← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 218

Sashe 57

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ajiye batun ubanki a gefe, ke abinda ya kashe maki yau ko kaf kasar da uwarki ta baro za a siyar za a iya biyansa aka ce maki?" Ita ma daya Co-wive din da suke kira Mama Zubaida tace "A'a rainin wayo mana Shatu, gwara ai a rena mana hankali, don uwarta kasuwa ne nan da zata cika mana gida da
uwa, wannan ai iskanci ne da walakanci" Khaleesat bata fasa kuka da ihun da take a dakin Ummanta ba tana surutai ita kanta bata san takamaiman abinda take cewa ba tsabar tashin hankali, Kanninta Noor da Islam kuwa har sun fara kuka su ma a dakin, kan kace me har makota sun fara tururuwan shigowa gidan, aka tsaya cirko cirko bakin kofar dakin Ummanta ana salallami, Mahaifinta ne Malam Ali ya shigo gidan yana zazzare ido, shi ma ya karaso da sauri yana tambayar abinda ke faruwa a gidan, Mama Shatu ta tabe baki tace "Wai er da ta fi kowa ce ta sauka yau daga Amurka shine uwar ke sanar mata ai an daura aurensu da shi wanda ya kai ta waje karatu har ta dena ganin kowa da gashi, shine fa ta cika anguwa da ihu da koke koke wai ita bata son auren bazata zauna da shi ba, ga jama'a na ta shigowa an zata gobara muke, wannan ai tsabar sangarci da iya shege ne" Juyawa Malam Ali yayi ya nufi gun da ake ajiye itacen girki da sauri ya suri daya ya dawo ya nufo dakin Umma yana cewa "Ina take..." Matan makota dake tsakar gidan suka hau basa hakuri suna don Allah ya kyaleta, yaki sauraron kowa yana zazzare ido, Khaleesat na hangosa ta tafi bayan Ummanta da gudu tana kuka ta rungumeta, kanninta ma suka yi bayan Umma gaba daya suna kuka, Mama Salame ta tsaya tayi bake bake gabansa tace "Haba haba, haba Malam Ali, meye haka kake kokarin yi?" Yace "Salame ki bar ni dai inci malfar ubanta a wajen, mu zata tona ma asiri?

Ni zata ja ma sabon bala'i da fitinan da ya girmeni?" Mama Salame tace "A'a wallahi baza ka doketa da wannan rafkeken icen ba ita ba jaka ba, mu je waje Malam Ali" Ita dai Umma kanta na kasa bata ce komai ba, haka Mama Salame ta samu ta tasa keyarsa ya fita daga dakin tana biye da shi, Mama Zubaida ta rike ha
a tace "Ikon Allah, mu muke ganin kinibibi iri iri a gidan nan, to in aka bibiya wani ta kyallara ido ta gani a Amurkan shine zata tona ma uban asirinsa da ke rufe, da can menene yasa ta hakura zata aurensa?

Sai ranan da aka daura aure ta nemi tara mana mutan anguwa tace bata san zance ba?

Yau ni nake ganin iskanci, to ta tsotsi nonon buzuwa ba dole ta iya makirci da kissa ba" Ita dai Khaleesat kuka kawai take a jikin Ummanta siblings dinta na kusa da ita suna taya ta, Mama Salame ta sake labulen dakin Umma duk don matan dake tsaye bakin kofar su kama gabansu, Umma ta juya tana kallon Khaleesat gaba daya ta kasa cewa komai, zamewa kasa Khaleesat tayi ta hade kanta da gwiwa tana kuka kamar ranta zai fita tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" a sanyaye Umma ta tafi gefen katifar dakin ta zauna ta kasa cewa komai.

Karfe biyun dare Umma na zaune kan darduma da carbi a hannunta, Khaleesat ta tsallake kanninta ta fito daga cikin net din da take kwance bayan ta tuna ko isha'i bata yi ba, tunda Mama Salame ta daura mata net tace ta shiga ta kwanta wajen karfe sha daya take kwance duk da ba bacci take ba, don ko bacci barawo bata gani ba, amma tayi shiru cikin net din tunani iri iri na yawo a kanta, gaba daya ta ji kamar hawayenta ma ya kafe, har a lkcn babu maganar da ya hadata da Ummanta, tana jin jiri da zazzabi ta nufi kofa zata fita ta dauro alwala, Umma dai ta bi ta da kallo, bayan ta dauro alwalan ta dawo ta saka hijab dinta ta tada sallah, bayan ta idar tayi nafila raka'a biyu, tana zaune kan darduman ta jingina da bango tayi nisa tunanin da take, gani take kamar a mafarki ake sanar mata an daura mata aure da Abdul amma ta ki farkawa daga mummunan baccin nan har yanzu, muryar Ummanta yaji ta kirata a hankali, Khaleesat ta juya ta kalleta amma ta kasa amsawa, Umma ta mike ta koma kusa da ita ta zauna tana kallonta, cikin sanyin murya tace "Me ya faru kuma tsakaninki da Abdul din Khaleesat?

Wani abun ya kara maki?

