← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 218

Sashe 195

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don haka maza mu shirya gobe mu tafi Bauchi mu samo mafita, farkon zuwan Ali furson ai can naje kishiyar Murjan ta rakani gun babanta ya bani taimako, babban bawan Allah ne mutumin a kauyen, kuma gun iyaye da kakanni ya gaji wannan baiwa tasa, in muka ce za mu biye Zahra'u da Ali to fa Khaleesah na cikin gararin rayuwa, miji wawa mata wawiya ga su matsoratan banza, don haka gwara mu rufa ma kan mu asiri Farida kar a mana dariya, naga ke da wayewar ki kuma kina da wayo, sannan hankalina bai kwanta ma ace mu tafi ba Khaleesah ba kar shegen yaron ya sake lallabowa ya dauketa tunda ba addini ne da shi ba, gwara mu je da ita kawai ayi abinda za ayi" Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah ya kai mu goben Nenne" Nenne tace "Allah ya maki albarka, ku hada kayanku a akwati daya ke da Khaleesar, Ni kuma zan zuba ko a bacco bag ne mu kama hanya" Alhaji Musa ne zaune parlon sa wajen karfe sha dayan safe yana waya, Momy dake zaune ta hakikance kan kujera sai kallonsa take har ya idar da wayar ya ajiye, rai bace tace "Yanxu suna nufin su ce uban yaki amincewa kenan Alhaji??" Alhaji Musa ya sauke ajiyar zuciya yace "Gashi kuwa kina jin yanda muka yi a waya da Deputy, ban ta
a tunanin zai yi turning down din maganar nan ba duba da irin mutanen da suka je har gida suka samesa, idan Abdallah zai yi hakuri ya saka ma ransa salama ina ga zai fi alkhairi, this was the only option I tot will work" Momy tayi mitsi mitsi da ido tace "Amma wannan mutumi anyi tsinannen talaka, ko duba girman mutanen da suka je har gabansa suka zauna bai yi ba, banda Abdul ya nace har yana neman yi ma kansa illa ya ja min asara don Allah yaushe za mu zubar da girman mu da mutuncin mu haka a gaban talaka fakiri?" Alhaji Musa ya sauke ajiyar zuciya yace "Yanxu ke a matsayin ki na uwarsa babu hanyar da zaki bi ki masa magana ya saka ma ransa salama ya mance wannan yarinya ya hakura?" Cike da damuwa Momy tace "Wallahi Alhaji nayi, ba irin yanda ban bi da shi ba a matsayina na uwarsa amma abun yaci tura, ko baccin kirki Alhaji bana iya yi saboda halin nan da Abdul ya jefa kansa kan wannan er talakawan, ace mutum bazai ci abinci ba kullum gashi nan gashi nan dai ne kamar wanda ya fara samun matsala a kwakwalwa to ina lafiya a nan Alhaji?

Kar wani abu ya samesa fa mu shiga uku shi Kenan garemu a duniya, shi yasa na kawo maka shawaran ka hada kan manyan abokanka ka nemi alfarman su je maka su samu matsiyacin uban yarinyar amma daga karshe dubi abinda yayi ma masu, nasan su kansu za su ga sun zubda mutuncinsu gaban mutumin da bai wuce drebansu ba" Alhaji Musa dai girgiza kafa kawai yake don shi kansa halin da Abdul ke kokarin jefa kansa ciki ba karamin damunsa yake ba, ya kira Malam Ali yayi sau uku tun ma lamarin Abdul din bai yi worst haka ba amma bai daga kiransa ba bai kuma biyo sa ba, har yayi zuciya ya goge numbersa, da ya ga dai Abdul bazai ta
a hakura ba yasa ya hada kan manyan abokansa ya turasu kamar yanda Momy ta basa shawara amma duk da haka babu wani fruitful result, mikewa Momy tayi ta fita daga dakin ranta a dagule ta tafi dakin Meemah, cike da damuwa tana kallonta tace "Meemah yanxu menene shawaranki akan wannan hali da
an uwanki ke kokarin jefa kansa?

Yanxu haka fa tun jiya da safe yaki bude daki, ba ci ba sha, ban san wani hali yake ciki ba, tsorona kada wani abu ya samesa fa in shiga uku Meemah shikenan gare ni a duniyar nan" Sai kuma ta zauna gefen gado ta dafe kai ta fashe da kuka sosai, Meemah ta sauke ajiyar zuciya, ita fa ko kadan halin da Abdul ya jefa kansa ba wani damunta yayi ba in dai akan er talakawan can ce, ace duk class da girman kai irin nasa amma kan er matsiyata ya nemi maida kansa kamar mahaukaci zautattace, Cikin rawan murya Momy tace "Wallahi kwanaki da naga abun nasa yaki ci yaki cinyewa har kudi na bada a min aikin da zai maido hankalin yarinyar kansa amma a banza Meemah, in ba dai zuwa zan yi in tone abinda nace maki an bani na binne a garden ba in
one su" Meemah ta wani kalleta, can tace "Kema dai wallahi Momy, ki tone me kuma?

