Sashe 181
Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Karfe sha biyu da yan mintuna Nenne ta shigo gidan fuskarta babu yabo babu fallasa, har ta cire gyalenta zata rataye saman igiya ganin tsakar gidan cike da hayaki don su Mama Shatu na ta girkin siyarwan su ta fasa ta nufi dakin Umma da gyalen a hannu, ko amsa gaisuwan su Mama Shatu bata yi, tun da Umma taji muryar Nenne ta fara ma Khaleesat mita tace "Sai da nace ki je ki gaisheta kafin ta samu labari kin dawo, yanxu sai abinda ta manta ne bazata fada mana ba" Khaleesat dai na kwance saman gadon Umma tana danna wayarta, tun da tayi breakfast take son tayi bacci amma yan unguwan sai shigowa dakin Umma suke wai yi mata sannu da zuwa, alhalin da yawansu gulma ce ke shigo da su ba komai ba, ga Sha'awa da taki tafiya tun da ta shigo dakin kusan awa daya da rabi kenan, har da wasu makotansu biyu duk sun zauna sun ki tafiya ko me suke jira oho, Nenne na tsaye daga bakin kofa don labulen dakin a
age yake tace "To Zahra'u sai me don Khaleesah ta dawo anki zuwa a gaya min ko kuma a turata ta gaisheni har sai da almajirina ya shigo ya gaya min, naga dai ba don ni ba ai ko iyapot bazata sake zuwa ba balle har ta koma wata Amurka, kuma ba wani ya haifar min uban nata ba dai da za a dinga nuna min an fi ni iko da ita" Khaleesat dai tayi murmushi ta sauko daga kan gadon ta zauna kasa tace "Sannu da zuwa Nenne" Nenne ta kauda kai ta tsirtar da yawu ta kalli su sha'awa tace "Su kuma wa ennan fa?
Baku ganin dakin babu sarari gashi duk ya dume bayin Allah sai sha
an numfashin juna ake, ke sha'awa zanin daddawan naki kika shigo dakin mutane da shi kika zauna?
Haba ki dinga ji tsoron Allah mana sha'awa" Mikewa sauran makotan biyu suka yi suna kallon Khaleesat suka ce "Allah ya huce gajiya Khaleesah" Daga haka suka nufi kofa suna gaida Nenne suka fita, Nenne ta tsirtar da wani yawun tace "Tab
ijam...." Sha'awa ta mike tace "Nenne shigowa ta kenan babu dadewa na zo yi ma Khaleesah sannu da zuwa, ashe ma tun da safe ta iso, ina can na gama curin daddawa ban san ta dawo ba" Nenne ta bata hanya da sauri don kar ta goga mata jikinta, a haka Sha'awa ta fita daga dakin, Nenne ta kalli Umma tace "Lallai Zahra'u kina da aiki, ke ba kazama ba ki bar mata kazamai su shigo maki daki su cika da warin jiki har da me daddawa? duk dakin ki ya dume ba dadin sha
a? yanxu da kin yi bakon kunya ina zaki ajiyesa, ga daki ba daki ba kamar zuciyar talaka, halan ina parida ta tafi don dai nasan da tana nan da tuni ta fatattake yan iska ta koresu, to dai duk komai ya zo karshe, Alhamdulillahi tun da Khaleesah ta dawo lafiya zuwa nan da yan kwanaki kadan sai mu tattara mu bar tsinannen unguwan nan mu koma inda bawon Allahn can
an albarka Ahmad ya siya mana, dama dai ni ce nace lallai sai an jira ta dawo tunda ta dalilinta aka yi mana wannan abun arziki baza mu yi mata butulci mu tare a gida babu ita ba, shi ne nace lallai ita zata jagorance mu zuwa sabon gidan a bude mu shiga cikin farin ciki, saukan al-qurani dama na saka anyi yafi a kirga a gidan, shikenan Allah ya rabamu da masu warin unguwan nan kuma haka" Nenne ta ajiye kwanon hannunta tace "Ga shi nan kwadon zogala na maki da naji ance kin dawo, to Ahmad din fa?" Khaleesat tace "Sai anjima zai shigo" Nenne tace "Ai ko bari in maza in tafi in
ora masa tuwon shinkafa da miyar agushi, in bada dubu biyu a siyo min nama me kyau in zuba a miyar" Daga haka ta juya da sauri tana yafa gyalenta ta nufi kofar fita daga gidan, Umma dai murmushi kawai tayi, Khaleesat ta kalleta tace "Dama Nenne ce tace baza a koma gidan ba Umma?" Umma tace "Gashi nan ta gaya maki kuwa, babanki ma bai yi na'am da gidan ba har yanxu" Mikewa Khaleesat tayi bata ce komai ba, ta dauko kwanon da Nenne ta ajiye mata ta bude, ai ko taji dadin ganin zogalen don hadadden hadi Nenne tayi masa.
