← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 218

Sashe 16

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

The flight to the United state was so comfortable for Khaleesat in her business class seat, don throughout bacci tayi, karfe hudu saura na asuba jirginsu ya sauka Maryland, It was soo cold in Maryland gashi bata da sweater a kayanta, bayan ta fito da luggages dinta tana duba Uber da zai kai ta gida tana rike da wayar kamar ance ta daga kai taga motar da yayi parking, kallo daya tayi masa sai kuma ta sauke kai kasa, ya karaso har inda take yace "Jirgin ya dade da sauka ne?" Sai a sannan ta kara kallon Sleepy face dinsa, sai kuma ta girgiza kai tace "Aa" Yace "Ohk let me drop you home" Daga haka ya koma gun motarsa ta bi bayansa with both of her luggages, ya bude booth ya amshi daya trolley dinta ya sa a booth, ita ma ta sa dayan, ya zaga ya shiga driver seat, tana jan kafa ta karasa front seat ta bude motar sannan ta shiga tana kallonsa da gefen ido, jinginar da kansa taga yayi da kujeran motar idonsa a lumshe, ta kulle motar gently, after few seconds ta sake kallonsa ga mamakinta sai taga kamar fa bacci yake, kallonsa ta dinga yi, and they seated for almost 3 minutes a haka ita dai bata tashesa ba kuma bata ce komai ba, Vibration din wayarta ne ya sa ya bude ido, ya wara ido ya fara kokarin tada motar, bude jakarta tayi to stop the alarm din da ya sa wayarta ke vibrate, bayan ya ja motar sun bar wajen, still not sounding normal yace "Ya jikin Mama?" Ta sauke idonta tace "Alhamdulillah, You shouldn't have bothered coming tunda akwai Lyft ko Uber" Without looking at her yace "The house key is with me, shi yasa na taho, cause i estimated when u are arriving" Bata sake ce masa komai ba shi ma haka, a haka har suka iso gida yayi parking, ya sake jinginar da kansa da kujeran motar, ita dai ta bude motar gently ta fita, jin fitarta ya sa ya bude ido, shi ma ya sauka daga motar, Entrance din shiga gidan ya nufa ta bi bayansa, Pajamas ne jikinsa sai Jacket da ya saka saboda sanyi, yana isa kofar ya kai hannu aljihu alamar zai ciro makulli, still taga yayi a bakin kofar, ita dai kallonsa kawai take, after some seconds ya juya yana kallonta, zuwa sannan his eyes are very clear gaba daya baccin ya gudu jin babu makulli jikinsa, ko bai gaya mata ba ta fahimci baya tare da makullin gidan, ya
an sosa kai yace "I think....

I think, i left the key at where i am coming from, i am sorry about that Halysaah" Sauke idonta tayi without saying anything, ya juya ya nufi motarsa ta bi sa da kallo, sai da ya isa gun motar ya juyo, da sauri ta dauke kanta daga kallonsa, yace "Mu je in dauko makullin, ba wani nisa zuwa can, kinga it's cold out here baza ki iya tsayawa cikin sanyi ki jirani in dawo ba" Bata yi musu ba ta koma gun motar don yanzun ma sanyin take ji sosai, sai da ya shiga sannan ita ma ta shiga, his car was so warm, ya tada motar suka bar garage din, inda yace mata babu wani nisa taga sunyi tafiyar kusan 15 mins basu kai ba, nan taji gabanta ya fara faduwa, lkci lkci take
an satan kallonsa ta gefen ido, wani unguwa suka shigo wanda ko wani gida da gate dinsa unlike some houses in US, daga karshe taga yayi parking ba tare da ya kashe motar ba yace "Let me get the keys" Bude motar yayi ya sauka ta bi sa da kallo taga gate din kusa da su ya bude ya shiga, tsaf take iya kallon hadadden gidan dake ta cikin gate din don ba irin gate dinmu na gida bane, ita dai sai bin unguwan take da kallo wanda ko ba a fada maka ba kasan na masu hannu da shuni ne a Amurka din, ba a wani dau lokaci ba sai gashi ya fito da wani Huge Dog dake biye da shi yana shisshige masa, wani faduwa gabanta yayi don a duniya tana mugun tsoron kare, ya duka yana patting Dog din yana masa magana at the same time, wani matashi ne dogo just like him ya fito daga cikin gate din gidan sanye da Pajamas shi ma, Khaleesat ta dinga kallonsa as if ta ta
a saninsa amma kuma bata san sa from anywhere ba, tana kallonsa tana gyara mayafin kanta kar ma ya kalli direction dinta su hada ido da shi, gabanta kuwa sai faduwa yake kamar mara gaskiya, matashin ya jingina da gate crossing his both legs yana kallon Housemate dinta taji yace "Daga ina kake?"
in basa amsa Housemate din nata yayi instead ya mike yana tura masa
aton karen don karen tsaf zai ce zai bi sa, Calmly matashin yace "Ina za ka?" Housemate dinta ya kallesa yace "You have any issue with that?" Matashin ya
an kalli motarsa calmly yace "Is that a lady in ur Car?" Housemate dinta yayi kamar bai ji sa ba still pushing the Dog to him, Matashin ya sake kallon motar, Khaleesat tayi saurin kauda kanta, tabe baki yayi yace "Enjoy" Daga haka ya ja karen suka koma cikin gidan, Khaleesat da duk taji conversation din nasu taji ranta ya baci, House mate dinta ya dawo cikin motarsa ya kulle without looking at her yace "Sorry for keeping u waiting Halysaah" Yana fara driving ta hade rai tace "Mene yasa bazaka gaya masa i am just ur housemate ba da kuma dalilin da yasa ka kawo ni nan din?" Housemate dinta yace "Never mind, ba wai yana da hankali bane"
07087865788
HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
8.......

