← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 210 OF 218

Sashe 210

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashe ina ma son sa da alkhairi in har na bari aka yi haka, ai sai dai in sa a aura masa warce zata zamo ajalinsa in ma na bari yayi auren kenan...." Shiru Mai martaba yayi yana kallon Jawwad bayan ya gama sauraronsa, after a while ya sauke ajiyar zuciya yace "Fulani ce tayi maka wannan tsarin ko?" Jay ya sauke idonsa yayi shiru don bayan sun gama magana da Mami few hours ago sai da ta jaddada masa kar ma yace ma Mai martaba yayi magana da ita, Mai martaba yace "Nasan duk tsarinta ne wannan, so kana nufin yanxu in sake turawa a sanar masu na canza maganar da nayi shekaranjiya kenan?" A hankali Jay yace "Ai ba sai an tura ba ranka shi dade, ta waya ma idan aka sanar masu ina ga ya wadatar" Mai martaba dai yayi shiru yana kallonsa, bayan wasu mintoci yace "Baza a
aga daurin auren nan ba Jawwad, ranan Juma'ah kamar yanda na tsara za a daura auren, nothing is going to change that" Jay ya daga kai yana kallonsa a sanyaye bai iya yace komai ba....

Ko da ya koma bangaren Mami ya sanar mata yanda suka yi da Mai martaba kuka ta sakar masa tace "Ni kuma in dai ba nan da sati hudun da muka shirya da kai ba wallahi Ahmad kayi aure ne ba da yawu na ba, ba kuma da amincewata ba, kuma bazan ta
a saka maka albarka a wannan aure ba" Sosai jikin Jay yayi sanyi yace "Don Allah Mami ki yi hakuri, ni nasan yanda zan yi convincing Mai martaba zuwa lokacin da kika ce kina son ayi auren" Cikin kuka Mami tace "Da dai yafi maka, duk da bana son auren nan haka na kai zuciya nesa na amince amma nace ga yanda nake son ayi min a matsayina na mahaifiyarka nan ma sai a tauye ni a nuna ban isa ba?" A hankali Jay yace "Kiyi hakuri, yanda kike so in sha Allah haka za ayi" Ba karamin Courage Jay yayi gathering ba ya sake komawa gun Mai martaba bayan Magrib, ya risina kai cikin ladabi yace "Ka gafarce ni ranka shi dade, i don't mean to disobey or disagree with you in any way, amma kayi hakuri ranka shi dade ka
aga wannan aure zuwa nan da wata daya kafin nan nayi shirye shiryen da zan yi a tsanake" Mai martaba ya
an yi murmushi ya jinjina kai bai dai ce masa komai ba, shigowar Aunty Parlon yasa Mai martaba yace "Zaka iya tafiya Ahmad, I've heard you" Jawwad ya mike yayi ma Aunty barka da yamma sannan ya fita daga parlon.

Wajen karfe tara Ajay ya shiga Bedroom din Jay yana kallonsa yace "Don me zaka samu Mai martaba kace a
aga auren?" Jay yace "I have no Choice Ajay, haka Mami tace take so" Ajay yace "Must you listen to everything?" Calmly Jay yace "C'mon Ajay, she is my mother, ta yaya zan yi aure babu blessings dinta?

Yanxu ba cewa tayi bata son auren kwata kwata ba kamar yanda tace few days ago, kawai so take sai na fara auren Hadiyah da 4 weeks sannan in auri Halysaah, idan ina son ganin dai dai ai abinda tace take so shi zan yi" Ajay ya girgiza kai yace "Ina me tabbatar maka wannan wani plan ne nasu suka hada ita da Aunty cause ita ke zugata...." Jay yace "What ever, ni dai nasan wata dayan da tace bazai cika ba ta canza min magana, shi yasa ban damu ba" Ajay ya sauke ajiyar zuciya yace "Abba isn't happy with this, he wasn't expecting this from you, considering the fact that he supported you from the onset..." Jay yace "I have no choice kamar yanda nace maka Ajay, Mami ce ta sa inyi haka and I did that for peace to reign" Ajay ya
an yi murmushi yace "At the end ina ga fa sai dai tayi hakuri ta saka albarkan nan da tace bazata saka ba daga baya cause I am assuring you come Friday sai Abba yayi abinda ya tsara, saboda wani reason mara ma'ana bazai canza maganarsa ba a maida shi karamin mutum, come Friday you will be groom to 2 bride...." Jay na kallonsa da damuwa yace "Haka Abba yace maka?" Ajay ya
aga kafada bai ce komai ba ya juya ya fita daga dakin, Jay ya rasa ma me zai yi ko kadan bai son bacin ran Maminsa gashi har da kuka tayi saboda shi, nazarin maganganun da zai sake samun Mai martaba da shi ya fara yi, ya fi minti ashirin pondering on what to say to the king for the third time, daga karshe ya mike ya fita with the hope that wannan karan Sarki zai janye batun auren zuwa nan da wata daya.

