← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 218

Sashe 102

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ki kwasa ki nuna masa tunda baki da seti" Khaleesat ta wani hade rai ta kauda kai, Nenne tayi kasa da murya tace "Ae sai ya fita duk zaki yi komai cikin sirri, yanxu boyewa zaki yi inda ko da wasa bazae gani ba" Khaleesat tace "Toh ae zae ji warin hayakin kuma, sannan ni bama ni da abun yin turaren wutan ai" Nenne tace "To dama ai shegen a gantale ya dauko ki bai bari duk mun shirya maki turaren wuta ba da sauran abubuwan da ake kai mata da su gidan miji, yanxu dai nasan shi zai maida mu gida ina da manyan robobin turaren wuta har biyu da na ajiye maki zan basa turaren da kasko ince ya tsaya gun masu siyar da gawayi a bakin hanya ya siya maki ko leda uku ne ya taho maki da shi, sai ki dinga hurawa a kaskon tunda ga AC a parlon nan da nan zai kama maki in kika hura" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba, Nenne tace "To shikenan ki maida ni mahaukaciya ina kokarin taimakon rayuwarki" Khaleesat tace "Na ji" Nenne tace "Yauwa to, yanxu gasu nan maza ki je ki boye inda bazai gan su ba kwata kwata" Khaleesat ta amsa ta nemi waje a nan kitchen din ta boye, Nenne tace "Yauwa to haka ake yi, yanxu maza tafi ki ce masa zamu tafi kar ya ga mun zaune masa a gida, dama ni wnn abubuwan yasa nayi ta doka masa kira yau kwana uku kenan, har Allah yayi ya zo ya dauke mu" Mikewa Khaleesat tayi ta fita daga kitchen din Nenne na biye da ita murya can kasa tace "Ko ruwan gidansa mu dai bamu sha ba balle yace" Khaleesat na tafiya a hankali ta nufi dakin Abdul, knocking tayi tana jiran ya amsa, after almost a minute ya bude kofar, ta sunkuyar da kanta tace "Za su tafi" juyawa yayi ya koma dakinsa, hakan yasa ta dawo parlor, Nenne na kallonta tace "Kin gaya masa?" Kai ta gyada mata ta tafi kusa da Aunty Farida ta zauna a kasa, Su Mama Shatu kana ganin fuskokinsu kaga bakin ciki da hasadda karara a kwance, bayan kusan minti biyar Abdul ya fito daga dakinsa yana murmushi yace "Har za ku koma Kaka?" Nenne tace "Wallahi kuwa Awdul, ai dama ba zama za mu yi ba, ni dai nayi farin cikin ganin jikata cikin kwanciyar hankali dama duk haka muke so" Shi dai bai ce komai ba, Nenne ta mike tace "Don haka yanxu sai ka maida mu gida kawai" Abdul yace "Toh naga ko abinci bata baku ba ai" Nenne tace "A'a mu muka hanata don duk a koshe mu ke, ruwan ma in ka lura ai bamu sha ba" Shi dai murmushi kawai yayi, a haka Nenne ta kada keyarsu Mama Zubaida da Mama Shatu suka fita daga parlon, Ita dai Khaleesat na biye da su duk jikinta a sanyaye, Aunty Farida ce last din fita a parlorn, tana kallon Khaleesat tayi kasa da murya tace "Za ki ga sako na ajiye maki bayan throw pillow din kujeran da na zauna, kar ki damu kafin in koma lagos zan samu lokaci in zo ni kadai kin ji?" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Bayan Abdul ya bude motarsa ya kalli Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi ganin su Aunty Farida za su tafi, yace "Mu je sai mu yi dropping din su mu dawo" Nenne dake kokarin shiga bayan mota ta dakata tace "Toh ai babu waje a motar, a ina zaka dora ta Awdul?" Aunty Farida tace "Sai ta shiga gaban motar Nenne ni in koma baya" Nenne tace "A'a babu ruwana wallahi, a irin narka narkan jiki na Shatu da Zubaida mu uku ma ya muka kare a baya balle kin shigo cikinmu Farida?

Ko dai a cinyar su zasu dora ki?" Shi dai Abdul murmushi kawai yayi, Khaleesat tace "Toh ni sai in zauna a bayan" A fusace Nenne tace "To ke dole sai kin bi mu ne kamar en matan amare?

