← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 218

Sashe 116

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sannan nace duk sanda na samu kudi zan nema mata Jami'ar garin nan tayi, ba wasu shekaru gareta ba balle ace lokaci zai kure mata" Nenne ta kallesa da sauri tace "A gidan uban wa zaka samu kudin?

Mutanen garin in sun fasa fadin abinda za su fada a kanka Allah ya tsine masu albarka, kai bari kaji Ali bana bukatar ra'ayinka ko shawararka a yanxu saboda kai ma sanda ka bi ra'ayinka ka yarje ma Awdul ya kai ta kasar waje babu wanda ka saurara ko kaji shawaransa, don haka ni ma yanzu wallahi bazan saurare ka ba Amurka ne sai Khaleesat ta koma ta karasa abinda ta fara in sha Allahu, in kuma nuna ma duniya zaka yi ni er banza ce a gareka to Bismillah" Kofar gida kawai Malam Ali ya fita da butansa a hannu, Nenne ta kalli Khaleesat tace "Maza ki hada akwatinki ki tsaya cikin shiri, in sun biya maki kudin jirgin ki kama gabanki kije kiyi abinda zai taimaki rayuwarki, zama gidan nan kadai ya ishi mutum ya fada cikin mummunan damuwa, gida kamar na 'yan sansanin gudun hijira, ga lafta laftan mata suna yawo suna doyi a cikinsa, ai ko mutum matsiyaci ne ya kasance dai yana da tsaftarsa dai dai gwargwado, amma gidan nan ga talauci ga kazanta, ina bawa zai iya rayuwa a nan idan ba dole ba" Nenne na kai wa nan ta kama hanya tayi tafiyarta, Khaleesat ta daga kai ta kalli Umma da ta bi Nenne da kallo, Mama Shatu ta mike tana kallon Umma tace "Muddin kika ce baza ki bude baki kiyi magana ba to kina ji kina gani za a mayar maki da er ki karuwa Zahra'u, wata birkitacciyar tsohuwa can kamar Nenne ce zata yanke ma er da kika haifa hukuncin abinda ya shafi rayuwarta?

Ita ta tsugunna ta haifar maki er?

Mu meyasa ba a mana iko akan namu yaran ba?

Saboda an san baza mu dauka ba mu ba yan iska bane, to kuwa wallahi Nenne na dab da kai ki ta baro ki, mata me tabin
walwa zaki yarda ta yanke hukunci akan 'er ki? ai in ita Khaleesar ta bude baki tace bazata je ba babu uban da zai tilastata ta je wallahi, waye bai san Nenne da kwadayi da son abun duniya ba kamar tayi sata?" Muryar Nenne suka ji ashe tana makale bata tafi ba tana jiran jin abinda za a ce, Nenne ta dinga kwalo ma Malam Ali kira, sai gashi ya shigo da sauri yana kallonta yace "Lafiya Nenne?

Ai magana ta wuce yanda kika ce haka za ayi" Mama Shatu tayi wuri wuri da ido daga inda take tsaye, Mama Zubaida ta mike ta lallaba ta dau kwandon kwanon wanke wankenta ta shige daki ta sako labule, Nenne ta rushe da matsanancin kuka tana kallon Malam Ali tace "Ali yau sai dai ka zaba ko ni ko Shatu a gidan nan, kawai ka zaba ko ni ko ita, ni Shatu zata kalla ta kira me tabin
walwa wato mahaukaciya er macukule?

Ni zata ce ma me kwadayi da son abun duniya?

Tunda nake me na ta
a zuwa gun almajirin ubanta dake bara a bakin danja nace ya bani?

Me na ta
a rokon uwarta me shanyayyen kafa?

Bata san ina labe ban tafi ba duk ina jin abinda take cewa, cin mutunci da zagi sai wanda ta manta ne bata min ba Ali, har tana gaya ma Zahra'u ni na haifar mata er da zan yanke mata hukunci akan ta?

Me nayi ma Shatu da har zata yi mugayen kalamai haka a kai na?

