← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 218

Sashe 54

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Karfe hudu saura suka sauka Nigeria washegari Friday, ita dai Khaleesat tun da ta ganta Lagos bayan ta gama da Custom da Immigration ta fara tunanin kuma yanda zata yi, to ko dai kawai ta tafi gidan Aunty Farida tunda a nan Lagos take, to ko tace zata je bata da sim din da zata kirata don ba gane anguwan zata yi ba kuma bata da lambarta a kai balle ko waya ne ta ara ta kirata a airport din, sai kuma tayi tunanin kiran Ummanta tunda tana da numberta a kai sai tace ta turo mata number Aunty Farida, gun wata mata warce taga kamar Bahaushiya ce ta nufa, ta gaisheta sannan tace "Don Allah Aunty wayarki zaki ara min in
an yi kira nawa ba caji" Matar ta fara kallonta daga sama har kasa, sai kuma ta bude handbag dinta ta ciro wayarta ta mika mata, Khaleesat ta amsa tace "Nagode" Dialing number Umma tayi ta kira taji a kashe, sosai jikinta yayi sanyi, ta kira har sau uku duk ana ce mata a kashe, a hankali ta zame wayar a kunnenta ta mika ma matar tace "Nagode, wayar ma a kashe yake" sai da matar tayi dialing wayar ta tabbatar eh a kashe din yake, kana ganin matar kasan she is not comfortable giving off her phone, Khaleesat na jan trolley dinta a hankali ta fito daga cikin airport din tana tunanin yanda zata yi, ko dai kawai ta tafi tashan da zata samu mota zuwa kano, since she have some money in her bank account, wani mutumi ne taga ya nufota, ya gaisheta da ladabi yana mata barka da zuwa, sannan ya nuna mata mota yace "Ke mu ke jira ki fito dama" She was looking at him with confusion, can ta kalli motar, shi ko har ya amshi Akwatunanta yayi booth din mota da su, sannan ya dawo ya bude mata back seat, zata yi magana sai ta hango AJ zaune front seat din motar, ta
an yi jim, sai kuma ta fasa cewa komai, ta tafi ta shiga motar, hotel drivern ya kai su kasancewar next available flight to lagos na karfe bakwai na magrib ne, dakin da aka biya mata na downstairs, shi kuma AJ sama taga ya tafi, All this while kuma bai ce mata komai ba, ita dai tana son ce masa ta gode amma bai bar space din hakan ba, ko tsayawa bai yi ba balle tayi godiyan, sai da driver din ya amshi passport din ta da zai mata booking din jirgi tare da AJ zuwa kano sannan ya bar hotel din, bayan Khaleesat ta shiga dakin babu dadewa aka kawo mata lafiyayyen lunch, duk da tana jin yunwa bata iya ta ci da yawa ba she is just restless, taje bandaki ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, bayan ta saka wasu kayan tayi sallah sannan ta dau handbag ta bude zata ciro lip gloss dinta, a nan taga kudin da Jay ya saka mata, ta dinga kallon kudin ko kiftawa bata yi a sanyaye.

Karfe shidda da yan mintuna drivern ya sake zuwa ya daukesu ya maida su airport, daga nan kuma suka hau jirgi zuwa garin kano, inda suka sauka airport din Aminu kano karfe tara saura na dare, this time around ma sai da drivern da ya zo daukan AJ ya sauka yayi mata magana tare da kai akwatunanta booth, ita dai tana ta tsaye don taxi kawai ta so dauka da zai kai ta gida, ganin drivern ya bude mata back seat ta karasa jiki a sanyaye ta shiga motar, sai da suka fita daga Airport din drivern ya kalleta ta madubi yace "Ranki shi dade wani anguwan za a ajiye ki?" Khaleesat ta
an kalli AJ dake zaune gaban motar yana danna wayarsa, sai kuma ta kalli drivern tace "Inda zan je da nisa, kar in bata maku lokaci gashi dare yayi, duk inda ka samu kawai ka ajiye ni zan samu abun hawa" Sai a sannan AJ yace "Ce maki yayi sauri yake?" Khaleesat tayi shiru, sai kuma tace "Ni Mariri zan je" Driver yace "Toh Allah ya kai mu lafiya Hajiya" Bayan tafiyar kusan minti arba'in suka iso Maririn, A hankali Khaleesat dake kallon drivern tace "Zan iya sauka a nan sai in karasa cikin layin saboda kar ku shiga baku samu wajen juyawa ba...." Drivern yace "Layin baya bulla ne?

