switching comfortably without even considering the consequences after, a iya rayuwarsa bai taba zama confuse and lost kamar haka ba, bai ma san ko Jay zai yarda he knows nothing about the sudden switch ba, he don
t even know if he will believe him, ba a good 5 minutes Jay bai fado masa a rai ba and he is just restless, in his wildest dream he never saw this coming, bude kofar parlonsa aka yi ya daga kai da sauri, Mami ta shigo parlon kana ganinta kasan tana cikin tashin hankali matuka, tun da ya kalleta sau daya ya dauke kai, ta karasa har tsakiyar parlon cikin rawan murya tace
Amma ka bani mamaki Junaid, wallahi ka ban mamaki, ban yi tunanin zaka yi ma Jawwad haka ba, baka duba irin son da yake maka ba da irin goya maka bayan da yake yi in every situation ko da kai ne baka da gaskiya, baya taba sauraron wanda zai karanto masa laifin ka har ni kuma, a kan ka Jawwad sai ya rufe ido ya gaya min babu dadi, duk abinda zan ma Jawwad bazai daga ido ya kalleni ba amma inyi kuskuren fadan wani aibu a kanka ranan sae abinda ya manta ne bazai gaya min ba cikin fushi, ya dauke ka tamkar wanda ku ka fito ciki daya, ya dauki son duniya ya daura maka and he is always ready to protect you at anytime amma wai kai zaka ci amanarsa ka auri warce kasan yake bala
in so kawai don nace ba yanxu zai aureta ba sai nan da warni Lokaci
.

Kuka ta fashe da shi sosai tace
Daga kai har Sarki kun nuna mana iyakarmu da ni da Jawwad a gidan nan, wallahi da da zuciya daya kake zaune da Jawwad ko sarki ne yace zai aura maka yarinyar nan baza ka amince ba duk yanda zai yi da kai kuwa, instead fighting zaka yi har sai kaga Jawwad ya samu, amma saboda baka tare da Jawwad da zuciya daya you are just using him shi ne zaka yi masa irin wannan sakayya ka auri budurwarsa, don Allah ka gaya min meye ribar ka Junaid?

Ajay dal different direction yake kallo amma duk yana sauraronta, Infact mamaki ma ya sa yayi stiff kawai a inda yake zaune jin kalaman Mami, cikin kuka Mami tace
Magana nake maka kake kallon wani waje daban, ka gaya min me da na yayi maka da kake son ganin downfalt dinsa haka?

Is it a crime don ya nuna yana yin ka, kuma yana goyon bayan ka?

Ajay ya kalleta kamar bazai ce komai ba, can dai yace
I new nothing about this marriage, ban san komai a kai ba, ke kika ce ma Mai martaba ya maida auren kaina which he did, ni ban san komai a kai ba, bai kuma yi shawara da ni ba
A fusace Mami tace
Baka san komai a kai ba amma auren ke kanka har yanxu kuma ga ka zaune comfortable as if nothing?

In baka san komai a kai ba al birkice ma Sarki zaka yi kace baka son auren baza ka iya cin amanar dan uwan ka ba, idan yaga ka daga hankalin ka ai zai nemi mafita, kuma ta nan ne zai san yayi babban kuskure abinda yayi, da nace ya maida auren kanka idan har ya dau Jawwad matsayin da sai yayi hakan?

Wallahi duk abinda ya samu da na bazan taba yafe maku kai da Sarki ba, i will never forgive you two kuma sai na fito na sanar ma duniya duk abinda ake ciki babu abinda zan boye dama an dade ana ruwa kasa na shanyewa a gidan nan, an dade ana nuna mana iyakarmu ni da Jawwad, an kuma ci amanar Marigayi Yusufa, an ci amanar sa, da shi ne bazai taba yin haka ba, an ci amanar dan sa, in har wani abu ya samu Jawwad zan fito in sanar ma duniya komai wallahi
Cikin kuka sosal ta kare maganar, shi dai Ajay kallonta kawai yake don bai ma san me zal reba, Lace Dania sat da na ce ma jawwad shi ke son katsakani da Allah amma ba kai ba, kawai kana, using dinsa ne, shi kansa za gane hakari yanxu, tunda gashi ka ci amanarsa, in har ka cika dan halak samun Sarki zaka yi duk yanda zai yi yayi a warware auren nan da ya daura da kai, amma sain ka cika dan halak
Tana kai wa nan ta fice daga parlon Ajay ya bi ta da kailo, bai taba ganin mutum that is so perfect in manipulation kamar wannan matar ba, cikin few minutes ta juya lamarin ta dawo ita ce victim din, jinginar da kansa da yayi masa nauyi yayi ya lumshe idonsa, he wish zai iya da ya sake samun Mai martaba amma bazai so ya bata masa rai ba, don bata masa rai da aka yi tun farko shi ya ja har yayi wannan abun da yayi
.
Chapter 217 · 0% Book details