← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 218

Sashe 134

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai shine wahalalle dama" Tace "Ni ban fito da kai cikin sanyi ba, tunda ba cewa nayi ka zo ba ai, kawai kiranka nayi nace kace mutumin nan ya cire hotona a Instagram, amma ban ce ka zo ba" Kallonta ya dinga yi, at this point kamar he is lost of words, ta juya ta koma kitchen ta ajiye cup daya ta fito ta wuce sama tana rike da cup din nata shayin, still ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, Khaleesat na gama shan tea din ta kwanta ta rufa da duvet ta lumshe ido tana addu'an Allah ya sa kar ta kara mafarkin da zai firgitata kamar daxu, kamar warce ta tuna abu ta bude idonta a hankali, ta jawo wayarta tana dubawa ko Housemate dinta ya biyo kiranta bata sani ba, amma sai taga bai biyo kiran ba, har ta ajiye wayar sai kuma ta sake dauka a hankali ta kunna data dinta tayi login WhatsApp, tun call din da yayi mata da safe bata daga ba bai kara mata magana ta WhatsApp din ba, and he uploaded a status not long ago, sauke idonta tayi ta kashe datan ta ajiye wayar ta gyara kwanciyarta, nan da nan mood dinta ya canza, duk yanda ta so tayi bacci kasawa tayi, sai juye juye take har kusan karfe sha dayan dare, mikewa zaune tayi daga karshe ta cire duvet din jikinta ta dau Jacket dinta ta saka sannan ta bude kofar parlon a hankali ta fita, tsaye tayi a corridor din sama tana kallon Ajay dake kwance kan 3 seater idonsa a lumshe don wutan parlon a kunne yake, ta fi minti biyu tsaye tana kallonsa, sai kuma ta juya ta koma dakinta ta dau one out of the new duvet Jay got for her, ta cire farin duvet din daga pack dinsa sannan ta fito daga dakinta ta sauka downstairs, tana tafiya a hankali ta isa har inda yake kwance, gida biyu ta linke soft duvet din ta rufa masa a jiki, ba wai hannunta ya ta
a sa bane but she could feel he is running temperature, tana rufa masa Duvet din ya cire daga jikinsa ya wurgar ba tare da ya bude ido ba yace "Gerrout Jay...." Sai kuma ya fara kokarin juyawa a kan kujeran sai ga shi a kasan carpet ya fadi timm, rufe bakinta tayi da sauri, ita kanta bata san meyasa dariya ya taho mata ba don da har jikinta yayi sanyi after noticing that he is running temperature, amma wannan reaction din nasa yayi mugun bata dariya, cikin magagi yake cewa "Bana son haka Jawwad, why are you stressing me, gerrout pls, i think i caught a cold, can you help increase the room heater before getting out" Sai kuma ya bude ido a hankali yana dafe kansa da yayi masa nauyi cause bai ji Jawwad na responding ba, ita dai kallonsa kawai take da mamaki, he look so shock ganinta, ya fara bin parlon da kallo, sai kuma ya kalleta ya hade rai yace "Kee, fita ki ban waje" Bata san sanda tayi dariya ba tace "Ai to bani na fadar da kai kasa ba, ni kawai bargo na kawo maka, and you heavily fell down on the Carpet" Ya kara daure fuska yace "Get out of my sight, am i a joke to you?" Ta wani juya kai, sai kuma ta nufi stairs tana waigansa har ta haura sama ta shiga dakinta, sai a sannan ta fara dariya tana mamaki shi kuma haka yake, har bayan minti talatin Khaleesat bata yi bacci ba tana dai zaune dakinta, after a while ta mike a hankali ta kara fita daga dakin nata tana leka downstairs, bata gansa kwance a parlon ba, hakan yasa ta fara saukowa downstairs, ta kalli duvet din da ya ajiye saman kujera da makullin gidan, sai kuma ta kalli bakin kofa ta karasa can ta murda kofar taji a kulle, window ta tafi tana leka Garage taga babu motarsa, ta dawo parlon ta dau makullin gidan tana kallo taga ya cire guda daya a ciki, she felt somehow ganin bashi da lafiya kuma still ya bar gidan a haka gashi snow din raguwa kawai yayi, ta fi minti biyu a tsaye after a while ta dau duvet din zata koma sama taji vibration din wayarsa, dube dube ta fara yi amma bata ga wayar kan kujera ba, daga karshe sai karkashin kujeran taga wayar, kilan sanda ya fadi daga kan kujeran shi ne wayar ya shige karkashin kujeran, screen din wayar ta dinga kallo ganin Jay ne ke kiransa, tayi silencing wayar ta wuce sama tana rike da wayar da duvet, sau uku Jay na kiran wayar, ita dai ta ajiye wayar gaban madubi tayi kwanciyarta.

