← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 218

Sashe 70

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama Safiyyah ta daga buhun dake makale kofar shiga compound din gidansu Khaleesat, Mama Shatu da Mama Zubaida ne tsakar gida ko wacce na zaune bakin murhunta ana girka abincin talla hayakin icce duk ya cika ko ina na gidan, Mama Zubaida sai mita take an siyo masu jikakken icce, gaishesu Safiyyah tayi suka amsa ana mata wani kallo kasa kasa, Safiyyah ta tsaya suka gaisa da Labiba dake wanke robobin da za a zuba abincin siyarwa, sannan ta nufi dakinsu Khaleesat ta daga labulen ta shiga da sallama, zaune ta tarar da Umma ta jingina da bango hannunta rike da carbi ga kawarta Mama salame da wata Zaliha makociyarsu sai Sha'awa ita ma makociyarsu zaune dakin ko wanne yayi jigum, zaunawa Safiyyah tayi tana kallon Umma ko gaisheta bata yi ba ganin yanayinta tace "Umma baki da lafiya ne?" Umma tayi karfin halin cewa "Sannu da zuwa Safiyyah" Safiyyah ta gaisheta sannan ta gaida sauran mutanen dake dakin, ta sake maida dubanta kan Umma kan tace komai Mama Salame da ta san kawar Khaleesat ce ita tayi kasa da murya tace "Tsakaninki da Allah Sapiya baki san inda kawarki Khaleesah take ba?" Safiyyah ta zaro ido tace "Kamar yaya Mama?" Sha'awa ta gyara zama tace "Ae tun ranan asabar rabon da a saka Khaleesat a ido, daga ta dawo kasar waje ta tarar an daura mata aure da audallah washegari Asabar aka nemeta aka rasa, babu inda ba a shiga neman Khaleesah ba amma babu ita babu labarinta, jiya jiya yan sanda suka zo suka tafi da Malam Ali" Safiyyah da ta shiga wani shock jin wai an daura ma Khaleesat aure da Abdul ta ajiye jakarta a gefe ta dafe kirji tace "Wani Abdul din aka daura mata aure da?" Sha'awa na gyara barkakken zaninta tace "Audullah saurayinta dai da kika sani, ranan juma'an nan da ta wuce aka daura masu aure, tana dirowa kasar aka sanar mata shine ta gudu har yau babu ita babu labarinta, gashi an tafi da Malam Ali an kullesa" Safiyyah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mikewa tayi tsaye ba tare da tasan tayi hakan ba tsabar shock din da ta shiga maganganun Sha'awa na yawo a kanta, hawaye ne ya cika idonta tana girgiza kai ta kasa cewa komai, ina jin bayan Khaleesat da tayi bakin cikin auren da aka daura mata da Abdul idan aka cire su Jay babu wanda yayi bakin ciki kuma irin Safiyyah, don ji tayi kamar an aza mata katon dutse a kirji tsabar bakin cikin wannan labarin, kawai ta fashe da kuka cike da tausayin kawarta, Abdul fa??

Housemate din Khaleesat ne ya fado mata a rai, nan Safiyyah ta dinga rera masu kuka kamar ita ce Khaleesat din, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana kunduma ma su Mama Shatu da Mama Zubaida zagi tana cewa "Wato har sararin kunna rubabbun murhun ku kuka samu a gidan nan baku dubi bala'in da ake ciki ba, ai in dai
a ne kowa ma ya haifa wallahi, yanda ku ke nuna halin ko in kula da abinda ya samu
a na ku ma dai kun haifi 'ya yan nan naga, shegu masu fararen kafafuwa tunda
a na ya auro ku yake shiga bala'i sinka sinka a duniya amma saboda baku da imani da tausayi ko wacce ta zauna bakin shegen murhun ta" Mama Zubaida ta kauda kai tana tabe baki tayi kasa da murya tace "Sai kuma yunwa ta kashe mu saboda yan sanda sun zo sun dauki Malam" Ita dai Mama Shatu sai juya miyarta take kar ya kone taki ko kallon inda Nenne take, Nenne na huci ta nufi dakin Umma ta dage labulen tana kallon cikin dakin tace "Saka dogon hijabi da rike carbi ba shine mafitarki ba Zahra'u, duk inda kika tura yarinyar nan waya kawai zaki buga masu ki ce ta dawo tun lamari bai lalace mana gaba daya ba, in ko ba haka ba wallahi sai a wanke daya daga kanninta a ba ma Awdul din tunda abinda yayi ta shi yayi su, in jar fata da gashi irin ta buzaye ne su ma duk suna da shi, babu abinda zata gwada masu sai shekaru tunda ta basu shekaru bakwai, don bazan zuba ido a karo na biyu
a na ya koma fursin ya tagay
yara ba, Allah kadai yasan nawa na kashe wajen shige shige har Allah ya bamu mafita a wancan lokacin da aka kullesa, tun asali bata san bata son Awdul din ba sai bayan da ya kashe mata uban dukiya da bazai lissafu ba?

Wace masifa ku ke son ja ma
a na ke da er ki a garin kano?