Me yasa kika ce baki son auren?" Khaleesat ta fashe da kuka a hankali tace "Umma wallahi bana son sa, bazan iya zama da shi ba, in aka ce za a kai ni gidansa zan iya mutuwa wallahi, don Allah Umma ku taimakeni ku yi min rai" Umma ta kasa ce mata komai hawaye ya cika idonta ta fara gogewa da hijab dinta, Khaleesat ta daura kanta kan kafadar Ummanta tana kuka me tsuma zuciya tace "Don Allah ku taimakeni Umma, bazan iya ba wallahi" Umma ta rungumeta tana patting bayanta ita ma hawayen na sauka idonta amma bata iya ta ce mata komai ba, they sat there for almost 40 mins, jin tana sauke numfashi a hankali Umma ta gane bacci tayi, a haka Umma ta zauna wajen Khaleesat na jikinta don bata son tashinta har kusan lokacin sallahn asuba.

Da safe wajen karfe tara Umma ta shigo dakinta rike da cup din kunu da kosai a roba, ta karasa kusa da Khaleesat dake kwance gefen katifarta ta ajiye mata sannan ta zauna cikin kwantar da murya tace "Ta so ki ci ko kadan ne Khaleesat" Khaleesat dai kallon cup din kunun kawai take, lkci daya hawaye ya cika idonta, Umma dai ta sunkuyar da kai, Islam ce ta shigo dakin rike da paracetamol da Umma ta aiketa ta siyo ma yayar tata, ta zauna kusa da Umma tace "Umma ga maganin na siyo ma Aunty" Umma ta amsa ta ajiye a gefenta tace "Tashi ki je ki karasa min aikin da na sa ki" Islam dake kallon Khaleesat ta mike a hankali ta fita daga dakin, Umma ta maida dubanta kan Khaleesat tace "So kike ki sa ma kanki wani ciwon ne Khaleesat nima ki sa min damuwa?

Ki tashi ko kunun ne ki sha" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin rawan murya tace "Ni bazan iya sha ba Umma" a sanyaye Umma tace "Toh ya kike son in maki Khaleesat?" Umma ta kasa ci gaba hawaye ya fara sauka idonta ta dafe kanta, kuka kawai Khaleesat take tana kallon Ummanta, Umma ta dake tana share idonta tace "Ko wajen Nenne zaki sai ki gaya mata ki ji abinda zata ce, ni kin san babu abinda zan iya yi akan lamarin nan Khaleesat" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Umma ta mike a sanyaye ta fita daga dakin don juye mata ruwan wankan da ta dora mata a kan wuta yana ta tafasa, a haka ta ta dawo ta samu ta lallabata ta
an sha kunun sannan ta tafi waje yin wanka, kafin ta fito har Umma ta fiddo mata kayan da zata sa tayi tagumi tana jiranta, karfin hali kawai Khaleesat take amma ji take kamar zata iya collapse at anytime, bayan ta shirya Umma tace "Amma
bana son yan gidan nan su san inda zaki, kar su gaya ma Malam" Khaleesat ta jinginar da kanta da bango, a hankali tace "Umma bazan iya zuwa ni kadai ba don Allah ki rakani" Umma tayi shiru, can tace "To zan fita in shiga gidansu Er Lami in jira ki a can, bana son su ga mun fita tare, bayan na fita da minti goma kema sai ki fito" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Umma ta mike ta dau hijab dinta ta saka sannan ta dora nikab ta fita daga dakin, Su Mama Shatu da Mama Zubaida suna ta girka abincin siyarwansu da yaransu za su fita talla da shi, tace masu zata shiga makota sannan ta fita, duk suka bi ta da kallo sun tabe baki, Mama Shatu tace "Ma ji ma gani dai, a sanda ake mana fafa an tura 'ya kasar waje ga namu yaran a zube ai babu bakin cikin da ba a kuntsa mana ba" Mama Zubaida tace "Sun gana tattatse
an mutane rana daya su fito su ce basu san zance ba, ke ina kika ta
a ganin anyi haka?

Ai na so Malam ya rarrade shegiya jiya da daddare, to dai ba kanta kadai zata ja ma babban magana ba, har shi Malam din" Duk Khaleesat na jin su, ita dai tana zaune ta jinginar da kanta da bango tana sauke numfashi a hankali, bayan minti goma da fitar Ummanta ta tashi da kyar ta fiddo gogaggen Hijab dinta ta saka sannan ta dora Nikab ta fita daga dakin, tunda ta fito suke kallonta, a haka ta nufi hanyar fita daga tsakar gidan tana ji kamar iska zai kadata ta fadi.

Gidan da Ummanta tace zata jirata ta nufa, ta samu Ummanta a tsakar gida tana jiranta yan gidan ma duk basa nan, Umma ta taso suka fita daga gidan, tafiyar kusan minti sha biyar ne zuwa gidan Nenne daga gidansu, Nenne ta ajiye tsintsiyar hannunta tace "Dawowa yayi da ita daga inda take karatun don an daura aure?" Umma ta zauna kan tabarman tsakar gidan ta cire Nikab din fuskarta ta gaida Nenne, Khaleesat ta zauna gefen Ummanta, Nenne ta amsa tace "Ai dama nace ko da ta dawo sai ta huta an kintsa ta kafin ayi maganar wata tarewa tunda yace baya bukatar taron komai, amma baza mu dau yarinya haka kawai ace an je kai ta ba" Umma dai tayi shiru bata ce komai ba, a hankali Khaleesat ta cire Nikab din fuskarta ta ajiye, Nenne ta
an duka tana kallonta tace "Lapiya naga idanuwanta sun kumbura haka, me ke faruwa?" Umma ta sauke ajiyar zuciya ta kasa cewa komai, A fusace Nenne tace "Magana nake ku ka min shiru fa?
Chapter 57 · 0% Book details