Naga dai kullum ci gabanka da na iyalan ka shi ne burina, fadi tashi babu wanda bana yi akan kai da iyalinka, amma daga karshe sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, tsofe tsofe da ni Shatu tace min me son abun duniya?" Kuka sosai Nenne take tana share idonta da gyalen jikinta, Malam Ali na kallon Mama Shatu da tayi tsuru tsuru yace "Shatu ki tafi gida, sai na neme ki" Mama Shatu ta gwalo ido tace "Ban gane in tafi gida ba Malam, wani gidan zan tafi?" Malam Ali yace "Gidan iyayenki, ki je na sake ki" Mama Shatu ta zabura tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ka sake ni fa kace Malam, na shiga uku na lalace" Labibah ta mike tana huci tace "Gaskiya Baba sai dai mu bi Baabarmu mu ma" Nenne tace "Shegiya ku bi ta mana, yunwar cikin ku kadai ma ya isheku ai" Malam Ali na kallon Mama Shatu dake rusa kuka yace "Kar in dawo in sameki a gidan nan" Daga haka ya fice daga gidan, Nenne ta bi bayansa tana goge idonta ita ma ta fita, sai a sannan Mama Zubaida ta fito tana salati tana kallon Mama Shatu dake kuka wiwi, Umma tsabar yanda jikinta yayi sanyi ta ma kasa cewa komai daga inda take zaune, Mama Zubaida na kallon Umma tace "Ke kam kinyi asara wallahi Zahra'u, ko wani bala'i ta dalilin ke da tsinannun 'ya yan ki yake faruwa a gidan nan, gashi yau saboda ke da er ki an saki Shatu, sam babu alkhairi a tare dake da zuri'ar ki Zahra'u" Umma ta juya tana kallon Mama Zubaida sai dai bata ce komai ba, Khaleesat ma ta daga kai tana kallonta, Mama Shatu na kuka sosai tace "Kuma in sha Allahu asirin da kike yi zai kare maki a gidan nan Zahra'u, yanda kika yi sanadiyyar tsinkewar igiyar aurena daya ke da er ki wallahi sai nayi sanadin naki igiyar kema, ko tsirara zan yi yawo kuwa, Ni saki daya aka min ke ukun gaba daya za a maki, kuma kamar Ali ya maida ni ne don yanxu na fara auren sa wallahi" Don mamaki Umma ta ma rasa abun ce masu ganin yanda suka juya zancen lokaci daya, yau ga fadan karfin hali tana gani kiri kiri, biyesu ma bata lokaci ne kawai a wajenta ga makota na jin su, tsam ta mike tayi shigewarta daki, Khaleesat ta mike ta bi bayanta.

Washegari da sassafe Umma da Aunty Farida suka fito tsakar gida suka tarar da Mama Zubaida da Mama Shatu a tsaye suna jiran fitowarsu za a je ba Nenne hakuri, ko wanne da Hijab dinsa har kasa don sanyi ake sosai, duk abinda suka yi ma Umma jiya hakan bai sa tace bazata bi su zuwa gidan Nenne ba, Su ma din sun san ta dalilin Umman sai Nenne ta iya hakura ta sa Malam Ali ya maida Mama Shatu shi yasa Mama Zubaida da kanta ta samu Umma ko kunya babu tayi mata magana wajen karfe biyar din asuba, Mama Shatu dama a makota ta kwana ranan don sae da Nenne ta dawo ta korata har da watsi da en tsummokaran ta, sae kusan hudun asuba Shatu ta dawo gidan daga inda ta kwana, a haka duk suka kama hanya zuwa gidan Nenne da asuban.

Ranan Thursday da safe Khaleesat na zaune dakin Umma tana kallon Aunty Farida dake ta jera mata kayanta da aka amso wajen guga a cikin akwati, ita dai Khaleesat har sannan ta rasa gane me take ji a ranta, farin ciki take ko akasin haka duk ta kasa ganewa, babban damuwarta yanxu bata san da idon da zata kalli Housemate dinta ba idan ta koma America, sannan gani take kamar babban burden kawai zata zame masa a can din tunda ita ba komai gare iyayenta da za su tallafa mata da shi ba idan ta koma,
an kudin dake account dinta ba wani kudin kirki bane kuma da shi ta siya sabon waya with new sim card, sai few abubuwan da tasan zata bukata a can kasar, sauran kudin dake account dinta ko dubu dari da hamsin bai karasa ba, duk wannan tunanin yasa take damuwa sosai a ranta, Aunty Farida ta daga kai tana kallonta kafin ta rufe zip din jakar tace "Baki manta komai ba dai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Aunty Farida tace "A Airport din za ku hadu da Safiyyah goben?" A hankali Khaleesat tace "Eh" Aunty Farida ta kulle zip din tace "Gwara ki saki ranki kiyi abinda ke gaban ki Khaleesat, ki cire duk wani damuwar dake ranki kar ki je ki samu matsala a karatun ki, shi kuma Jawwad Allah ya saka masa da mafificin alkhairi...." Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, Aunty Farida ta mike ta dauko daya akwatin don hada few foodstuffs din da suka siyo mata da Umma wanda zata iya shiga Amurka da shi, a hankali Khaleesat tace "Toh Aunty ta yaya za a maida masa kudinsa dake account dina?" Aunty Farida ta daga kai ta kalleta, can tace "Kudin wa?
Chapter 116 · 0% Book details