← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 218

Sashe 194

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe goma saura na daren Khaleesat ta shigo parlon Babanta tare da Aunty Farida, Umma ma na zaune parlon sai Nenne, Nenne ta gyara zama tace "To yanxu Ali ko don wannan girmama ka da yan unguwan nan suka yi suka shigo har gidan nan suka zazzauna a tabarma suna gabatar maka da kansu ya kamata ka rufa mana asiri kar ka sake zama bakin gate kamar Mai gadi, baka ji dadin da naji ba wallahi ganinka a tsakankanin manyan mutane a tsakar gida" Malam Ali dai kallonta kawai yake, can yace "Yanxu Baaba wa yace maki yan unguwan nan ne?" Nenne ta saki baki tace "Ba yan unguwan nan bane?

To yan unguwan dake gaba da namu ne ko wanda ke bayan namu?" Malam Ali yace "Ni ba
in da suka zo gidan nan bama su da alaka da unguwan nan gaba dayan ta" Nenne ta zaro ido tana kallonsa tace "Kai haba dai?

To a ina ka samo su Ali?

Su waye?" Malam Ali ya sauke ajiyar zuciya yace "Dalilin tara ku a nan da nayi kenan Baaba, duk za ku ji waye su da kuma me ya kawo su gidan nan" Nenne ta gwalo ido tace "Wani laifin kuma ka sake yi Ali?

Mun shiga uku mun lalace, abun arziki bai amshe mu ba, ko kwace gidan suka yi?" Malam Ali ya kara sauke wata ajiyar zuciyar cikin nutsuwa ya fara koro masu bayanin su waye mutanen da suka zo da kuma dalilin zuwan nasu gidan, tunda ya fara magana Khaleesat ke kallonsa babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, haka ma Umma da Aunty Farida that look speechless, Sai da Nenne ta jira ya kai har karshe sannan tayi mitsi mitsi da ido tace "Amma ka ban mamaki kuma ka ban tsoro da baka masu koran kare ba Ali, anya kuwa ba a canza min kai a daki na je wankan jegon ka a ban
aki ba kuwa tunda gidan yawa ne kuma mu uku muka haihu ba wani tazara tsakaninmu???

Ali yanxu kana nufin baka kore su ba ka zauna ka sauraresu har karshe?" Malam Ali yace "In kore su kuma Baaba?

Na fa gaya maki su wa da su wa suka zo, ta yaya zan koresu fisabililahi?" Nenne ta mike a fusace tace "To ina ruwana da koma su waye, kai ko shugaban kasa ne in ya gaya maka abinda bai gamshe ka ba ai zaka kama kanka balle ma ba shi bane, yanxu a takaice kana nufin ce masu kayi toh shikenan?" Malam Ali yace "A'a, ni ban ce masu haka ba Baaba...." Nenne tace "Amma daga Awdul din har iyayensa Allah Ubangiji ya tsine masu albarka daga su har wanda ya basu shawaran turo maka manyan mutane su baka hakuri, kai kuma da yake gantalalle ne kai baka san ciwon er ka ba maimakon kace masu ai an sa mata rana biki saura sati daya yanxu haka shine ka zauna da wata safarka a kafa kamar
an bigilantee a tsakankaninsu kana sauraronsa, to wallahi idan ban kai karar su kotu ba Allah ya tsine min, ko Awdul ne ka
ai namiji da ya rage a duniya idan na kara basa auren jikata a kirani tsohuwar banza tsohuwar hofi, haba fisabililahi, sannan shi yaron nan da ya siya mana gidan nan kanin ubanmu ne shi ko na uwarmu da zai siya mana katon gida haka idan har ba sonta da aure yake ba, sai ya fito ya gaya mana yana sonta mu wani irin
walwa gare mu da baza mu gane ba? ai ni ba yarinya bace nasan abinda nake, wallahi sonta yake so kuma na aure, haka kawai ka biye barayin gwamnati su saka ka a tsakiya don su tsorata ka ka sake daukar er ka ka bada a karo na biyu?

Ko dai baka da lafiya ne Ali?" Malam Ali dake ta kallonta cikin nutsuwa yace "Yanxu fa Baaba baki saurareni na kai karshen bayani na ba...." A fusace tace "To ina jin ka maza maza tafi karshe" Malam Ali yace "Ni nace masu bazan ma Jiddah dole ba, duk abinda take so shi zan mata kuma shi nake so, in ma shi Abdul din tace take son komawa ni bazan hanata ba sai dai in bi ta da fatan alkhairi, in kuwa tace bata so to hakan ya zauna don bazan mata auren dole a karo na biyu ba" Nenne tace "To maza tun basu yi nisa sun isa gida ba ka bi su kace ai babu wannan zancen ko makamancin sa, yarinya tace bata sonsa ta tsanesa, in kuma wannan karan da karfin mulki za su yi amfani da shi wajen auren nata kamar yanda suka yi da kudi watannin baya to sai su yi mu gani, maza su gaya ma
an su ya cire shegun idonsa akan Khaleesah bata sonsa kuma tafi karfinsa nesa ba kusa ba wallahi" Hawaye ne kawai ke zuba idon Khaleesat tana shessheka tana jin wani zafi a ranta, ta jinginar da kanta jikin Aunty Farida cause she is beginning to loose her control, Sosai Aunty Farida ke jin dadin maganganun Nenne don ita ma banda tafarfasa babu abinda zuciyarta yake a inda take zaune, Umma kuwa dafe kanta da yayi mata nauyi sosai tayi, Nenne tace "Ka ji me nace maka ko baka ji ba Ali??