In dai yana bulla babu damuwa za mu samu hanya in sha Allah" Tace "Toh shikenan, nagode" Nan ta nuna masa inda zai bi ya shiga unguwan, shi dai AJ kallon ikon Allah kawai yake without uttering a word, haka jama'an anguwan suka dinga bin motar da ya dalle ko ina da haske da kallo, ba ko wani mai mota bane zai yarda ya shiga hanyar nan da motarsa cause driving is uncomfortable there in baka yi hankali ba sai ka goge motarka, gashi gidan nasu can ciki ciki ne, at last dai tace "Kawai in ka samu waje a nan zan sauka, ga gidan can" Drivern yace "Toh shikenan Hajiya" Haka ya samu yayi parking motar, sannan ya sauka zai dauko mata akwatunanta a bayan booth, ta bude motar ta sauka tana kallon kofar gidansu hankalinta ya
an kwanta ganin bata ga Babanta a kofar gidan ba, kan kace me yara yaran anguwan da suka ga ita ce a motar suka taho da gudu ana mata oyoyo, haka dai ta samu ta hadasu da akwatunanta sannan ta zaga zuwa side din da Ajay yake, tana wasa da gefen gyalenta ta kasa kallonsa tace "Thank you so much Allah ya saka da alkhairi" yace "Wanda ya hada ki jirgi daya da ni zaki ma godiya, Jay kenan" Sai a sannan ta
an kallesa, bata dai ce komai ba ta juya tana tafiya a hankali ta bar wajen, godiya tayi ma drivern ta masa kwatancen unguwan da zai shiga wanda a nan zai samu hanyar billa zuwa titi, yayi mata godiya shima ya shiga mota sannan ta nufi cikin gidansu gabanta na faduwa, a hankali tayi raising sack din cement that was use as barrier between the door and inside of the house zata shiga cikin gidan ta ci karo da kanninta da suka fito yi mata oyoyo da gudu bayan yara sun shiga da akwatunan ta, a haka suka shiga cikin gidan tare tana Rungume da su, zazzaune taga kishiyoyin ummanta biyu da 'ya yansu rakacaa a tsakar gidan har a lkcn ba a sauke tuwon dare ba gashi ana neman karfe goma, kananun yaransu ne kawai suka taso yi mata oyoyo da gudu, muryar wata makociyarsu dake zaune cikin gidan taji tana cewa "Ikon Allah sannu da zuwa Amarya ashe dai kina hanya dama" Khaleesat dai kallonta kawai take jin abinda tace, taji kishiyoyin ummanta na cewa "Ai ko dai, kinga mu da muke gidan ma ko gaya mana ba ayi ba balle mu shiga mu fita tahowar nata ya fasu, kinsan haka aka maida mu a gidan, to ga dai ta mun ganta kamar an jefota, mun kuma yi murna" Khaleesat ta gaishesu without waiting for response ta shige dakin Ummanta, zaune ta ganta a bakin kofa Umma dake kallonta cike da damuwa tace "Khaleesat me ya samu wayarki kusan wata daya?

Dama kina hanya shine Abdul din bai gaya mana ba?" Khaleesat ta rungumeta a hankali tace "Umma lalacewa wayar yayi" Umma ta dago kanta tana kallonta tace "To shi ya dauko ki a tashar jirgin?" Khaleesat ta sauke idonta tace "A'a" Muryar kawar Ummanta da taji a dakin yasa ta daga kai don bata ma san tana ciki ba, Khaleesat ta gaisheta da murmushi, Mama Salame ta amsa da fara'a tace "Ashe dai kina hanya amarya" Khaleesat tace "Amarya kuma Mama?" Mama Salame tace "Au shi Awdul din bai gaya maki ba dama, ai yau ana saukowa sallan juma'a aka daura auran ku"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
HALYSAAH 27...
Chapter 54 · 0% Book details