← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 218

Sashe 201

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 7 min read

And he found out everything, when I say everything I mean Everything Ajay" Ajay ya
an bude ido ya ajiye laptop dinsa yace "Really?" Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Dama ai zancen duniya baya buya, but banyi expecting za a gano komai easily haka ba, yau na kara jin tsoron mutum, mutum abun tsoro ne Ajay, nasan har gidan da na siya Abba ya sani yanxu, he was angry but calm at the same time, I wish I told him all this before he find out himself..." Ajay was quiet for some time don shi ma ya girgiza, can yace "To yanxu me yace maka at the end?" A hankali Jay yace "He said it's fine, I told him about her Grandma da tace zata zo, gobe kenan...." Ajay yace "Ba nace ka kyale wannan tsohuwar ba, sai ta zo ta karasa fada masa abinda ba a fada ba a Kanon hankalin ka zai kwanta, she talks too much shi yasa nace kayi ignoring kawota da tace kayi gidan nan, but you still went ahead and told Abba" Jay ya sauke wani ajiyar zuciyan yace "Bazata yi abinda kake tunani ba, i will bring her tomorrow in sha Allah, don Abba na contemplating asalin Baban Halysaah, an ce masa Kano aka dawo kuma aka ce Bauchi" Sosai Nenne ta nutsu tayi zaman ladabi da biyayya tun da aka shigo da ita babban parlon Mai martaba, don a iya saninta ba kowa ne ke da access din parlon sarki ba, ita a ganinta ba karamin karramata da mutunta ta aka yi ba haka, dama ta baza tsadadden turaren Khaleesat da suka barota a gida, sai zuba uban kamshi take abun ta ga sabon gyale da atamfa a jikinta kai baza ka bata shekarunta ba, zuwa sannan sun kusa minti goma kenan a parlon a zaune, Ajay ne yayi leading dinsu zuwa parlon sannan ya fita, Nenne ta saci kallon Aunty Farida da tayi picking call din da ya shigo wayarta ta hade rai tace "Ke Parida ba nace ki ajiye wayar nan ba, ba fa parlon gidanmu bane nan, ba fa kowa ake ma iso zuwa wannan parlon ba sai wanda ya isa, wannan wani irin kunyata ni kike son yi bayan na yarda dake na jajibo ki, Haba parida..." Ko rufe baki Nenne bata yi ba sai ga Mai martaba ya shigo parlon walking like the king he is, Nenne ta sinne kai irin babban mutum ya shigo, Sau daya Aunty Farida ta daga kai bayan ta gansa ta ajiye wayar hannunta, ya karaso har cikin parlon ya zauna a spot din da ya saba zama yana kallonsu, tuni dama Nenne ta fara jero masa gaisuwa tun bai kai ga zama ba, shi ma ya gaisheta cikin girmamawa, Aunty Farida ma ta
aga karamin Nikab din da ta dora kan Abayan jikinta ta gaishesa kanta a kasa, ya kalleta ya amsa sannan ya kalli Nenne yace "Kun zo lafiya Baaba" Nenne tace "Wallahi lafiya lau ranka shi dade, na ce ni dai yau a kawo ni in gaishe ka in sa maka albarka don kai din mutumin kirki ne kowa ya shaida, Allah Ubangiji yayi maka albarka ya kare gaban ka da bayan ka, ya rufa maka asiri duniya da lahira, Allah ya albarkaci zuri'ar ka, ya ja da ranka, ya kara maka lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya taya ka riko..." Ya gyada kai with calmness yace "Ameen Baaba, Ameen, dama albarkan irin ku abun so ne gare mu, muna godiya kwarai, Allah ya kara girma, madallah" Nenne tace "Ni dai nayi farin ciki da ganin ka, nace duk yanda za ayi yau dai a kawo ni wajen sarki mu gaisa, shi ne na saka Parida kanwar surkata ta rakoni muka taho tare" Mai martaba yace "Madallah, ai ba a jima ba aka kirani ake sanar min wakilan da na tura sun isa can gidan Alhaji Aliyu, kuma anyi komai lafiya har an tsaida lokaci ban san ko sun sanar maki daga Kanon ba" Nenne da ta bude ido sosai tana sauraron abinda Sarki ke cewa tayi kasa da murya tace "Wallahi ba a sanar min ba, kilan Aliyun zai ce a jira in dawo kafin a sanar min, amma nayi farin ciki da wannan abun arziki haka, ai hada zuri'a da kai Mai martaba abun alfahari ne abun farin ciki ne, nayi murna