Tun gari bai waye ba ka san yanda zaka yi ka sanar masu babu wannan maganar da suka zo da shi don har an saka ma Khaleesah rana da wanda take so kuma ranan jama'ar nan daurin aure" Malam Ali yace "Shikenan Baaba, su a yanda suka zo ma suna tunanin bayan sun gabatar da bukatarsu nauyin su da ganin girmansu zai sa in amince lokaci guda babu ja in ja, amma wallahi ban yi haka ba, nuna masu nayi ni bani da ta cewa sai abinda 'ya ta tace shine magana don bazan kara mata dole ba, yanxu zuwa gobe suna saurarata su ji ya ake ciki, don haka bazan boye masu komai ba in sha Allah, zance su yi hakuri nayi mata miji" A fusace Nenne ta nufi kofa tana cewa "In Alhaji Musa bai yi hankali ba zan taka har gidan nasa in ci masa mutunci wallahi, tun da saboda shegen
an sa aka halitto Khaleesah ba sai ya zo ya sake daura auren ba mu gani, wato ya zo maka da manyan mutanen garin nan yanda zaka yi masu biyayya ga ka
an banza ko?

To mu zuba da su" Tana kai wa nan ta fice daga parlon, Umma ma ta mike ta bi bayanta don bakin ciki ma bazai bari tace komai ba, shi dai Malam Ali kallon Khaleesat kawai yake, a hankali yace "Kiyi hakuri Jiddah, babu me maki dole in sha Allah, ki kwantar da hankalinki" Ita dai Khaleesat hawaye kawai take ta kasa cewa komai, Aunty Farida tace "Amma Malam tun farko bai kamata ma ka zauna ka ci gaba da sauraransu ba bayan kaji dalilin zuwan su, kamar yanda Nenne tace da kawai sai kace masu ai an saka mata rana kawai" Malam Ali yace "To tunanin nan bai zo min ba wallahi, amma ba komai in sha Allahu zan kira na kusa da Deputy din gobe in gaya masa yanda ake ciki don ya bani numbersa suna sauraran kirana gobe" Aunty Farida tace "Allah ya kyauta" Mikewa tayi ta dago Khaleesat suka fita daga parlon.

Daren ranan nan Khaleesat kasa baccin kirki tayi, she was so disturb, ta rasa menene zai sa Abdul ya hakura da ita ya cire ransa a kanta cikin ruwan sanyi babu tashin hankali, dama kullum a ranta tana jin ba fa hakura yayi ba, he is definitely coming back amma bata san ta wannan salon zai sake dawowa ba, ko kadan bata yi mamakin gano sabon gidan nasu da suka yi ba ba don ko dubu biyu suka ba wani a Mariri tsaf zai kawo su tunda kusan kowa yasan inda suka dawo yanxu, sai kusan karfe hudu da rabi ta tashi daga saman darduman da take zaune bayan ta idar da sallolin da tayi sannan ta kwanta....

Da asuba bayan ta idar da Sallah tayi azkar ta tafi dakin Umma ta gaisheta, Umma dake zaune kan darduma har lokacin ta dinga kallonta don tana ganin idanuwanta ta gane bata yi bacci ba daren jiya kuma tayi kuka, Khaleesat ta zauna kusa da ita ta gaisheta cikin sanyin murya, Umma ta jawo ta jikinta a hankali tace "Bana son ki tada hankalin ki Khaleesah, in sha Allahu babu wani abu da zai sake hadaki da Abdul ina nan ina maki addu'a kema ki dage da addu'a kinji?" Hawaye ya cika idon Khaleesat ta gyada ma Umma kai kawai...

Aunty Farida na zaune dakin Nenne tana kallonta tana ta koro mata jawabi, Nenne ta kare jawabinta da cewa "Don haka kema ki hada kayanki kala uku ko hudu zuwa nan da gobe mu kama hanya kawai, sam ban ga ta zama ba wallahi Parida, dole ko nawa ne in bada a min addu'a a dauke hankalin tsinannen yaron nan akan jikata ya rabu da ita na har abada, zuwa anjima kuma ki kira min Murja in sanar mata gamu nan zuwa Bauchi gobe, dama ina ta cewa zan je kwanan nan to ga babban dalili zai kai ni yanxu, ke ina ga ma har da Khaleesar za mu tafi don gwara mu je da ita aga warce za ayi ma addu'a ido da ido, in akwai wani taimako da za a bata tayi amfani da shi sai a bata in tsareta tayi, banda Ali
an banza ne da wani idon yake son mu kalli yaron nan dake ta mata hidima saboda soyayya, ai sonta yake Ahamad din, to kanin ubanmu ne shi zai mallaka mana kantamemen gidan nan haka babu dalili?
Chapter 194 · 0% Book details