← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 218

Sashe 48

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Are you okay?" Ta wani murguda baki tace "Toh ba ina hanya bane wai, haka kawai dai babu dalili bazan kama hanya in fito cikin sanyin nan ba yaya, ko ka manta jibi za mu fara exams ne?" Kashe wayarsa yayi, Safiyyah tace "Allah dai ya tsine ma Surayya albarka, kuma wallahi kafin mu gama exam mu bar kasar nan sai na mata abinda bazata ta
a mantawa ba a rayuwarta, ko da wasa kuma bazan ma gaya masa abinda ya faru dake ba kar yayi burgan cewa ki dawo gidansa ya kara ma matarsa extra nama" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah ta mike ta dau jakarta da gyale tace "Sai na zo gobe in sha Allahu, saura kar ki karasa cinye abincin ki zauna kina asaran hawayenki akan
an daba, ga lambata na sa maki a waya in da wani abu ko kuma kina bukatar komai kawai ki kirani" Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat ta sauke idonta kasa, Downstairs Safiyyah ta hadu da AJ wanda shigowarsa gidan kenan tana
an murmushi ta gaishesa ya tsaya ya amsa yana danna wayarsa yace "How are you doing" Tace "Alhmdlh ya karatu" Yace "Fine, ya naki" Tace "Muna ta fafatawa dai, to fa mun gode da hidima yaya, Allah ya saka da alkhairi da abinda ku ka ma kawata, Allah ya biya ku" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta jin wai tana masa godiya, ita dai ta ci gaba da godiyar ta ba kakkautawa, Yace "Ameen" Tace "Yaya Housemate din ya fita ne, ni zan koma gida ne yanxu" Sai ga Jay ya shigo parlon from outside, ganinta yace "Ohk zaki koma Safiyyah?" Tace "Eh wallahi yamma tayi amma in sha Allahu zan shigo gobe da safe" Yace "To Allah ya kai mu, mu je inyi dropping dinki" Tuni AJ yayi wucewarsa sama, Safiyyah ta bi bayan Jay suka fita daga parlon tana mamakin inda karen gidan yake bata gansa ba tun daxu, sai bayan da suka dau hanya tace "Yaya Housemate...." Dariya ta ba Jay bai jira me zata ce ba yace "I am Jawwad Safiyyah" Tace "To ni dai don Allah kayi dubara ka amshe wayar da ka ba Khaleesat kar taje ta kira yan gidansu su gigita ta, kaga bamu san ko Abdul din na kasar nan ba ko ya koma Nigeria, in ta kira suka gaya mata wani maganar da kyar ta iya abun arziki a jarabawan nan" Jay yayi shiru cause he reason with what Safiyyah is saying, can yace "Haka ne kuma, i will tell her not to speak to anyone for now, amma bazan iya amsan wayar ba naga kamar it's whiling away her time" Safiyyah tace "To in da kati a wayar don Allah ka kone sa, in da WhatsApp kayi uninstalling dinsa kaga ta haka babu wanda zata ma magana, the exams is just for a few weeks, kamar gobe ne za mu gama" Yace "Sure i will do so Safiyyah" A haka suka isa gidansu ta sauka daga motar ta masa godiya yace "Ki gaida mutanen gidan" Tace "To za su ji" Yayi reverse ya dau hanyar gida hoping Khaleesat bata riga ta ma kowa magana back in Nigeria ba.

Washegari da safe Jay yayi booking appointment na ganin likita saboda daren ranan ma Khaleesat dai bata yi bacci ba, yasan dai ba lallai su samu ganin likitan a ranan ba, so he was just helping her to manage her self with the drugs available, da Safiyyah kuma ta zo sai taji ta nemi zazzabin ta rasa dama kadaici ne da damuwa suka mata yawa.

