← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 190 OF 218

Sashe 190

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Aunty dake zaune kan kujera ta dinga kallon hoton da Mami ta fiddo mata a wayarta, can ta kalli Mami baki bude tace "To ai na ta
a ganin yarinyar nan a Amurka da muka je kwanaki Fulani" Cikin tashin hankali Mami tace "Da gaske?" Aunty tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, wallahi a gidan nasu na Amurka take zaune sanda naje, don dakin da suke saukan ba
i a sama duk kayanta ne da akwatunan ta a ciki, har sai da na kira Mai martaba na kai masa kara" Mami tace "To ai a sanda ku ka je Jawwad na nan Nigeria Fulani" Aunty tace "Kwarai kuwa, daga ita sai Junaid da ma'aikata na tarar a gidan, Junaid ya min rashin kunya ya gaggaya min bakakken maganganu a kanta, daga karshe ya kuma dauketa ya bar gidan, Wato tunda watsattsiya ce kuma ba son ci gaban Jawwad din yake ba shine zai zugasa ya aureta, Shi idan ba mugu azzalumi ba me yasa bai ce zai aureta ba, don mugunta sai ya tusa ma Jawwad saboda shi ne dai dai er bariki, yo er bariki mana, in ba er bariki ba me take yi a cikin wannan gidan cikin maza har biyu sannan ga masu aiki?

Wallahi a yanda Jawwad ke tsoron Junaid idan ya hanasa auren yarinyar nan tsaf zai hanu, duk mun fa san Junaid ke controlling dinsa kinga kuwa tabbas da goyon bayan Junaid dari bisa dari akan maganar yarinyar" Mami ta dafe kanta da yayi mata nauyi don gaba daya ta ma kasa cewa komai, cikin tashin hankali tace "Ba fa er Nigeria bace Fulani, bamu ma san ko er wace kasa bace suka dawo Nigeria da zama" Aunty tace "Ni tafi min kama da Buzuwa, kuma akwai su da mallake miji kuwa da rabasa da danginsa, Wallahi in zaki fito ma Jawwad a mutum ki yi masa fata fata ki ajiye wannan kulafucin nasa da kike yi a rai to zai fi maki, don wannan kamata yayi ki ci masa mutunci sosai ba kadan ba ki nuna masa bacin ranki" Mami tace "Bazan masa haka ba Fulani, amma nasan me zan yi..." Aunty tace "To ga shawara, kuma shi kadai ne mafita a yanxu dai...." Mami ta daga kai tana kallonta tana jiran jin me zata ce.....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello* Ur evidence via 07087865788
https://chat.whatsapp.com/HVViEW83j9p1CPuLj0GcaA?mode=ac_t
HALYSAAH 89
Karfe goma da rabi still that morning Jay ya koma bangaren Mami, zaune ya sameta parlor tayi nisa tunanin da take, ta daga kai tana kallonsa, yace "Lafiya kuwa Mami?" Murmushi tayi tace "Ba komai Jawwad, kawai nazari nake ko in tafi Gomben da nace zan je yau ne ko kuma dai in bari gobe" Yace "Ai da sauran lokaci yau din Mami, karfe sha daya ma bai yi ba, in zaki je kawai kiyi tafiyarki yau din" Mami tace "To bari in shirya, shiru shiru baka dawo ka amshi wayar ka ba" Jay ya dau wayar sa dake gefen Mami, sannan ya zauna yana kallonta yace "Mami kiyi hakuri plss zan bi Ajay za mu tafi Abuja, amma kwana biyu kawai za mu yi mu dawo in sha Allah" Mami tayi shiru tana kallonsa, can tace "Yanxu za ku tafi Abujan kenan?" Jay yace "Eh, amma driving za mu yi zuwa Kano sai mu kwana a can, gobe mu bi flight zuwa Abujan" Mami tace "To ai shikenan, Allah Ubangiji ya kai ku lafiya, ya tsare hanya" Yace "Ameen" Mikewa yayi yace "Let me go and get ready" Tace "Ohk" Daga haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga parlon ya kullo mata kofa, ta rungume hannunta tace "Tabdi jam" Da yamma Jay ya gama shirin da yake ya fito daga daki yana kallon Ajay dake kwance kan 3 seater yace "Mu je..." Ajay ya daga kai ya kallesa yace "Mu je ina?" Jay ya hade rai yace "Plss ka dena rena min hankali mana" Ajay yace "Dole ne sai naje?

Kayi tafiyarka mana" Jay yace "In ka zauna kai kadai a gidan me zaka yi?" Ajay yace "Me nake yi yanxu?" Jay ya ja tsaki yace "Don Allah ka tashi mu je yamma na yi, in ma bazaka shiga gidan ba kayi zamanka a mota mana" Ajay yace "Wai dole ne sai naje gidan da ko shawara ba ayi da ni ba wajen siya?

Saboda kana ganin zan hanaka siya ko me?

But at least I should have know as a brother, ni bazan ta
a yin abu without ur knowledge Ba no matter what it is" Jay ya
an yi shiru, sai kuma yace "Ohk My bad...

Yanxu dai ko bazaka shiga ba ka tashi mu je, i don't want you to start running temperature again, kana ganin an bar ka kai
aya kake fara running temperature...." Ajay ya wani kallesa, sai kuma yace "Do I look sick to you now?

Ai na ji sauki" Jay ya kamo hannunsa zai dagosa daga saman kujeran with one hand, Ajay yayi wata dariya yace "That is a lie, Kai ka isa" Karfe biyar saura suka isa Tudun Yola, Jay yayi parking dai dai gate din gidan, Ajay dai kallon unguwan kawai yake don manyan gidaje ne kawai a unguwan, Jay ya kallesa yace "This is the House" Ajay ya kalli gate din gidan sannan yace "Allah ya sanya alkhairi" Jay yace "Ameen" After some seconds yace "Yanxu dai bazaka shiga ba?" Ajay yace "Ina jiran ka a nan" Jay yace "Ohk then, Amma kasan kuwa nayi ma Mami maganar Housemate?" Ajay ya kallesa yace "Ohk... ai baka gaya min ba" Jay yace "Yea, i don't want to stress you with talk duba da baka jin dadi" Ajay yace "Na fa ce maka ni naji sauki, You can see for ur self" Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Mami was so calm about it, and she wish me nothing but what's best for me, ta amince lokaci daya without prolonging the issue, dama kuma nasan bazata ta
in abinda na nuna ina so ba I told you that, tunda Mami da Mai martaba sun amince min, i don't care what others will think or say about this..." Ajay dai kallonsa kawai yake bai ce komai ba, can ya
an yi murmushi yace "I am happy to hear that, Allah ya sanya alkhairi" Jay na kallonsa yace "Ameen...." After some seconds yace "Or is there anything you want to tell me but you are not telling me?" Ajay yace "Kamar me kenan?

Why did you say so?" Jay yace "Naga kamar har yanxu kai baka yi na'am da batun nan dari bisa dari ba, You are just being neutral about it" Ajay yayi dariya yace "I don't get you Bruh, idan akwai wani abu ance maka bazan gaya maka bane?" Jay bai sake cewa komai ba ya bude motar ya sauka yace "Bazan dade ba in sha Allah" Ajay yace "Kana wuce minti goma i promise you I am leaving" Jay yace "Ai ba motar ka bace Malam" Bai jira cewarsa ba ya nufi cikin gidan, Ajay ya jinginar da kansa jikin kujeran motar maganganun Mami suna kara dawo masa a kai kamar a lokacin take gaya masa su, rufe ido yayi trying to erase the thought of his mind.
Chapter 190 · 0% Book details