Washegari ta idar da sallan asuba bayan ta gama azkar dinta zata kwanta wayar Ajay ya fara vibrate gaban madubinta, ta dinga kallon wayar sai kuma ta karasa can tana duba screen din taga Jay ne still ke kiransa, ta juya ta koma saman gado tayi kwanciyarta, wajen karfe tara na safe ta gama shiri zata tafi school, tana tsaye gaban mirror din dakin tana kokarin daure gashinta sai ga Jay ya sake kiran wayar Ajay, ta dinga kallon wayar babu ko kiftawa sai kuma ta daga wayar ta sa handsfree bata ce komai ba, daga daya bangaren Jay yace "Why were you not picking ur calls Bruh, hope baka fita jiya ba cause naji anyi snow sosai, how are you doing?" Khaleesat dake sauraronsa ta sauke idonta tace "Good morning, he forgot his phone" Shiru Jay yayi daga daya bangaren for almost 10 seconds, can yace "Halysaah..." Tace "Good morning" Yace "Morning, where did he forget his phone?" Tace "In my apartment" Shiru Jay yayi bai ce komai ba, after some seconds a hankali yace "Ohk then" Daga haka ya katse wayar, Khaleesat ta dinga kallon screen din, sai kuma ta ajiye wayar tana kallonsa, sai bayan kusan minti daya ta iya ci gaba da gyara gashinta.

Bayan Khaleesat ta gama abinda take ta saka wayar Ajay a jakarta zata tafi school da shi incase yaje zai amsa a department dinta, bata nuna ma Safiyyah komai ba da suka hadu a school duk da har sannan she is still very much angry at her, Safiyyah na kallonta tace "Yanxu dai sai hankalin ki ya kwanta don naje na duba na ga Aymaan ya cire hoton naku a account dinsa, ko wa yayi masa magana oho, ni kuma gashi bai min reply din WhatsApp message dina har yanzu ba" Khaleesat tace "Toh in ba dai he is irresponsible ba ta yaya zai dau hotona bai san ni ba yayi posting a account dinsa?

Bai ma dau matarsa da muhimmanci ba in dai haka ne, who does that?" Safiyyah tace "Atoh, nima dai haka naji aka ce yana da mata amma ban sani ba ban kuma tabbatar ba" Khaleesat ta kalleta baki bude, Safiyyah tace "Wallahi kuwa, haka naji ana cewa, kuma wai yana da ciwon zuciya, ni dai bai min kama da me ciwon zuciya ba kuma ban ma yarda da wnn labari ba, kinsan yan mata na jin haushinsa saboda sai wanda ya ga dama yake kulawa shi yasa aka masa wannan sharrin, amma ki kalli mutum lafiyayye kamar sa a wani ce ciwon zuciya, gashi da son zuwa club" Khaleesat ta ma rasa abinda zata ce ma Safiyyah, kawai ta kauda kai don lamarin Sophie ya fara bata tsoro, the way she is saying it kamar bakinta da bakinsa suka yi magana ya gaya mata yana da ciwon zuciya kuma yana da mata, Safiyyah tace "Ni dai tashi mu je mu ci abinci yunwa nake ji, kilan ma haushin an sa shi ya cire hoton ne ya sa yayi banza da ni ta WhatsApp kuma na kirasa yaki picking, dama an masa shaidan girman kai and he is way too pompous of himself, bazai wuce Housemate dinki ya san sa ba shine yayi masa magana ya sauke hoton, dama ni fa sam gayen bai min ba ga wani jijji da kai da yake wai shi
an gidan Deputy sai kace
an vice president, deputy governors da ba a ma san da zamansu ba a Nigeria, gani yake yafi kowa a haka fa, kina kallon idonsa kinsan bazai rasa shan drugs ba" Khaleesat tace "Amma dai yanxu idan Abdul yaga hoton nan me kike tunani Safiyyah?" Safiyyah ta mike tace "Waye kuma Abdul?

Pls mu je mu ga abinda za mu siya mu ci yunwa nake ji wallahi" Har Khaleesat ta bar school ranan bata ga Ajay ya zo amsar wayarsa ba, hakan kuma yasa taji a ranta he is sick.

Mamaki abun ya ba Khaleesat ganin har ta dawo school Housemate dinta bai kirata ba ko kuma yayi mata magana ta WhatsApp, wayar Ajay ma bai sake kira ba, sai dad dinsa da ta ga ya kira wayar har sau biyu, da daddare taji zuciyarta ya kasa daurewa kawai tayi ma Housemate din nata magana via WhatsApp, ta gaishesa sannan ta tambayesa ya jikin cousin dinsa, after almost 15 minutes yayi mata reply da Alhamdulillah, daga nan kuma bai sake cewa komai ba, she was taken aback, haka nan ta ajiye wayarta kawai ta kwanta tana jin wani iri a zuciyarta.
Chapter 134 · 0% Book details