← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 218

Sashe 198

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bayan minti arba'in suka dawo Jay ya sake kiranta ta fito, Shopping yayi mata na abubuwan da zata bukata irin pack din bottle water, drinks, costly cookies,, Sae gwangwanin powdered milk da Milo with sugar, da carton din Indomie, bread ma manya uku ya siya da Butter, a gefe kuma ga kwai, duk dai wani abu da zai sa ta zama comfortable a gidan duk da bai san kwanaki nawa zasu yi ba, sannan ya siya ne not for only her to use, ya kuma siya masu abinci a restaurant pack biyar da gasassun kaji, Ita dai Khaleesat na jingine jikin motar ta ma rasa abinda zata ce har yara suka gama shiga gidan da kayayyakin, ya mika mata ledan drugs din yace "You check the prescription idan kin ci abinci sai ki sha" Cikin sanyin murya tace "Thank you so much, Allah ya saka da alkhairi" Ya wani kalleta, ita ma dai kallonsa kawai take
an tsayuwar nan da tayi har ta gaji, yayi kasa da murya yace "Pls Halysaah in sha Allah komai zai wuce ki dena saka ma kanki damuwa, i am assuring you babu abinda ya isa ya maki don ya gama samun nasara kuma a kanki, ki kwantar da hankalin ki and trust my words"
an murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace "Go get some rest, ki ce da Kaka in sha Allah za mu dawo gobe yanxu Magrib ya gabato shi yasa baza mu shiga mu gaisheta ba, from our place to here is almost 45 minutes ride" Khaleesat ta
an bude ido cikin sanyin murya tace "Da nisa ashe" Ya
an yi murmushi yace "May be mu zo around 11 in the morning gobe" Tace "To Allah ya kai mu" Yace "Ameen, in kin ji zaki Iya magana anjima ki kirani, bana son in kira kina bacci kaka ta tashe ki" Tana murmushi ta gyada masa kai sannan ta
aga masa hannu alamar Bye bye ta juya ta wuce cikin gidan, Jay ya shiga mota yana kallon Ajay yace "Common ya jiki baza ka iya yi mata ba alhalin idan ita ce sai ta maka ya jiki ko baza ka amsa ba" Ajay ya kallesa yace "Dama bata da lafiya ne?" Banza Jay yayi masa don shi ne ma ya hado mata maganin a Pharmacy shi kuma ya shiga yayi shopping wanda duk da Atm card din Ajay din suka yi duk siyayyar don shi ya mance nasa a gida amma yake masa tambayar rainin wayo yanxu.....

Washegari karfe takwas da rabi Jay ya kira wayar Khaleesat, Nenne dake ta tambayar wanene bayan Aunty Farida ta sanar mata Jay ne tace "
aga ki bani shi" Aunty Farida tace "Ki ce masa me, bari dai in daga tunda bacci take" A fusace Nenne tace "Ki bani nace, ke komai sai kin nuna iyawa" Aunty Farida ta kyabe baki tayi picking call din ta mika mata, Nenne ta doka sallama tace "Ina kwana Ahamad" Jay na jin muryarta ya gaisheta cikin ladabi, ta amsa tace "Wallahi in gaya maka jiya dai ba mu yi baccin kirki ba, jikin nata ba dadi, dama tana dadewa ita bata yi ciwo ba amma in ta tashi yi ba kyau, da ta sha magungunan kamar zazzabin ya sauka sai kuma ya dawo da karfinsa, dama jiya muna mota zuwa garin nan sau biyu tayi amai, to daren jiya ma tayi sau biyu, gashi taki cin komai har shayi an
ada mata ta kasa sha" Jay dake ta sauraronta duk sai yaji a hankalinsa ya tashi, a hankali yace "Toh ina ga za a hada mata da allurai Kaka..." Nenne tace "Atoh, ni na rasa kan ciwon nata..." Yace "Yanxu za mu taho in sha Allah" Nenne tace "Toh Allah ya kawo ka lafiya Ahamad" Bayan Nenne taji shiru alamar ya katse wayar ta ajiye tana kallon Aunty Murja tace "Lafiyan Allah take da, daga sanda iyayen tsinannen yaron can Awdul suka turo barayin gwamnati da daddare wajen Ali shikenan ta birkice, ba komai ne ya ja mata wannan ciwo ba sai damuwa, ta saka ma ranta damuwar abun sosai ba kadan ba, ba dole ta damu ba tunda ita tasan ukuban da ta sha gidan Awdul don bai da kunya ya kuma dawowa yace ga zance ga magana, in sha Allahu karshensa ne ya zo, in ma yana da mugun nufi ne a kanta to ga dai ta a Bauchi bazai kuma ta
a sanin inda take ba" Aunty Murja ta sauke ajiyar zuciya tace "Abun kam babu dadi, Kuma Allah ya fi sa, babu abinda ya isa ya mata wanda Allah bai yi mata ba" Nenne tace "Maza ku tashi ku tsaftace tsakar gidan can, banda ke ma ai sai dai gidan nan ya ru
e don na lura kishiyarki akwai aukin kazanta, yarinyar can taki kuma ki kulleta a daki ki saka kwado kar ta kunyata mu idan bakinmu sun iso...." Aunty Murja dai tayi murmushi ta tashi ta fita.
Chapter 198 · 0% Book details