Har suka isa gida babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu, yana parking a garage ya bude motar ya sauka, ita ma ta sauka tana satan kallonsa, kofar entrance din parlor taga ya nufa without looking at her, hakan yasa tana tafiya a hankali ta bi bayansa, ya bude kofar parlon ya juya ya kalleta, ita ta fara shiga parlorn sannan shi ma ya shiga ya kulle kofar, dakinta ta tafi bayan ta bude kofa ta juya ta kallesa, kwanciya taga yayi a kan 3 seater ya lumshe ido, ta shiga dakinta kawai ta kulle.

Washegari da safe karfe takwas da 'yan mintuna Khaleesat ta fito daga dakinta, zaune ta gansa da text books a gabansa alamar he is studying, yana daga kai tayi saurin dauke idonta daga kallonsa, har ta karaso cikin parlon ta tsaya jikin kujera tana wasa da edge din mayafin jikinta, a hankali tace "Ina kwana" Ya ajiye pen din hannunsa yace "Good morning Halysaah" Still bata dago kanta ba kuma bata fasa wasa da gefen gyalenta ba, yace "How was ur trip?" Ta
an kyafta ido tace "Alhamdulillah" Yace "Sorry jiya ban tambayeki jikin Mama ba, i was sleepy hope she is better now?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, tace "She is fine Alhamdulillah" Yace "Hope ur mind is now at rest?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, sai kuma ta
an gyada masa kai, wayarsa ne ya fara ring ya dauka sannan yayi picking ya kai kunne, ta
aga kanta tana kallonsa, taga shiru yayi alamar yana sauraron abinda ake gaya masa a wayar, after few seconds yace "It should be upstairs then" Daga haka ya katse wayar ya ajiye ya daga kai, da sauri Khaleesat ta dauke kanta daga kallonsa, Yace "Hope nothing Halysaah?" A hankali tace "Kawai, i want to appreciate you, thank you so much, Allah ya saka da alkhairi...." Cikin calm voice yace "No, You need not to Halysaah, iya abinda zan yi ma kanwata na maki ai" Cikin sanyin murya tace "To Nagode Allah ya saka da alkhairi" Ya
an yi murmushi yace "To Ameen, so u can be this calm?" Ta wani kallesa, yace "Makarantar zaki tafi baza ki bari ki huta from ur long journey ba?" Ta sauke idonta tace "I am having presentation today" Yace "Ohk then, Allah ya bada sa'a" A hankali tace "Ameen" Ya nuna mata Trolley dinta da ya shigo mata da shi parlon yace "Ga boxes dinki can" Ta kallesu tace "Thank you" Yace "You are welcome" Daga haka ya ci gaba da abinda yake, Sai da ta kai su dakinta sannan ta dawo ta nufi kitchen, Tea kawai Khaleesat ta sha da Cookies sannan ta dauko jakarta zata wuce makarantar, makullin gidan ya mika mata yace "The house key...." Ta tsaya tana kallonsa, sai kuma tace "Ain't u using it?" Ya daga kafada yace "Will sort my self out" Shiru tayi at first, can kuma ta nufesa ta amshi makullin tace "Thank you" Yace "You are welcome" Daga haka ta fita daga gidan ta kullo masa kofar.

Khaleesat na tafe tare da Safiyyah dake mata mitar Ya Mustapha yace bata daga kiransa, ita dai Khaleesat tafiyarta kawai take bata ce komai ba, Safiyyah ta tsaya tace "Ohh ga gantalalliya na maki magana ko?" Khaleesat ta tsaya tana kallonta tace "To me zan ce Sophie?

Ke kanki kinsan ina da wanda zan aura to menene amfanin in daga wayar Yaya Mustapha?

Beside wallahi ko da bani da wanda zan aura ni bazan kulasa ba, ai ana barin halaq ko don kunya" Da wani expression Safiyyah tace "Ban gane ba, as per cewar Surayya cousin sis dinki ce ko kuma kawarki ce?

Where did u know her from?

Meye hadinki da ita da har za a bar halal don kunya?

Can you hear ur self pls?

If you are not interested in my cousin brother ba sai kin ta corner corner ba kina kawo zancen da hankali ma bazai dauka ba, meye hadinki da wata Surayya da zaki bar halal don kunya?" Khaleesat tace "Ni dai don girman Allah ki ma bar wannan zancen, Ya Mustapha kuma kiyi ma Allah ki gaya masa i am engage, ni bazan daga kiransa ba" Safiyyah tace "Wallahi bazan fada ba ai kina da baki ki gaya masa da kanki, ke da wa aka yi engaging da zance masa u are engage?
Chapter 16 · 0% Book details