Ranan monday da safe Jay yayi dropping din Khaleesat school for her first exam, and he stayed behind har zuwa sanda za su gama don su koma gida tare, kawai shi dai baya son barin ta ita kadai, Jay is trying his very best na ganin Khaleesat ta sake ranta domin tayi karatun jarabawanta da kyau kar ta samu matsala, ga kuma Safiyyah dake encouraging dinta a gefe ita ma, kuma hakan yayi tasiri sosai don ta
an sake ranta tana karatun, AJ dai tun ranan da ya shigo ya ganta zaune a daki har bayan da suka yi Exams uku bata sake saka shi a ido ba, bata san ko yana gidan ba ma ko baya gidan, ita dai 24/7 tana daki, hatta abinci cook din gidan ne ke kai mata sama yayi knocking ta fito ta amsa, in ta gama still shi yake zuwa ya amshi tray din, bayan sati biyu da fara exam dinsu ranan suna da interval Safiyyah ta zo gidan da yamma, abinci ta kawo ma Khaleesat, Khaleesat taji dadi sosai ganin tuwo ne don dama tun jiya take sha'awan tuwon, Safiyyah tace "Kinga ba dadewa zan yi ba yanzu zan tafi kafin mutumin can ya fara kirana kamar Surayya ce ta bar gida" A hankali Khaleesat tace "Baza ki bari anjima kadan ba pls" Safiyyah tace "Wallahi yanzu Ya Mustapha zai fara kirana, bai ma san na fito ba, kuma nayi order din Lyft ma da zai maidani gashi nan ya kusa karasowa nan, tashi ki rakani kofar gida" Khaleesat ta girgiza kai tace "Kawai ki tafi za mu hadu schl tomorrow in sha Allah" Safiyyah tace "Wai ke baki gajiya da zama ke kadai a daki, don Allah ni dai tashi ki rakani kema ki
an yi strolling kafafuwanki" a hankali Khaleesat tace "Baza ki gane ba Sophie, wallahi i am not comfortable staying in this house, na kagu mu gama jarabawan nan in koma Nigeria" Safiyyah tace "Ae ranan Housemate dinki ya gaya min wai kince masa zaki koma apartment dinki nace lallai baki da hankali, Allah ma yasa Abdul bai sake gidan ba" Tana dariya ta kare maganar, sai kuma ta kwantar da murya tace "Kiyi hakuri kawata, nan da sati kadan zaki ga mun gama exams din in sha Allah, ki kwantar da hankalinki pls, yanzu dai tashi ki rakani" a hankali Khaleesat ta sauko daga kan gadon ta dau gyalenta suka fita dakin tare da Safiyyah, suna saukowa downstairs suka tarar da AJ a parlor da Jay, Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta don sai yau taga AJ for almost 2 weeks, ita ta zata ma baya gidan ne, Jay na kallon Safiyyah yace "Are you going soon Safiyyah?" Safiyyah tace "Eh wallahi Yaya Jawwad Lyft dina yana hanya ya kusa" Yace "Alright, ki gaida mutanen gidan" Tace "In sha Allah za su ji" Sallama tayi ma AJ ya amsa mata, sannan ta kama hannun Khaleesat suka fita daga parlon, suna tsaye waje suna jiran karasowar Lyft wata mota ta shiga gidan bayan matukin motar ya fito daga cikin motar ya bude gate, Safiyyah tayi kasa da murya bayan sun shiga ciki tace "Ke kinga wani Ride me suna ride Khaleesat?

Su dai da masu kudi kawai suke harkar su a kasar nan, in kin bibiya abokansu ne 'ya yan masu kudi irinsu" Khaleesat dai bata ce komai ba, bayan kusan minti uku sai ga Lyft din Safiyyah ya iso, Safiyyah ta bude bayan motar ta shiga, Khaleesat ta daga mata hannu, Safiyyah na mata murmushi tace "Sai mun hadu a schl kawata, kiyi karatu da kyau fa" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata sannan ta koma cikin gidan, duk a dar dar take tafiya a babban compound din gidan, har yau ita dai ta kasa sakin jiki a gidan nan gani take kamar a kaya ma take she is so very uncomfortable, a haka ta isa parlon gidan ganin baki biyu dake parlon tare da su Jay wanda da alama abokansu ne Khaleesat ta sauke kai ta gaishesu, suka amsa da fara'a, ita dai ta nufi stairs, daya daga frnds din nasu taji yace "Bakuwa ku ka yi a gidan" AJ dake shan fruit salad yace "Eh, yarinyar wani abokinmu ne a Nigeria ta zo jarabawa" Jay ya saki baki yana kallon AJ da ke ta shan fruit salad dinsa ko ajikinsa, Ita kanta Khaleesat sai da ta
an juya ta kallesa sannan ta wuce sama, abokin na gyara zama yace "Waow, amma da gani da wuri abokin nan naku yayi aure, ya huta abunsa gashi mu duk mun kasa har yanzu" AJ dai ya ci gaba da shan fruit salad dinsa yace "Ai kam ya huta, mu ma da munyi auren da wuri duk da mun haifi kamarta ai"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
HALYSAAH 24
Parlon dake sama Jay ya ja AJ zuwa can yace "Ohk now, let me explain Bruh" AJ na girgiza kai yace "I am not interested pls Jay, ni fa bana son ma kana min magana a gidan nan kar ayi zaton tare mu ka kawota" Jay yace "Naji.... bayan yanzu bazan sake maka magana ba, kawai dai na duba naga duk gidan nan dakin ka ne kadai yake da wahalan shiga..." Nan da nan AJ ya hade girar sama da ta kasa yana kallonsa yace "I don't understand, me yasa kake using dakina kake misali?

What are you insinuating?
Chapter 48 · 0% Book details