Sashe 205
Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Wajen karfe shidda na yamma Malam Ali na tsakar gida bakin pampo yana alwala, Nenne na zaune kan farin kujeran roba tana kara jaddada masa abubuwan da za ayi ma Khaleesat na fita kunya tunda ba karamin gida za a kai ta ba, Tace "Wallahi Ali sai kaga setin kayan gadon aka ce mana miliyan uku babu ragin ko biyar, setin kujeru kuma Miliyan biyu cif cif, in ba 'ya yan sarakunan ba ma ni bana jin akwai er da za ayi ma wannan setin kayan dakin, ko iya su muka kai mata babu me renamu wallahi, akan dai ace mu cakalkala kudi mu siya mata tarkacen banza masu arha da baza a ga darajarsu ba, don haka ni dai ga dubu dari biyar ina da shi a ajiye, Parida zata kawo Miliyan daya tace, ita Zahra'u dama babu ita a lissafi in ba dogon hancinta zata kai kasuwa ta siyar ba, don haka nake baka shawara wannan gidan nan naka na Mariri da nawa ka siyar kawai mu fita kunya, ko miliyan hudu aka samu aka siyar da gidajen kaga ai sai mu fitar da er mu kunyar gidan sarauta Ali, wallahi hankalina a tashe yake ga lokaci da aka sa ba mai tsawo ba, kan kace me zaka ga kamar gobe ne" Malam Ali dake ta sauraronta ya idar da alwalan da yake sannan yace "Allah ya rufa asiri ya nuna yanda za ayi amma siyar da gida kam bai taso ba Nenne, shikenan fa gare mu...." A fusace Nenne tace "Baza ka raba kanka da kalman nan na shikenan gare ka ba, shi kuma wannan da muke ciki na gwamnati ne?" Malam Ali dai bai ce mata komai ba, don su ne suke ma gidan nan kallon gidan zamansu amma banda shi, har cikin ransa ya riga ya sa cewar gida ne aka basa ya zauna na
an wani lokaci ya tashi, Tsayuwar mota su
ka ji a kusa da gate, Nenne ta kalli gate din, can tace "Kaddai tsinannun iyayen Awdul din ne suka sake biyo ka..." Mikewa tayi ta nufi gate din fuskarta babu rahama, wasu manyan mata ta gani har su hudu cikin shiga ta alfarma, suna kallonta suka ce sannu, Nenne ta koma gefe tace "Yauwa sannun ku, ko batan hanya ku ka yi ne" Daya daga matan tace "Ba nan ne gidan su Halysaah ba?" Nenne tace "Eh nan ne, Khaleesat ba, Malaman makarantar su ne halan?" Matar tace "To mu dai shiga daga ciki ko?" Nenne ta juya ta koma ciki da sauri tana cewa "Bisimillan ku, sannun ku da zuwa, ai Khaleesar ma ta
an yi tafiya bata nan, amma ku shigo ciki" Suna biye da ita har zuwa parlon gidan, shi dai Malam Ali bai ce masu komai ba kamar yanda babu wanda ya ce masa komai balle su gaishesa, Nenne na shiga parlor ta kora yaran Mama Shatu dake zaune suna kallo, duk suka fita daga parlon, ko wacce a cikin matan ta samu kujera ta zauna a parlon, Nenne na murmushi tace "Halan kun samu labarin an sa mata rana ne, bari in kira maku uwarta tana ciki" Da sauri Nenne ta tafi dakin Umma ta sanar mata Khaleesat tayi baki kamar Malaman makarantar su a Amurka don ko wacce shiga tayi ta alfarma ga gwala-gwalai, a tare Umma da Aunty Farida suka fito parlor, haka kawai Umma taji gabanta ya fadi, ta dai karaso parlon ta zauna ta gaishesu duk suka amsa, Aunty Farida ma ta gaishesu tana kallonsu, ledan pure wata guda Nenne ta kinkimo ta kawo masu tsakar parlon ta ajiye tana cewa "Wallahi yaran duk sun shanye wanda ke prij me sanyi" Matar dake tanka Nenne tun daxu tace "Mun san duk baku san mu ba, baku kuma san daga inda muke ba" Nenne ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "Ba Malaman makarantar su Khaleesah bane a Amurka?" Matar tace "Ko daya, ni sunana Hajiya Fatima, kuma ni din kanwata ce ga Mai martaba Sarkin Bauchi..."
