← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 218

Sashe 139

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na shiga uku, sai aka yi yaya?" Khaleesat taki bata amsa don takaici, Safiyyah ta hade rai tace "To kuwa sai nayi masa hauka, uwarsa yaje nema maki a gida ko an gaya masa kowa shege ne kamar sa?" Kallonsa kawai Khaleesat take daga nesa har ya nufo inda suke zaune, Safiyyah kuwa ko lura da shi bata yi ba rai bace take cewa "To ke baki kira masa Cops ba? don Allah ki gaya min sai aka yi yaya da yaje apartment din naki?

Yau ga mahaukaci kai" Juyawa Safiyyah tayi ganin shadow din mutum a gabansu, yana kallon Khaleesat da kyau yace "Kara ta kika kai gun wancen garan don ya min me?

Me kike tunanin zai iya min?

Muscles dinsa na banza har ni zai nemi ya daka?

Who did he think he is?

Me yake takama da shi?

Sarautar tasu da bata taka kara ta karya ba ko me?

Sannan naga kamar yana mance a America mu ke not Nigeria, ni zai nuna ma dabanci bai san course dinsa nayi a Nigeria ba?" Safiyyah ta mike tace "Look Aymaan, ita fa Khaleesat ba irin wa ennan shegun matan da kake tunani bane gaskiya, ka bar ganinta sakaka a Amurka, yarinya ce ita me mutunci da ta san ciwon kanta, kuma harkar duniya bata gabanta wallahi, wannan get together din ma ni na ja ta don dole taje ba wai ra'ayinta bane shi yasa throughout ta kebe gefe daya a wurin u saw that too, shi kuma wanda kake kira da gara fiance dinta ne, ba wai shisshigi yake yi ba, sannan sarautarsu kuwa ta taka kara ta karya don gidansu a nan Amurka ma ba ko wani shege bane a Nigeria ke iya mallakan irin wannan babban gidan a wata kasar, kai kuma naga hayan apartment kake a Amurkan, Sannan iyayen Khaleesat basu fara turata wata kasa karatu ba sai da suka tabbatar da mijinta a hannu, kuma shi ma a kasar yake, ka ga ai baza kace masa gara ba" Aymaan na mata wani kallo yace "Ke ki iya bakin ki kar ki ja ma kanki matsala a rayuwarki, Fiance din banza, a ina Fiance ya zama miji? ranan daurin aure ma an fasa balle common Engagement, shi da Engagement din yake takama dama?" Safiyyah tayi wani shewa tana rike kugu tace "Na ga kamar ba zaman lafiya kake so ba Malam, to wallahi idan baka fita harkar kawata ba a kasar nan a gaban idon ka zan kira maka 911 in lafta maka sharrin da babu me fitar da kai sai Allah, kamar yanda ka fada nan ba Nigeria bane tuni za ayi mana maganinka wallahi, kuma Unguwan da take tsaf za a bincika surveillance camera a ga sanda ka shiga apartment dinta ta yanda za a tabbatar ba sharri aka maka ba..." Aymaan ya gyara tsayuwa yana kallonta da kyau yace "Really?? dama ke mahaukaciya ce ban sani ba?" Safiyyah tace "Dawanau ce ni karewa, wallahi idan baka yi hankali da mu ba a kasar nan zaka ga jahilci tsantsa, ai ni da nake ganin ka sumi sumi a makaranta ban san gogaggen dan iska bane kai sae yanxu, to banda
an iska waye zai fada apartment din mutum kamar gidan ubansa?

Ashe dama ciwon
walwa gare ka ake yada jita jitar ciwon zuciya gare ka?" Har ya daga hannu zai wanka mata mari sai kuma ya rike fist dinsa ya cije hakora yana kallonta yana huci, Safiyyah tayi wani dariya tace "No slap me, try it plss, mare ni mana.... wallahi rabon ayi deporting dinka back to Nigeria a cikin jirgin ruwa ne ke tunzura ka, try slapping me ka ga ikon Allah" Yace "Daga ke har kawar taki zan yi maganin ku wallahi...." Daga haka ya juya kamar zai tashi sama ya bar wajen, Safiyyah tace "Ni wallahi da aka ce min babanka Deputy ne sai da kunya ya kamani ranan na rufe fuska, na zata
an vice president ne kai irin wannan jijji da kan da kake ashe common Deputy ne ma da ba a san da ku ba a Nigeria, kuma in ka fasa maganinmu baka cika namiji ba wallahi, dama ana ganinka an ga kwararren
an shaye shaye
an codeine, ban san wani tsautsayin yasa har mu ke gaisawa da kai ba banda nima dai gantalalliya ce bani da kamun kai"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via 0902 469 2720_
HALYSAAH 66
Khaleesat tsabar yanda ta zama shock kasa cewa komai tayi a inda take zaune kamar ruwa ya cinye ta, ta shiga uku ita kam ga kuma wani da yafi Abdul tashanci, Safiyyah na huci tace "Ta shi mu je, don dai ban san yanda ake yi bane a kasar nan, da Nigeria ne ai daga nan police station na nufa in je in kai report, to su nan ban san ko ana haka ba" Ita dai Khaleesat ta kasa tashi don duk jikinta yayi sanyi kamar an watsa mata kankara, Ganin Khaleesat taki tashi Safiyyah tace "Ki tashi mu tafi don Allah kar ya sake dawowa" Khaleesat ta kalleta tace "In tafi ina?