sosai, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi..." Maganar da Umma ta kira Aunty Farida zata yi mata kenan kafin shigowar Mai martaba da Nenne ke tayi mata bala'i, Aunty Farida ta dade bata ji farin ciki irin na wannan lokaci ba, she is finding it hard to believe it, yanxu har an aika neman auren Khaleesah kenan amma ko da wasa daga Jay har Ajay babu wanda yace masu komai all this while, kuma kullum sai sun je can gidan Aunty Murja, Nenne ta nuna masa Aunty Farida tace "Kanwar uwar yarinyar kenan uwar su daya uban su daya, ita kanta bata sani ba banda yanxu da muke ji tare..." Sarki ya jinjina kai yana kallon Aunty Farida yace "To Madallah, ke ya sunan ki..." Nenne ta gyara zama tace "Parida, sunanta Parida Isuhu, tun tana er shekara goma Aliyu ya daukota daga gaban iyayenta a Nijar ya kawota gaban yayarta wato uwar wannan jikar tawa da aka je neman aurenta yau, to Ali ne yayi mata auren fari aka zo zaman babu dadi kuma gashi abokinsa ne mutumin saboda ya yarda da shi ya basa ita ga manema kaca kaca ya hanasu, to daga karshe dai da kansa ya amso mata takardarta ya raba auren ganin tana cutuwa gashi ita ba me baki bane sai dai kuka, to tun sannan har yau tana gaban Ali, duk wanda ya zo neman aurenta sai taki basa hadin kai yau shekara bakwai kenan, duk bayan wasu shekaru za su shirya su je gaida iyayensu ita da yayarta a Nijar, iyayen nasu buzaye ne mutanen kirki wallahi, aure me hada mutanen arziki ga shi ya hada zumunci tsakanin Nijar da Najeriya" Mai martaba yace "Wannan gaskiya ne Baaba" Nenne tace "To tun da har mun samu ganin ka har mun gaisa, to ina ga mu za mu zo mu koma Ranka shi dade kar mu shiga lokacin ka" Mai martaba yace "A'a, ku bari a karasa da ku bangaren fulani ku samu ku ci wani abun kafin ku tafi Baaba, bazai yiwu ku tafi baku sha ko ruwa ba a masarautar nan..." Nenne zata yi declining offer din nasa sai ga kanwar Aunty ta shigo parlon da sallama tana rike da bowl din fresh fruits, tare da Auntyn suke amma ita tana can baya tana tafe tana waya don wani lkcn in har Aunty zata kawo ma Mai martaba abun ci ko sha kanwarta ke rike mata har zuwa parlonsa in ta ajiye sai ta fita, Sarki na kallon Zuwaira yace "Ki shiga da ba
in nan cikin gida Zuwaira, ayi masu duk abinda ya kamata" Zuwaira ta kalli Nenne sai kuma ta kalli Aunty Farida dake kallon direction daban hakan yasa bata ga fuskarta da kyau ba kawai dai tasan fara ce kamar za a latsa ta jini ya fito, kallon Mai martaba tayi da ladabi tace "To ranka shi dade" Ta kalli Nenne ta gaisheta a takaice sannan tace "Mu je" Nenne ta mike bayan ta amsa gaisuwanta, Aunty Farida ta sauke Nikab dinta sannan ta tashi ita ma, hada ido suka yi da Mai martaba, tayi masa sallama ta bi bayan Nenne dake biye da Zuwaira, sun fita daga parlon kenan sai ga Aunty cikin shiga ta alfarma ta sha gwala-gwalai tana ta
u dai dai, daga sama har kasa take kallon Nenne da Aunty Farida dake sanye da Nikab, Aunty ta kalli Zuwaira tana yatsine fuska tace "Su waye wannan kuma Zuwaira?" Zuwaira ta ta
e baki tace "Oho, Mai martaba ne yace in shiga da su cikin gida, a parlonsa na same su" Nenne ta kwantar da murya tace "Ina wuni Pulani, ba
i ne daga Gombe...." Ko amsa gaisuwan Nenne Aunty bata yi ba ta shiga parlon Mai martaba, Zuwaira tana kallonsu a walakance tace "Mu je don Allah ina da abinda zan yi ni kam...." Bata jira cewarsu ba ta ci gaba da tafiyarta, Nenne ta kalli Aunty Farida, sai da taga Zuwaira tayi nisa sannan tayi kasa da murya tace "Parida kira mana Ahamad kice mun gana da Sarki ya fito ya maida mu gida" Ko Nenne bata ce haka ba dama Aunty Farida bata yi niyyar bin Zuwaira ba, haka nan suka canza hanyar da zai sada su da Compound Aunty Farida na kokarin kiran Ajay ta wayarta...

Aunty na shiga parlon Mai martaba tana kallonsa tace "Ranka shi dade, wasu ba
i ne wannan aka kawo su har cikin parlon ka?
Chapter 201 · 0% Book details