Wajen karfe hudu da rabi Jay ya zo gidansu Khaleesat, bayan sun gaisa da Umma da Aunty Farida Khaleesat ta dauko masa bottle water din da ta siyo masa ta ajiye masa, Aunty Farida dai sai godiya take masa ya ma kasa kallonta yana
an murmushi kawai, Khaleesat ta zauna gefen Ummanta tana kallonsa babu ko kiftawa, tsadadden Gezna ne fari jikinsa, kayan sun masa kyau ba kadan ba, anya ta ta
a ganinsa da manyan kaya kuwa, ya fito sak Hausa Fulani yau, Aunty Farida tace "Za ku karasa can gidan Nenne da shi ai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai sannan ta mike, Hijab dinta ne har kasa jikinta dama, ta dau nikab ta
ora, ta fita tsakar gida tana jiransa, after almost 5 minutes ya fito daga dakin, step mothers dinta dake tsakar gida duk suka kafesa da ido kamar yanda suka yi san da ya shigo, Khaleesat dai ko kallonsu bata yi ba ta nufi kofar fita gidan ya bi bayanta, sai da suka fita kofar gida ya kalleta yace "What is this u are covering ur face with Halysaah?" Dariya tayi tace "Nikab ne baka sani ba?" Kallonta kawai yake suna tafiya, can yace "Tell me why you are covering ur face?" Tana murmushi tace "Saboda kallona za ayi ta yi a unguwan, kuma na saba sakawa in zan fita dama" Murmushi kawai yayi bai ce komai ba, a hankali tace "Ko in cire?" Ya kalleta yace "A'a, gwara haka, kinga za a rage kallon ki" A haka suka isa gidan Nenne, Nenne ta rasa inda zata sa Jay tsabar tarba, ta kinkimo masa gaba daya coolern tuwon da tukunyar miyan ta dire a gabansa, lemon kwalba kuwa dama guda biyar ta sa aka siyo masa da ruwan gora biyu, shi dai sai murmushi yake gashi ba yunwa yake ji ba, Khaleesat ma sai murmushi take, can ta cire nikab dinta ta ajiye, Nenne tace "In ma kunyata kake ji bari in shiga makota ka ci tuwonka ka koshi, don kai kadai nayi tuwon nan wallahi in ma baka ci da yawa ba wallahi bazan ji dadi ba, wanda ka rage ma a leda zan juye maka ka tafi da shi, ni ko gurin Zahra'u sai in je anjima ta tsam min tuwon daren ta..." Daga haka Nenne ta yafa gyalenta ta fita daga gidan, Khaleesat sai kallonsa take tana murmushi, ya cire hulan kansa ya ajiye gefe don har ya fara zufa ganin abincin da aka dire masa, yana kallon tuwon yace "Ya za ayi da tuwon nan Housemate, Ni fa na ci abinci kafin in fito wallahi" Khaleesat tayi dariya tace "Haka nan zaka tuttura ka ci, kasan tun yaushe take maka girkin nan kuwa?" Plate ta jawo ta saka tuwo daya, ya zaro ido yace "I can't finish even quarter of this Halysaah, a koshe fa nake" Dariya kawai take bata tankasa ba ta bude tukunyar miyan dake ta kamshi ta zuba miyar a wani bowl daban, ta saka nama yanka hudu, ta maida tukunyar miyar gefe tace "Oya gashi" Ya kalleta yace "Where am I going to start from?
Billah I am full, ki ci don Allah..." Khaleesat ta wanke hannunta ta dau cokali ta dibi tuwon da miya tana kallonsa tana murmushi, yayi kasa da murya yana kallonta shi ma yace "Ko feeding dina zaki yi?" Murmushi tayi ta sunkuyar da kai don hakan take son tayi amma kunya ya hanata yi, yace "In dai zaki yi feeding dina zan ci wallahi" Dakewa tayi ta kai masa tuwon baki ya amsa yana murmushi, nan da nan yaji ya samu appetite din cin tuwon....