Am not going anywhere Safiyyah, haka kawai in koma apartment dina ya bi ni can?" Safiyyah na huci tace "Kuma fa haka ne" Khaleesat ta dafe kanta da yayi mata nauyi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Safiyyah tace "Wannan fa kamar ya fi Abdul zama
an daba, ni wallahi ban san haka yake ba da ko hanyar da ya bi a makarantar nan ma bazan dinga bi ba, in ba dai in danna 911 yanxu su taho ba gaskiya" Khaleesat ta wani kalleta tace "Su taho su yi maki me?

Kar kiyi dialing ki bari sai na bar nan tukunna" Safiyyah ta koma ta zauna tayi tagumi, Khaleesat ta bude handbag dinta duk jiki a sanyaye ta ciro wayarta, ta fi second talatin ta kasa dialing number Ajay don ta tsani masifarsa ita kam, but did she have a choice?

Haka kawai ta koma Apartment dinta Aymaan ya bi ta ko kofar a kulle yake ya balle ya shigo mata ta shiga uku, ita sai yau ma ta kare masa kallo kana ganinsa kaga someone on drug shi yasa idonsa suka zama kamar me sexy eyes ashe tsabar shan kwaya ne, Safiyyah ta kalleta tace "Dole dai wancan mara mutuncin za ki kira, don ni wallahi bana son Ajayn nan gwara Housemate sau miliyan, ki ji fa ranan har da korata saboda kawai zai maki magana sai kace bai san yanda muke da ke ba, ya maida ni kamar wata bare ranan, abinda Housemate dinki bazai ta
a yi ba kenan yace in tashi wai zai maki magana, tun daga ranan na kullacesa a raina wallahi, ashe haka yake da ba
in hali ban sani ba, nace masa good afternoon wai ya amsa da evening tsabar rainin hankali, pls i don't like him" Khaleesat tace "To ina da wanda zan kira bayan shi ne?" Safiyyah tace "Yaushe Housemate din naki zai dawo ne?

Gaskiya we are missing him yayi maza ya dawo" Khaleesat tace "Oho" Daga haka tayi dialing number Ajay, sai da ya katse ta sake kira sannan ya daga, taji yace "What again Madam?" Hurriedly yayi tambayar as if in a haste to cut the call, ta sauke idonta a hankali tace "Zuwa yayi ya same mu a department ni da Safiyyah" Ajay yayi shiru, sai kuma yace "Sai aka yi yaya?" A sanyaye Khaleesat ta gaya masa abubuwan da ya zo ya fada da kuma yanda suka yi da Safiyyah daga karshe, Ajay dake ta sauraronta yace "Kin ga wannan kawar taki me shegen rawan kai sai ta ja maki bala'in da baki yi tunani ba a rayuwarki, who sent her to exchange words with him?

Duk ba ita ta kai ki inda kika hadu da gayen ba?

And meye kike son in maki da kika kirani yanxu?" Khaleesat ta katse wayarta ta ajiye, Safiyyah dake ta kallonta tace "What is he saying?" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, sai ga wayarta ya fara ring ta duba taga shi ke kiranta, Safiyyah ta ta
e baki tace "Allah sarki Housemate gaskiya yana kokari da wannan Ajay din ashe haka yake?

Wallahi yanda kika san Malamin islamiyya haka nake ganinsa ni dai yanxu, kullum a fusace yake, ki daga kar ya katse, ni yanxu na gaya ma Mustapha wannan magana ai zai gano na tafi Party bayan ce masa nayi baki da lafiya zan je apartment din ki daga schl ranan" Khaleesat tayi picking call din ta kai kunne taki cewa komai, yace "Kashe min waya kika yi?" Tace "To me zan yi idan ban kashe ba, kawai kayi ta ma mutum masifa kullum" Yace "Sai ki je kiyi sorting self din ki out" Daga haka ya katse wayarsa, Safiyyah tace "Tirrr, anya wannan zai iya zama da mace kuwa?

Ina ga a world din da ya tashi iya maza ne kawai suka yi surrounding dinsa, amma sam bashi da sympathy wa mace, kawai tashi zaki yi mu tafi gidan Yaya Mustapha don nima ban baki goyon bayan zuwa apartment din ki ba, Aymaan drugs din da yake sha basa gaya masa gaskiya" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, gaba daya taji zaman America din ma ya fita kanta har ma da karatun, shikenan ita daga wannan sai wannan a rayuwarta, hawaye taji ya cika idonta, Safiyyah tace "Ke kuma matsalata dake kenan, komai sai kice kuka kamar wata er yaye, Meye abun kuka kuma?
Chapter 139 · 0% Book details