← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 218

Sashe 114

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shi fa Abdul duk abinda yayi yana da manufar yin hakan duk mun sani, ba haka kawai ya dauketa ya kai ta karatu ba...." Umma ta dakatar da ita tace "Ban ce shi wannan bawan Allahn yana da wata manufa ba amma dai kam Khaleesat bazata koma Amurka ba Farida" Aunty Farida bata sake tanka Umma ba ta fitar da albasan da ta siyo zata je ta shanya a bakin kofa, Safiyyah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya a hankali tace "Toh shikenan Umma, ni zan koma gida, dama abinda ya kawo ni kenan" Umma tace "To ki gaida mutanen gidan Safiyyah mun gode kwarai, shi ma ki yi masa godiya don Allah" Safiyyah tace "To Umma" Jiki a sanyaye ta mike ta fita daga dakin, Aunty Farida ta dau hijab dinta da ta rataye a igiya tayi ma Safiyyah alamar su je waje, ita dai Khaleesat na zaune inda take bata tashi ba don duk taji conversation din Safiyyah da Ummanta, Aunty Farida na fita kofar gida da Safiyyah tace "Safiyyah kar ki yarda ki gaya masa abinda Umma ta ce, ki bari Babanta in ya dawo anjima zan samesa in yi masa magana" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya tace "To Aunty, don Allah ki yi convincing dinsa shi ma, It will be very sad idan aka ce bata karasa karatun nan ba, shekara daya fa kawai ya rage mana" Aunty Farida tace "In sha Allah zan yi bakin kokarina, kuma Khaleesat zata ci gaba da karatun ta" Safiyyah tace "To Aunty, gobe da safe zan kira ki sai inji yanda ku ka yi da Baba" Aunty Farida tace "To babu damuwa, ki gaida gida" a haka suka rabu Aunty Farida ta juya ta koma cikin gida...

Khaleesat ta gama girkin da take bayan ta kashe gawayin tayi alwala ta shiga dakin Ummanta, tana idar da sallah ta kwanta, gaba daya taji damuwarta ya dawo sabo fil maganar Housemate dinta da Safiyyah ta kawo mata, Umma na kallonta tace "Baza ki ci abincin bane yanxu?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Sai anjima" Ita dai Aunty Farida linke kayan su Islam take don tun bayan tafiyar Safiyyah bata ce ma Umma komai kan maganar da Safiyyah ta kawo ba sanin Umma bazata ta
a fahimta ba.

Bayan Magrib Aunty Farida ta samu Malam Ali yana zaune kofar dakinsa, bayan sun gaisa yace "Amma ba Lagos kika zo gaya min zaki koma ba Farida?" Murmushi kawai Aunty Farida tayi don in akwai abinda ya tsana zamanta Lagos yayi fadan har ya gaji, ta kauda tambayar da yake mata tace "Magana na zo mu yi kan Khaleesat" Yayi shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace "To ina sauraron ki" Cikin nutsuwa Aunty Farida ta sanar masa batun da Safiyyah ta zo da shi daxu da rana, Malam Ali ya girgiza kai yace "Ashe ban daddara ba kenan Farida, na yi tunanin duk mun dau darasi kan abinda ya faru wanda duk nafi kowa laifi a ciki...." Aunty Farida ta kwantar da murya tace "Ae wancan issue din da wannan ba daya bane Malam, shi fa Abdul da isa da gadara ya turata karatu Amurka kuma babu yanda muka iya haka duk muka sallama masa domin zaman lafiyanmu da naka, Abdul da manufarsa na tura ta karatu, shi ko wannan bawan Allahn babu wata manufa a ransa, saboda Allah zai biya mata ta karasa karatun kar tayi asaran shekarun da tayi, iya shekara daya fa ya rage mata Malam, ka san muhimmancin karatun nan balle ka kushe komawarta America ta karasa, in kowa zai kalubalanci haka ai banda kai Malam, don Allah ka duba wannan lamari, kuma shi wannan bawan Allahn da ya ce zai dau nauyin shekara dayan da ya rage mata su ne fa suka dau maka lauya har aka wanke ka a kotu aka kashe maganar bashin ka da Baban Abdul...." Malam Ali yayi murmushi yace "Ai nayi appreciating hakan da suka min kuma kullum ina saka su a addu'ata, amma babu zanc
en komawar Jiddah America karatu Farida, kiyi hakuri a bar batun nan gaba dayanta, we shouldn't be a bad parent for the second time saboda son abun duniya, tayi hakuri in Allah ya hore min sai in biya mata tayi Jamb ta nemi ko BUK ko Northwest, duka duka shekarunta nawa suke?