abbara Nenne ta saki ta mike tsaye tana tafe hannu tace "Lale lale, lale marhaba, sannun ku da zuwa, ashe manyan ba
i muka yi bamu sani ba, wallahi ba a sanar mana kuna hanya ba" Hajiya Fatima tace "Yana da kyau dai ki fara sauraronmu ki ji me ke tafe da mu tsohuwa" Nenne ta zauna kan Carpet tana kara masu sannu da zuwa baki har kunne, Hajiya Fatima ta nuna warce ke zaune gefenta tace "Fulani Asiya kenan, matar yayanmu Marigayi sarki Ahmadu Yusuf, mahaifiya ga Ahmad Jawwad...." Nenne tayi shiru tana kallon Mami da idanuwanta kamar za su fito, haka ma Umma da Aunty Farida da duk jikinsu yayi sanyi tun Hajiya Fatima bata fara introduction ba, suna ganinsu sun san babu alkhairi a tattare da zuwan su dama, Hajiya Fatima ta ci gaba da magana cike da isa da gadara tana nuna warce ke zaune 2 seater tace "Wancan Hajiya A'isha kenan kanwar Fulani Asiya, ta kusa da ita kuma Hajiya Nafisah kanwar matan Mai martaba Sarkin yanxu...." Nenne tayi karfin halin cewa "To Allah Ubangiji dai yasa lafiya, don ni ban gane kan wannan zuwan naku ba kuma" Hajiya Fatima tace "Gaskiya ba lafiya ya kawo mu ba tsohuwa, duk da zuwa muka yi cikin lumana ba tare da wani tashin hankali ba" Nenne ta
aga kai ta kalleta baki bude, cikin nutsuwa Mami ta fara magana tace "Ni ce Mahaifiyar Jawwad, kuma Jawwad shi kadai Allah ya bani a duniya, a burikan da nake da shi kan Jawwad a duniya babu auren bazawara ciki, ko kuma auren wata kabila can baya ga cikakkiyar Hausa Fulani, tun daga neman auren da aka zo aka yi na
a na har saka rana bani da masaniya akan ko daya, sannan duk wani bautatawa da kashe uban dukiya da Jawwad ya dinga yi akan er ku da ma ku kanku babu wanda ban sani ba, amma duk ba wannan ne damuwata ba, kuma bazan ce zan amshi duk wani abu na alkhairi da yayi maku ba, kamar yanda nace maku mun zo cikin aminci ne babu tashin tashina, don haka tun da girma da arziki ku cire ran auren er ku da
a na Jawwad idan ba haka ba wallahi duk wani mummunan matakin da na dauka a kanku ku kuka siya, er ku ba sa'ar auren Jawwad bace don shi din
an gidan sarauta ne,
an sarki jikan sarki babu abinda zai yi da er ku bazawara, kai ko da ba bazawara bace wallahi babu abinda zai yi da wata kabila warce ba ma na kasar nan ba, ina sake jaddada maku tun da girma da arziki ku janye batun auren er ku da
a na...." Cousin sister din Aunty me suna Aunty Nafisa tace "Iya tatsarsa da ku ka dinga yi ma ya isa haka, don hidimar da yayi maku in muka ce yafi na miliyan dari biyu tsaf bamu yi karya ba, da ace tsiya ya kawo mu hatta gidan nan wallahi sai mun kwace amma mun zo maku cikin lumana don mu din ba kananun mutane bane kuma mun fi karfin dukiyar da Jawwad ya kashe maku, kawai abinda za ku yi a zauna lafiya shi ne ku janye batun auren nan cikin ruwan sanyi tun kan tijara ya biyo baya" Har sannan Nenne ta kasa rufe bakin da ta hangame zaune kan Carpet with shock, Aunty Farida tayi wani murmushi tana kallonsu daya bayan daya tace "Mu janye batun aure sai kace mu muka je neman auren Jawwad din?
Ina ce wa enda suka zo neman aure su za su dawo su janye sannan su amshi kudin da suka kawo, kuma ni a iya sanina ba mata bane suka zo neman auren Khaleesat, mazan nan dai da suka zo neman auren su nake tunanin za su sake dawowa su ce sun janye a maido masu da kudin
an su, ko kuma mafi sauki in kin isa da
an ki ai tun daga gida zaki masa umarnin ya janye ba sai kin zo mana nan ba, a yanxu mu dai bamu da sauran magana da ku sai dai iyayenmu maza su saurari wakilan Mai martaba, duk da dai ban san ko gidan sarautar taku har dankwali da dankwali na zama batun neman aure ba" A tare Hajiya Fatima da Hajiya Nafisah suka mike suka daka mata wani tsawa suna nunata da
an yatsa, Hajiya Nafisah tace "Ke karamar er iska mu kike gaya ma magana?
Kin san su waye mu?