← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 218

Sashe 126

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai kusan karfe uku na rana Khaleesat ta tashi daga bacci, bayan tayi wanka tayi sallan azahar ta sauka parlor don yunwa take ji sosai, kunna heater din parlon tayi don parlon yayi sanyi kamar fridge, ta karasa ta tsaya jikin window din parlon ta daga labule tana kallon beautiful Neighborhood din ta, ko ina fari tas saboda snow din da aka yi sosai daren jiya da bai gama narkewa ba, after some minutes ta sake drape din windan a hankali ta nufi kitchen, shayi ta hada ta debi cookies ta dawo parlorn ta zauna, bayan ta gama ta kai plate din da cup kitchen ta wanke sannan ta koma sama don harhada textbooks dinta da reading materials, gaba daya sauran kayanta na tsohon Apartment dinta duk ta gansu a dakin alamar Jay ne ya kwaso mata su daga old apartment din nata, ta gama hada kan reading materials dinta, ta fara gyara kayan sawanta a press din dakin kenan taji an danna bell din gidan, ta
an yi jim to be sure a apartment din take jin karan bell din, after some seconds ta fita daga dakinta ta sauka downstairs bayan an sake danna bell din, ta karasa har bakin kofar ta bude a hankali tana duba waye a bakin kofar, yana kallonta calmly yace "Good evening Halysaah"
an murmushi tayi ta koma gefe don basa hanyar shigowa, yace "A'a kawai ki shirya, za mu je kiyi shopping abubuwan da kike bukata, i will wait for you inside in the car" Shiru Khaleesat tayi tana kallonsa, ganin zai koma motarsa tace "Amma ai ba abinda zan bukata yanxu, don naga akwai komai a gidan" Yace "For ur personal use Halysaah, beside ai babu cleaning agents a gidan, i forgot to get them..." Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, yace "I am waiting at the garage" Daga haka ya juya ya koma garage ta bi sa da kallo kafin ta rufe kofar ta juya ta nufi sama a sanyaye, bayan minti sha biyar ta sake saukowa downstairs tana sanye da jacket dinta, tana fita waje taji wani azababben sanyi duk da Jacket din jikinta, ta kulle gidan tana rike da makullin ta nufi motarsa, bude front seat din tayi ta shiga ta kulle, yace "Akwai sanyi ko?" Tana kara takurewa waje daya tace "Sosai, ni ban ma san akwai sanyi haka ba" Yayi murmushi ya kara dumin motarsa yace "Kina cikin gida da room heater ya za ayi ki san akwai sanyi" Murmushi tayi tana juya makullin hannunta ta
an kallesa a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya Halysaah, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Hope you are comfortable in the new house?" Ta gyada masa kai tana kallonsa, yace "Good to hear that..." Tada motar yayi suka bar garage din, bayan sun dan yi nisa da tafiyar a hankali tace "Yaya Junaid fa?" Sai a sannan ya kalleta yace "Ajay yana gida, he is under the weather, baya son irin season din nan" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Ya kika baro su Umma and Aunty Farida?" Tace "Mun yi chatting dasu jiya da daddare, Umma tace tana son ta maka magana if you are around" Yace "Ohk to idan mun koma gida sai in kira ta" Khaleesat bata sake cewa komai ba, jifa jifa dai take kallonsa, shi kam ya maida hankalinsa kan driving din da yake, Wani babban Shopping mall ya kai su, bayan yayi parking sun shiga ciki ya dau shopping cart yana turawa, zata amsa cart din a hannunsa yayi murmushi yace "No, don't worry Halysaah, i will do the wheeling and u do the shopping" Ta sauke idonta bata ce komai ba, gun cosmetics ya fara kai su yace "Ki dauki duk abinda kika san za ki bukata a nan Housemate..." Ta
aga kai ta kallesa, ya
