← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 218

Sashe 109

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ma ai shegen ne tunda ba karasawa yake yi gidana ya gaisheni ba, banda kaddara a ina za mu san sa har mu aura masa Khaleesat mutumin da baya ganin mutuncin mu, kana masa magana yana amsa maka cikin gadara da yanga wai shi
an Alhaji Musa, waye bai san satan da ubansa ya zabga a gwamnati ba kafin ya koma kasuwanci, ko don muna kauda kai?" A takaice Aunty Farida tace "To sakin ta yayi..." Nenne ta juya ta kalli Aunty Farida na en sakwanni, can tace "Ban ji me kika ce ba Parida?" Aunty Farida da har hawaye ya kawo idonta tace "Sakinta Abdul din yayi" Nenne ta kasa motsi a inda take tsaye, a hankali tace "Sakin aure ko sakin me?" Aunty Farida dai bata tanka ta ba, ita dai Khaleesat na kwance tayi backing din Nenne bayan surutunta ya tasheta daga baccin da take, Nenne ta saki wani salati muryarta na rawa tace "Wato dai
an nawa ne ba a son a ga ya zauna lafiya a gidan duniya kamar yanda kowa yake zaune" Fita tayi ta koma tsakar gida ta rushe da kuka sosai tace "Allah ya isa tsakanina da Zahra'u da er ta, babban burin su a duniya su ga Ali ya tagayyara, babban burinsu su ga Ali cikin mawuyacin hali cikin tashin hankali, banda haka ko dukanta da zaginta Awdul ke yi a gidan bazata hakura ta zauna ba albarkacin ubanta?

Shi ne har zata amshi sakin da yayi mata hannu bibbiyu ta dawo mana gidan nan domin shari'arsu da Ali ya dawo sabo?" Mama Zubaida da Mama Shatu tuni suka mike tsaye jin abinda Nenne ke cewa, cikin kuka Nenne tace "Ban ta
a ganin er da burinta taga ubanta a walakance ba, kun ga ai ta dawo taga yanda za ayi da uban nata ko furson din za a mayar da shi ko hukuncin rataya za a yanke masa, ni dai na shiga uku na lalace, Allah ya hada Ali da mata da 'ya yan da basa tausayinsa kuma su za su yi ajalinsa, yanxu in Khaleesat er arziki ce da yace ya saketa ba sai tace babu inda zata je ba tunda bautar Allah take??" Malam Ali ne ya shigo gidan da er taliyar Hausa da ya siyo cikin Bacco bag, Nenne na ganinsa ta rushe da sabon kuka tace "Wallahi ta kashe auren ta dawo taga yanda za su yi da kai Ali" Malam Ali ya tsaya yana kallon Nenne, Nenne na fyace majina tace "Ga ta can dakin uwar a kwance tana jiran taga da wace motar za a zo a kwashe ka, dama wallahi tun da muka je gidan da parida nasan za a samu babban matsala don babu alkhairi a ran Parida, kuma in bata yi hankali ba daga ita har Zahra'un sai dai su koma kasar su, duk wanda baya son kwanciyar hankalin
a na to kwanciyar hankalina ne baya so wallahi" Malam Ali dai ya nemi tabarma ya zauna ya kasa cewa komai, Mama Zubaida tace "Ikon Allah, kuma abinda ya faru kenan ni Zubaida?

Aure wata daya da yan kwanaki amma har an yi saki?

Yanxu zawarawa har biyu garemu a gidan nan kenan?" A fusace Nenne tace "Ta zauna tayi ma uban wa zawarci a gida?