Kawai don na zo gidanki sai in koma gida da ciwon jiki? ni wallahi in da matsi a mota ma bana shiga, da mun sani da bamu taho da Zubaida ba don duk ita ta cika waje..." Abdul ya kalli Khaleesat yace "Don't worry, ki koma ciki kawai" Hawaye ne ya cika idonta tana kallonsa, Aunty Farida ta yi ma Nenne wani kallo ta shige gaban motar, Nenne ta kyabe baki ta shiga bayan motar tana hararansu Zubaida da su ma duk suka shiga motar kuma babu warce tayi gigin gogan jikin Nenne a cikin motar, Nenne tace "To duk ku sauka Khaleesah ta fara shigowa ta dawo kusa da ni tunda ba wani auki gareta ba, ku ne abun tsoron dama" Babu musu duk suka sake sauka daga motar suka koma gefe, Nenne na kallon Khaleesat tace "Ba sai kin yi kuka ba, shigo ki matso kusa da ni mu ga adadin wajen da zai rage, in ya kama wata sai ta hau adaidaita sahu" Khaleesat ta goge idonta ta karasa ta shiga cikin motar ta matsa kusa da Nenne, space din da ya rage a motar tsaf zai dauke su Mama Zubaida, Nenne ta tabe baki tayi kasa da murya tace "Duk fa wari suke, in Farida ta shigo nan ai jikina za su rakube in ta shakan wari su cuce ni, in de ba kusa dani Faridan zata dawo ba, kuma Zubaida duk ta fi warin, banda akwai turare da AC a motarsa ai da mun ji kunya" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba su Mama Zubaida suka shigo motar Nenne na yatsine yatsine, a haka suka bar gidan.

Sai kusan karfe biyar suka isa Mariri, bayan Abdul yayi parking dai dai kofar gidansu Khaleesat Nenne ta bude motar ta sauka tare da Khaleesat, su Mama Zubaida ma duk suka sauka da Aunty Farida suna ma Abdul godiya sannan suka shiga cikin gida, Nenne na gyara gyalenta tace "To Allah yayi maka albarka Awdul mun gode, amma dai zan yi maza in karasa gida akwai sakon Khaleesat da zan dauko in bata tunda Allah ya kawo ku ta tafi da kayanta kawai" Yana zaune driver seat ba tare da ya juya ba yace "Toh Kaka" Tana kallon Khaleesat tace "Mu je ki taho da sakon" Khaleesat bata ce komai ba ta fara bin Nenne zuwa gidanta, bayan sun yi nisa Nenne tace "Ai kinga shegen bai ce bari ya karasa gidan nawa da mu a motar ba, gaba daya baya ganin mutuncin gidana dama" Ita dai Khaleesat tayi kamar bata ji me tace ba, har suka isa gidan Nenne Khaleesat na gaisawa da mutanen anguwan, Nenne tace "Munafukai, sun yi mamakin ganin ki haka ai, kinsan duk ca aka yi kin shiga duniya kin gudu, sai daga baya kuma aka ji kina gidan mijin ki" Murmushi kawai Khaleesat tayi, bayan sun shiga gidan Nenne ta dauko turaren wutan ta saka su a katon leda da kasko biyu sannan suka fito, suna isa kofar gidansu Khaleesat Nenne ta saka ledan a bayan motar Abdul tana cewa "Kaga har mun dawo Awdul, dama turaren wutan ne ba wani abu ba, don haka ku yi maza ku tafi kar Magariba ya tarar da ku a hanya" Yace "To Kaka" Khaleesat na kallonsa tace "Zan shiga in gaida Ummata" Bata jira cewarsa ba ta shiga cikin gidansu ya bi ta da kallo, ko minti uku bata yi da shiga dakin Ummanta ba sai ga Nenne, tana tsaye bakin kofar dakin bayan ta dage labule tace "Abun kuma ba hauka bane ai, taso ki fita yana jiran ki..." Khaleesat ta daga kai tana kallon Nenne, Nenne tace "Ae sai yayi mana kallon mutanen banza marasu hankali, taso nace ki fita kar ki ja mana reni" Umma na kallon Khaleesat tace "Ku je Khaleesat, kin ga yamma tayi" Fuska a daure Khaleesat ta mike ta fita daga dakin, Nenne ta rakata har bakin motar Abdul, tana shiga gaban motar yayi ma Nenne sallama ya ja motarsa ya bar wajen, har suka isa gida ana kiraye kirayen magrib bai ce mata ba, ita ma bata ce masa komai ba, bayan yayi parking ya sauka motar ita ma ta sauka, tana tafiya a hankali ta bi bayansa suka shiga gidan, Kitchen ya shiga direct, har zata wuce dakinta ta tuna sakon da Aunty Farida tace ta bar mata kan kujera, ta karasa inda Aunty Farida ta zauna ta dauke throw pillow din wajen ta dinga kallon Dollars din dake ajiye da wayoyi biyu, daukan 1000 dollars din tayi wanda Jay ne ya bata da zata dawo Nigeria, ta dau wayoyin biyu, daya na Ajay daya na Jay, lkci daya jikinta yayi sanyi hawaye suka cika idonta, muryar Abdul taji a kanta yace "What's that?" Da sauri ta boye hannunta a baya tana kallonsa tsabar yanda ta gigice.
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
We sell all kind of children school shoes, school bag, Lunch box, Readymade for children....

Atamfa, Lagos laces, veils, Handbags, shoes, lafaya, jewelries, kitchen items e.t.c.....

All at affordable prices
Akwai adashin kayan kitchen, kayan yara and atamfa with laces if interested....
Chapter 102 · 0% Book details