an bude ido yace "Look Halysaah, i want you to be free and open with me, kar ki saka komai a ranki ko kiji nauyin tambayar wani abu da kika san kina da bukata, assuming i don't have the means ai bazan ce zan yi ba Halysaah, so feel free plss Housemate, haka jiya nace ki turo min Skin care set din ki ba ki turo ba, ni ina maki duk abinda nasan zan ma kanwata ne ko er uwa ta, so ki dau duk abinda kika san kina da bukata yanxu" Ita dai idonta na kasa bata ce komai ba, ya mika mata katin kudinsa yace "Ko in baki katin in jira ki a mota?" Ta
an kallesa sai kuma ta girgiza masa kai a hankali tana murmushin karfin hali tace "A'a" yace "Then shop all you need Housemate" Cikin sanyin murya tace "Ohk, Thank you so much" Shi dai murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba, few abubuwan da tasan zata yi needing take dauka a wajen cosmetics din tana ajiyewa a cart din da yake tura mata, amma idan ta dau abu daya sai ya kara mata biyu a kan wanda ta dauka, ita dai sai dai ta kallesa, ta dau set din Cream din shafawanta da shower gel, nan ma yayi doubling mata su ya zuba a cart, a hankali tace "Ina da saura fa" Bai ce mata komai ba, ta ci gaba da tafiya, tana kallon pad amma ta kasa dauka kawai ta wuce, shi ma kuma bai ce mata komai ba yana wheeling cart din har dai suka gama da bangaren cosmetics, ya nufi gun cleaning agents tana biye da shi abaya, duk shi ya dinga daukan abubuwan da yasan zata bukata a gida, sai bayan minti talatin suka fito daga shopping mall din ya zuba duk abubuwan da suka siya a booth din motarsa, maimakon su nufi gida sai taga ya kai ta wani babban store din Africa yace "I didn't get much cooking ingredients for you cause i am not good at that, so mu shiga sai ki dau duk me zaki bukata na girki...." Ta kallesa tace "To ai ko fara amfani da wanda ka siya ban yi ba" Yace "I know, zan
an yi tafiya ne Housemate, so i want to be sure you have enough of everything" Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, yace "Mu je" Daga haka ya sauka daga motar, jiki a sanyaye ita ma ta sauka ta bi sa zuwa cikin store din, Spices din girki da su seasoning, albasa, irish, dankalin hausa, doya, eggs, all kind of peppers, tomatoes, da dai duk wani mahadin girki suka siya a store din, sannan ya kara mata frozen chicken da turkey, sai beef, bayan ya biya kudaden suka bar store din, yana driving Khaleesat ta kallesa cikin sanyin murya tace "Thank you so much, Allah ya sa kafi haka" Yayi murmushi kawai, sai kuma ya dau wayarsa dake vibrate yana dubawa, ganin Ajay ne ke kiransa yayi picking ya kai kunne yace "How are you feeling?" After some seconds ya ajiye wayar, Khaleesat tace "Is he sick?" Yace "Yeah, i told you he is under the weather" Khaleesat ta yi shiru, Jay ya kalleta yace "Ko mu je gidan ki dubasa?" Ta
an buda ido, sai kuma tayi murmushi a sanyaye tace "Bazai kulani ba ai" Jay yayi dariyar da bai yi niyya ba yace "Saboda me bazai kula ki ba?" Ta sauke idonta tace "Jiya ma da ka je dauko makulli ai yayi kamar bai gan mu ba a mota" Jay yace "Jiyan nan ma da ku ka gansa ba shi da lafiya, sai da nace kar ya fita yaki saurarana, bayan ya fita kuma aka fara snow" A hankali Khaleesat tace "To Allah ya basa lafiya" Jay yace "Mu je can gidan za ki gaishesa?" Tayi shiru don har zuciyarta tana fargaban kar ya shareta, Jay yace "A bari next time ko?" Ta sauke idonta a hankali tace "To mu je, amma idan bai kulani ba ai shikenan" Jay yayi murmushi yace "Idan bai kulaki ba kema sai ki sharesa" Khaleesat ta
an kallesa suka hada ido, murmushi tayi har sai da dimple dinta ya lotsa tana kallonsa, ya dauke idonsa ya maida dubansa kan titi yana ci gaba da driving dinsa gently.
Chapter 126 · 0% Book details