Ai ko taki ko ta so sai naje na ba Awdul hakuri ya maidata dakinta don kaf zuri'armu babu wanda ya ta
a zawarci sai in mutuwa mijin yayi, to ko bakin halinta bai isa ya sa ya korota ba bai shirya ba, Khaleesah ce duk wani mummunan bakar maganar da ya zo bakinta take ya
a ma mutum, ko kuma in ka gaya mata abinda bai gamsheta ba tayi maka wani kallon walakanci da kaskanci da tula tulan idanuwanta, wani lkcn kana mata magana tayi maka banza wannan duk mun san halinta ne ba wai sharri ba, ga nukurci kamar er sarkin kutare, to ai ba ko wani namiji bane zai dau wannan, don haka zan je in basa hakuri ya dubi girman Allah ya maidata dakinta..." Mama Shatu tace "Toh ko samun sa kika yi ai sai yayi niyya zai maidata Nenne, in zai iya ai bazai fara sakin ta ba" Wani zagi Nenne ta kundumo mata a fusace, dai dai nan aka rafka sallama a kofar gida, Malam Ali ya mike tsaye yana kallon hanyar fita gidan, Nenne tayi tsit zufa na keto mata, can ta fara kuka a hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Zahra'u dai bata zo mana pamily da alkhairi ba, kun ga har an zo tafiya da shi" Mama Zubaida ce ta yafa gyale ta nufi hanyar fita daga compound din, wani mota taga anyi parking a kofar gidan, mutumin dake tsaye kusa da motan ya nufota yana kallonta, Mama Zubaida ta gaishesa har da risinawarta, ya amsa yace "Mai gidan na ciki kuwa?" Mama Zubaida tace "To Allah ya sa dai lafiya Malam" Mutumin yace "Eh to, ni Dreban Alhaji Musa ne, an bani sako ne in kawo ma mai gidan" Mama Zubaida tace "To ni mai dakinsa ce, ni ce uwar gidansa, ko zan iya karba in mika masa, don baya jin dadi ne" Mutumin yace "To ba damuwa" Hannu yasa a aljihu ya ciro Envelope ya mika mata, ta amsa yayi mata sallama ya koma zai shiga mota, Mama Zubaida ta koma gidan tana juya takardan ita kanta sai da gabanta ya fadi don irin wannan in an kawo ai sammaci yake nufi, Nenne na ganin Envelope din hannun Mama Zubaida ta rushe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, shi kenan Ali a haka zai kare kenan ni Zainabu? wani takardan kotun aka sake kawo masa kenan?" Malam Ali ya amshi Envelope din hannun Mama Zubaida ya yage ya ciro takardan ciki ya warware, "Ni Abdallah Musa, na saki er ku Hauwa saki daya, biyu, uku" content din dake jikin takardan kenan, Shatu ta amshi takardan hannunsa tun da tayi karatun primary, tana duba takardan ta karanto abinda ke jiki amma fa da kyar tana in ina, Nenne ta tsaida kukan da take bayan taji Shatu ta karanto rubutun jikin takardan tace "Ji tsinanne la'ananne matsiyaci? saki har uku kamar warce ta kashe ubansa ko uwarsa?

To Allah Ubangiji ya tsine masa albarka, dama banda kaddara uban me Khaleesat zata ci da
an barawon Gwamnati? ubansa barawon gwamnati shi kuma
an daba, Ai mu wannan sakin abun farin ciki ne a gare mu gaba daya tunda ba na'am muka yi da auren ba, kuma ko yau Khaleesat ta fita sai ta samu mijin nuna ma tsara da ya fi sa komai wallahi, bakin cikinmu daya zawara da ya maida ta, dama kullum da fargaban aurenta da shegen nake don har raina bana son sa babu yanda na iya ne kawai, banda jarabawa wasu iyayen kwarai ne za su dau er su su ba tsinanne irin Awdul?

Khaleesah sai dai kawai tayi hakuri don cuta kam Ali ya cuceta, ya cuci Rayuwarta, don duk shi ya ja mata wannan masifa, da suka ce maka er ka suke so bayan an fito da kai furson in kai uba na gari ne sai ka cije kace sam baka yarda ba sai dai a maida ka furson din ka mutu a can, amma saboda tsoron azaban duniya ba na lahira ba ka zabi ka sadaukar da erka don samu encin kanka, to gashi nan bayan ya rabata da budurcinta ya sako mana ita, dama auren sha'awa kawai yayi da ita, Allah ya isa bamu yafe masa ba wallahi" Nenne na kai wa nan ta fashe da kuka ta jawo kujera er tsugunno ta zauna tana rera kuka sai kuma tace "To yanxu ko zuwa za muyi mu basu hakuri ya dubi girman Allah ya maidata tunda malamai sun ce saki uku a madadin daya yake" Wajen karfe goma na dare Aunty Farida ta zauna gefen Khaleesat dake zaune da cup din kunun da Umma ta dama mata tunda ta kasa cin abinci, Aunty Farida tace "Baki shanye kunun bane?" Khaleesat ta dau cup din ta ci gaba da shan kunun a hankali, Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba tana kallon buhun abubuwan da ita da Umma suka hada zata kai ma Khaleesat gobe, don da gobe zata je wajenta, tun daga dakakken yaji, kubewa busasshe, kuka, kanwa, su citta da kanumfari, gyadar miyar, har da garin danwake da sauran abubuwa da yawa duk su ne a cikin buhun, ga turaren wuta da suka siya mata masu kyau, Aunty Farida ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat da ta kasa shanye kunun hannunta,
a hankali ta jawota jikinta, soothingly tace "Kiyi hakuri Daughter, Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, kar ki saka komai a ranki kin ji?" Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida bata sake ce mata komai ba don ita bata ma son ta tambayi abinda ya hadasu don mayar da maganar bacin rai kawai zai kara masu, Ita dai Umma na zaune kan darduma Islam na bacci a jikinta, Maman Salame ce tayi sallama ta shigo dakin tana kallon Umma tace "Wani labari ne wannan nake ji a garin nan Zahra'u?" Umma dai tayi shiru tana kallonta, Maman Salame ta zauna kan tabarma tana kallon Aunty Farida da Khaleesat dake gefenta tace "Farida" Aunty Farida ta
an yi murmushi tace "Ina yini Maman Salame" Maman Salame tace "Wai da gaske ne?

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Farida tace "A ina kika ji Maman Salame?" Maman Salame tace "Ga labari nan ya baza Mariri?
Chapter 109 · 0% Book details