Ai lokaci bai kure mata na karatu ba Farida, kuma ko aro ne zan nema in biya mata in sha Allah, don haka bana son a sake tada zancen ci gaba da karatun ta a America" Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, after a while tace "To shikenan, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi" Yace "Ameen" Mikewa tayi ta bar wajen rai babu dadi.

Washegari wajen karfe tara Aunty Farida ta gama shirin da take, Umma dake kallonta tace "Ina za ki ne?" Aunty Farida na dora Nikab dinta kan Hijabin jikinta tace "Ba nace maki zan je gidan Abida ba shekaranjiya" Umma tace "Shi ne zaki mata sammako?" Aunty Farida tace "Jiya tace min bata da lafiya ne, kuma ina son in dawo da wuri in wanke kai na" Umma ta tabe baki tace "To sai kin dawo" Ita dai Khaleesat juya kokon gabanta take a hankali tana sha ga dumamen tuwo shi ma a gabanta, da kyar take shan kokon, dumamen kuwa ta kasa ci, dama jiya da daddare ma bata wani ci tuwon ba, Aunty Farida tayi ma Umma sallama ta fita daga dakin.

Nenne na gyara daurin dankwalinta tayi kasa da murya tace "To ke banda abun ki ai Zahra'u Jahila ce Parida, matar da har yau bata da wayewa kanta a murfi yake kamar matar kauye, ita ta wani san maki muhimmancin karatu kina ganin mata haka kara zube, gashi sai yanda kazaman kishiyoyi suka yi da ita sun mayar da ita Bora?

Ai bari ki ji Parida, Zahra'u a yanxu dai ita daga tuwo sai bautan Allah kawai ta saka a gaba, babu ruwanta da wani ci gaba na duniya ko kyale kyalin duniya, ta riga ta amince ta kare rayuwar ta a haka in dai zata ci tuwo tayi bautar Allah, shi yasa kullum zaki ganta rike da carbi a kuturin dakinta da ko Ceiling din arziki babu, ni bana ma jin Zahra'u na yi ma Ali addu'an Allah ya dawo masa da arzikinsa don in tayi hakan gani zata yi kamar ta butulce ma Allah, duk tunaninta fa haka Allah ya so ganinsu cikin ba
in talauci, gani zata yi in tayi ta ma Allah magiyan ya yaye masu talauci kamar butulci tayi bata gode da ni'imarsa ba tunda tana samun tuwo ta ci, to irin tunanin yayarki kenan Parida, in ba haka ba ta yaya zaki dinga yi ma er cikinki bakin cikin karasa karatu ta taimake ku a rayuwa ta cire ku daga kangin talauci? shikenan kuma don kai jahili ne sai ka rasa sanin abinda ya kamata?

Har wani kwambo fa take da jahilcin ta da rashin wayewa, ki bar ni da su kawai zan yi maganinsu daga Alin har Zahra'un, da can uban me yasa suka bari aka kai ta Amurkan in har da tsoron Allah a lamarinsu daga ita har Alin?

Wato sai yanxu suka zama iyayen kirki masu tsoron Allah ko?
Chapter 114 · 0% Book details