Karfe goma saura Jay ya tafi bangaren Ajay, a parlor ya samesa yana kallon kwallo, Jay ya sauke ajiyar zuciya ya zauna yana kallonsa yace "Daga wajen Mai martaba nake" Ajay ya
an kallesa, sai kuma yace "Ya ku ka yi da shi?" Jay yace "I am just hoping he consider all what I said"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
07087865788
HALYSAAH 98
Washegari da safe Jay ya tafi bangaren Maminsa don gaisheta, bayan ta amsa gaisuwarsa tana kallonsa tace "Ya ku ka yi da Sarki?" Jay ya sauke idonsa yace "Mami sau uku ina yi masa magana...." Mami tace "Ba sau nawa kayi masa magana nake tambayarka ba Jawwad, cewa nayi ya ya ku ka yi da shi daga karshe?" A hankali Jay yace "Kinsan bazai yi magana me tsayi ba Mami, he was quiet at the end kuma yace min ya ji, i am just hoping he is convinced kuma zai yi considering duk abun da na gaya masa, don haka ko da zaki ga wani abu daban Mami ki sani i tried my best in maki yanda kike so, duk yanda nake jin nauyin Mai martaba i confronted him thrice just to please you Mami" Sallaman Aunty yasa Jay yayi shiru ya daga kai yana kallonta, Aunty ta karaso cikin parlon tace "Fatan mun wayi gari lafiya Fulani" Mami tace "Lafiya lau Alhamdulillah, ya kwanan su Zuwaira?" Aunty ta nemi kujera ta zauna tace "Alhamdulillah" Jay ya sauke idonsa ya gaida Aunty ta amsa sannan ya mike yana kallon Mami yace "Zan
an fita Mami, sai na dawo" Aunty tace "Zaka
an fita ko dai za ku fita, Boss din naka na can naga ai ya shirya yana jiran ka kaje ka ja maku mota" Ko kallonta Jay bai yi ba har ya fita daga parlon, Aunty ta ta
e baki tana kallon Mami tace "Tare fa za su fita da Junaid don naga Junaid din ya fito yana rike da makullin mota" Mami dai bata ce komai ba don abinda ya dameta daban a ranta, ba kadan maganar auren nan ya tsaya mata a rai ba, Aunty ta gyara zama tace "To yanxu yaya ake ciki?

Mai martaban ya yarda a
aga daurin auren ko kuwa?" Mami ta girgiza kai tace "Ina tantama Fulani, don sau uku Jawwad din ke samunsa da maganar amma yaki ce masa komai, kin ga kuwa bai amince ba kenan" Aunty tace "Sai kace ba Sarki ba, ai ni nasan ko don ya nuna mana iyakar mu fa sai yayi abin nan da yaga ba ma so, ga abu ya zo a kurarren lokaci balle a bi ta kasa a lalata, amma dai kin san abinda zai faru?" Mami na kallonta tace "A'a sai kin fada" Aunty ta mike ta koma gefenta ta zauna tana kallonta....

Ko kallon Jay Ajay bai yarda yayi ba ya nufi motarsa, Jay ya bi sa da kallo yace "Ni zaka walakanta?" Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace "Since when did I become ur driver Jay, if you are not too fine to drive ga drebobi sai wanda ka zaba a gidan nan, why do I have to drive you, on a serious note bazan je unguwan nan me nisa ba da daddaren nan, gwara ma ace hanyar Kano na kama in san tafiya me nisa dama zan yi kawai, haba ai unguwan yayi nisa sosai ga hanyar babu kyau ga dare yayi, throughout the day time me yasa baka ce in raka ka ba sai da daddaren nan, beside i told you i am meeting a friend yana jirana, you met me already prepared to go out balle kace kirkiro fitan nayi" Jay dai kallonsa kawai yake, Ajay yace "Zaka je wajen budurwar ka sai kace sai an raka ka, idan nace bazan je ba kuma ya zama issue, kaje for once kai kadai mana, haba you are stressing me wallahi" Kallonsa kawai Jay yake yaki tanka sa, Jin Jay yaki cewa komai kuma bai fasa kallonsa ba yace "To in har zan je sai ka min full tank, sannan akwai shopping da zan yi online the bill is on you, agreed?" Jay ya wani kallesa, haka nan babu yanda Ajay ya iya suka bar gidan a cikin motarsa yana mita, Jay dai ko kallonsa bai yi ba, karfe tara saura mintuna Ajay yayi parking dai dai kofar gidansu Aunty Murja, Jay ya ciro wayarsa after some seconds ya kai kunne duk da ba kira yake ba don yasan ko ya kirata ba lallai ta
aga ba, he tried calling her once yesterday bata yi picking ba kuma bata biyo sa ba, can ya kalli Ajay yace "Can you pls call Halysaah's line, I can't reach her" Ajay ya juya ya kallesa, sai kuma yace "You can't reach her?
Chapter 210 · 0% Book details