Shi kadai fa ya rage min namiji sai mata, wallahi ki fito da ita Zahra'u in ya so su riketa a sake min
a na, nasan har da hadin bakin makirar tsohuwar can Gaje, yanxu kuma zan kama hanya in tafi Hotoron duk inda ku ka boye Khaleesah sai kun fito da ita baza ku kara ja min salalan tsiya ba, sha'awa taso ki rakani gidan tsohuwar banzan can Gaje" Da sauri Sha'awa ta mike ta figi ba
in gyalenta ta fita daga dakin ta bi bayan Nenne dake huci suka fita daga compound din gidan, Mama Zubaida da Mama Shatu suka saki guda a tare bayan Nenne ta fita, Mama Shatu ta kyalkyale da dariya tace "Ana yi muna hura murhu, ma ga dai karshen wannan dirama me dadin kallo a gidan nan, su buzuwa sai a koma dajin da aka shiga aka nemo maganin farin jini ayi ma Malam bayanin lamari ya kwabe, ba dai 'ya yanmu bane munana masu ba
in jini, maji ma gani dai" Umma dake jin duk abinda suke cewa ta jinginar da kanta da bango hawaye na sauka idonta Mama Salame na bata hakuri, Safiyyah dai jingina tayi daga bango a inda take tsaye hawaye na zuba idonta ita ma, ganin abun take kamar a mafarki wai an daura auren Khaleesat da Abdul, to amma ina Khaleesat zata tafi tun ranan Saturday ita da tasan Khaleesat ko kawaye bata da su a kano, Housemate ne ya fado mata, ta dau jakarta da sauri tana share hawayenta ta fita daga dakin Umma, Umma ta bi ta da kallo hawaye masu zafi na bin idonta daga ranan asabar zuwa yau har ta rame, ko abinci bata iya ci ta kira Aunty Farida yafi a kirga akan ta zo gareta ko zata ji saukin radadin da take ji a zuciyarta, Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi Safiyyah da wani kallo suna tabe baki har ta fita daga compound din, Mama Zubaida ta matsa kusa da Mama Shatu da yake murhunsu kusa da kusa yake, tayi kasa da murya tace "Kin ga ki hakura da dafa waken nan da kika ce don gaskiya zai bata mana lokaci ga waje da nisa, gwara mu je a kara kada hankalinta taji ta tsanesa da auren kuma taki dawowa, in ya kama a kadata ta shiga duniya duk sai mu ce ayi, kudi ne dai zai yi kuka ba wani abu ba, kinga daga karshe in ma Labiba ko Lamisah duk wanda yace a basa duk daya ne a wajen mu babu banbanci, babu abinda zata gwada masu sai farin fata da uban gashi kamar na doki, in idanuwa ne su ma suna da shi, sannan suna da hancinsu dai dai gwargwado, tun asali kece kika yi ta makon fiddo kudi da ba a kai ga haka ba ma wallahi" Mama Zubaida ma tayi kasa da murya tace "Wallahi ban taba zaton aikin mutumin na ci haka ba Shatu, kinsan Malaman Jabu sun yi yawa yanzu sai dai ka kai masu kudinka su yi cefanen gidansu, shi sa kika ga ina ta ja da baya naki sakin kudi dama jarina ba jarin arziki ba, kinsan tun bayan rasuwar Malamin nan da yayi mana aiki kan Parida naki sakewa da Malamai don asaran kudi kawai mutum yake shi din dai ne malami gangariya amma mutuwa ta dauke mana shi kwatsam, gashi har yau duk uban kyan parida babu mashinshini tana can tana tuwo tuwo a Legas tana aiko ma yayar kudi kuma in sha Allahu a haka zata kare ga dai kyan da diri da komai amma babu mashinshini, to in anyi duniya don manzon Allah haka Khaleesar ma zata kare, amma yanxu tunda muka samu sabon Malamin nan naga aiki da cikawa kema kin san fiddo kudi bazai kara min wahala ba, ba gashi har na sa an amso min adashina ba daxu, in sha Allah sai mun karkato da hankalin Abdul kan 'ya yan mu, ko Labisah ko Labibah, ba dai kyau suke takama da shi ba wai su buzaye, to wallahi sai dai su ga ana aure....." Shiru Mama Zubaida tayi ganin Salame ta fito daga dakin Umma ta ci gaba da juya miyarta with serious face, Safiyyah na fita kofar gida ta ciro wayarta a jaka don tana da number Housemate, tayi dialing numbersa gabanta na faduwa tana hoping yasan whereabout din Khaleesat, jin Khaleesat take a ranta kamar er uwarta ta jini, she can't imagine halin da take ciki yanxu, yana fara ring Jay dake mota tare da Ajay ya daga wayar ganin Safiyyah ke kiransa yayi picking ya kai kunne calmly yace "How are you Safiyyah?" Da kyar Safiyyah tace "I am fine, ina kwana?" Yace "Lafiya lau, kin dawo Nigeria kenan?" Ta gyada kai da kyar tace "Pls tambaya nake son in maka Ya Jawwad" Jay yace "Ina jin ki Safiyyah" Safiyyah tace "Don Allah kasan whereabout din Khaleesat, wai tun Saturday ta bar gida har yanxu ba a san inda take ba, yanxun nan na zo gidansu nake samun labarin" Hawaye na zuba idonta ta kare maganar, a hankali Jay yace "Halysaah?" Lkci daya Ajay ya juya ya kallesa, sai kuma ya fixge wayar ya katse ya ajiye, Jay dai kallonsa kawai yake, can yace "Kawarta ce fa" Ajay yace "And so?

Assignment din announcing whereabout dinta aka baka ne?
Chapter 70 · 0% Book details