Don Allah ki rabu da Abdul zai dawo dai dai nasani, lallai ne sai mutum ya samu abinda ya kwallafa rai dama in ba don yaga kuna biyesa ke da Daddy ba, ai abun nasa har da iskanci, ita kadai ce mace a duniya bayan ga mata wa enda ma suka fita komai" Wani tsawa Momy tayi mata tace "Tun ba yau ba nasan baki da imani baki da tausayi Meemah, kuma mugun nufinki akan Abdul sai dai ya kare maki wallahi, in dai dawowar yarinyar garesa ne zai dawo masa da farin cikinsa to ina maraba da hakan wallahi, da nasan wannan abun ne zai biyo baya yaushe har zan raba su ta karfi da yaji??

Ai da sai dai in ta gana mata azaba a gidan nan, amma ina neman rasa yarona akan mace kice kar in damu, to wallahi zan je in tono layun in Kona, sannan in har sato ta ne kadai mafita ni da kaina zan basa shawaran yayi hakan, dama wancan karan ma ai sato ta din yayi daga Lagos, ko ba a daura auren ba ya tafi duk inda zai tafi da ita kawai, yanxu ai jin
an ta take budurwa shi yasa zata yi ta iskanci tana rawan kai, kawai na cuci
a na a banza a hofi saboda dalilina mara tushe" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, Meemah ta wani kyabe baki tana ci gaba da danna wayarta, da wuka Momy ta tafi garden din kamar dai zata yanko vegetables, tayi bake bake ta tona ramin da ta binne layun ta ciro tana kare masu kallo, sannan ta tafi kitchen zata
onasa saman gas...

Tun da Khaleesat ta sanar ma Jay mutanen da mahaifin Abdul ya aiko wajen Babanta hankalinsa bai sake kwanciya ba kamar yanda nata hankalin ke a tashe tun daren jiya, gaba daya yaji zaman Abujan ma kamar a
aya yake, at first bata ma gaya masa ba sai da suna waya da yaji mood dinta da yanda take responding sai ya tambayeta abinda ke damunta shine har ta gaya masa, bayan la'asar Ajay ya shigo daki rike da Glass cup na Smoothie da Ammi tayi masu, ya ajiye ma Jay nasa yana kallonsa yace "Anything?" Jay ya kallesa kamar bazai ce komai ba, after a while kawai ya gaya masa abinda Khaleesat ta sanar masa, Ajay yayi shiru na kusan minti daya after listening to Jay, can ya kallesa yace "I think kawai ka samu Mai martaba da maganar, since Mami ta nuna maka she is fine with ur choice, gobe da safe sai mu koma Bauchi ka gaya masa ta amince....

But i will advise you duk yanda ku ka yi da Mai martaba kar ka gaya ma Mami, don nasan shi idan ya tashi zartar da ko wani hukunci sai ya gama zartarwa yake sanar da kowa" Jay dake kallonsa yace "Amma me yasa kace kar in gaya ma Mami yanda muka yi da Mai martaba?" Ajay yace "Just an advice, Ina ga kamar in baka gaya mata ba process din zai fi tafiya smoothly kuma da sauri, baza a tsaya wasu sirfa ba or anything of such, You know our mothers and exaggerating of things" Jay dai yayi shiru bai ce komai ba, Ajay ya
an yi murmushi yace "Dama nasan gayen nan bazai hakura ba, and he can do anything silly, I don't even think she is safe in kano...."
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah* ur evidence via 07087865788
*TAKAICIN UBA
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.

Masu bu
ata daga farko su yi following channel
inmu.
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T
Driving yake yana sauraron Karatun Alkur
ani daga k
ar sudais.

Shi ka
dai ne abinda yake saurare ya rage masa zugi da ra
din rashin Hibbarsa.

Ko da ya yi parking a makeken wajen shak
atawar kasa shiga ya yi ya shiga cusa hannayensa cikin tarin sumar gashin kansa da ya gadota daga gurin Ummeeynsa.

Ya dinga cukuikuye gashin yana jin kansa na sara masa kafin ya mayar da seat
din kujerar ta sa ya koma ya kwanta tunanin rayuwarsu da Hibba na sake bujiro masa
arar da wayarsa ta yi ne ya farkar da shi daga wancan tunanin, ba sai ya kalli screen
din wayar ba ring tone
din ya sanar da shi wacece
Ummeey
ya fa
da yana sakin murmushin gefen kumatu kafin ya jawo wayar ya kanga a kunnensa.

Cikin muryar shagwab
a kamar yarda ya saba mata magana ya ce
Hayateey!

Ummeey daga
daya gefen ta saki murmushi tana
jin da
din sunan da yake kiranta da shi.

Amin ya gida hope dai kana lafiya, muma kwanan mu uku a Nigeria.

Ya
dan yi dum da waya a kunne kafin ya ce
Nigeria kuma how comes?

Ya aka yi Abeey ya barku kuka je?

Dariya ta yi sosai kafin ta ce
Da kansa ya sauko ya ce mu je.

Yauwa ba wannan yasa na kira ka ba, Amin bu
de kunne da kyau ka ji lokaci ya yi da ya kamata ka yi aure.

Wani irin dum ya ji k
irjinsa ya buga, Ummeey zata sake janyo masa wani jidalin kenan shi tun yaushe ya cire maganar aure a rayuwarsa, ya Riga ya gama da wannan babin an gama samun mata na gari tun bayan da Hibba ta rasu.

Ba ka ji ni ba ne?

Ummeey
din ta fa
da with a serious tone.
Chapter 195 · 0% Book details