← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 202 OF 218

Sashe 202

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma ni ban ta
a ganinsu ba alamar babu abinda aka hada da su, ita dayar Nikab ma ta saka balle in ga fuskarta, su waye ne su da za su shigo har wannan parlon bayan ga can inda ake sauke ba
i?" Calmly Mai martaba yace "Ina ce kin gaisa da su ai?" Aunty ta
an hade rai tace "Eh, wai daga Gombe suke in ji tsohuwar" Mai martaba yace "To haka ne" Mikewa yayi yace "An sanar min ina da ba
i a fada yanxu, zan je in same su Fulani"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
07087865788
Bear with me pls, I am not well
HALYSAAH 94
Calmly Ajay ke driving bayan sun baro masarautar, yana ta sauraron Nenne da tun fitowar su take fadin irin kirkin Mai martaba tana sa masa albarka, shi dai ba abinda yace don kawai gani yake ba a tare su da kyau ba, yasan dai Abbansa zai sake masu kamar yanda ya saba yi ma kowa amma mutanen cikin masarautar will never do so, ita dai Aunty Farida hankalinta na kan wayarta, Sai duk yaji bai ji dadi ba don ya fahimci ko ruwa basu sha ba balle har a basu wani abinci, ko da gangan Aunty zata iya hanasu barin ace ta samu labarin shi ya kawo su gidan, Nenne tace "Toh wai Ina Ahamad din, ko a masarautar ma fa bamu gansa ba" Sai a sannan Ajay yace "Ya je ajiye Baabarsa unguwa" Nenne tace "Allah sarki, iya sarki kawai mu ka samu muka gaisa da, kai ma kaga ko Baabar ka bamu gani ba" Ya
an yi shiru, sai kuma yace "Ni Mahaifiyata ta rasu" Nenne tace "Allahu Akbar, Allah sarki, Allah ya ji
an ta, ya gafarta mata, to ko dai kishiyar baabar taka muka gani za mu fito parlon Mai martaba, wata tana nan ita ba fara ba, sannan tana
an da narkeken jiki ba can can ba, tana da matsakaicin tsayi" Ajay yace "Eh..." Nenne tace "Amma dai bata da kirki kwata kwata, saura kadan ta walakanta mu in gaya maka" Ajay ya kalli Nenne ta madubi yace "Ta maku magana ne?" Nenne tace "Ina fa, ina gaisheta ko amsawa bata yi ba ta sha gwala-gwalai, ni na zata ma uwarka ce shi yasa na ja bakina nayi shiru ban gaya maka ba" Ajay yayi shiru, kuma bai yi mamaki ba kwata kwata, after a while yace "Ku yi hakuri, yawanci bata son ba
i dama" Nenne tace "To er sarkin wani gari ce take wannan uban girman kan haka da rashin son talakawa?" Ajay ya
an yi murmushi bai dai ce komai ba, sun yi tafiyar kusan minti talatin kiran Mai martaba ya shigo wayarsa, dagawa yayi ya kai kunne tare da sallama, after some seconds yace "Eh muna hanya ne yanxu zan maida su, na zata kun yi sallama ranka shi dade...." After few more seconds ya ajiye wayar ya kalli Nenne yace "Dama baku yi sallama da Sarki ba?" Nenne tace "Cewa yayi a shiga damu a bamu abun sha, da naga ba arziki yasa muka ki bin yarinyar tana nan wata kiti
ir kiti
ir da ita, dama Parida da nasani ba zuwa zata yi ba don bata son rainin wayo" Ajay yace "Ohk, yanxu yake gaya min ai baku yi sallama ba" Nenne tace "Tun da mun gansa ai an wuce wajen kawai, wataran za a sake haduwa in sha Allah" Suna kusa gidan Aunty Murja after 40 Mins ride Ajay ya ajiye wayarsa da yake driving yana dannawa, bayan sun shigo unguwan ya kalli Aunty Farida yace "Mai martaba ya bada sako a baku, na tura a account din Jiddah" Aunty Farida ta
an yi shiru, sai kuma tace "To mun gode Allah ya saka da alkhairi" Nenne tace "Wallahi mu ba don ya bamu komai muka je gaishesa ba, banda shi din babba ne ai da nace kawai a maida masa, amma dai babu laifi, don Allah kayi masa godiya in ka koma gida tunda bamu da wata hanyar yi masa godiya" Ajay yace "In sha Allah" Suna shan kwanan gidansu Aunty Murja, Nenne ta fara hango Khaleesat karkashin bishiyar mangwaro dake gaba da gidan Aunty Murja da dogon sanda a hannunta ita da yaran gidansu Aunty Murja tana tsalle tana plucking Mangwaro, tsohon zanin Aunty Murja ta daura sai er karamar Hijab da slippers a kafarta, Nenne taji kunya ya lullubeta ta rike ha
a tace "Kwance fa muka baro ta sheme sheme daxu ba lafiya, yanxu meye wannan take yi cikin 'ya yan cikinta fisabilillahi?" Khaleesat bata hangosu da wuri ba don da suna shan kwana taga motar zata gudu ta shige gida tun basu karaso ba, sai kawai yara taji suna Nenne Oyoyo bayan sun ga motar, ta juya suka hada ido da Ajay dake kallonta a gaban motar, sai yanxu ya kara tabbatar da ashe yarinya ce er karama sae rashin kunya idan ta samu waje, Tuni Nenne ta sauka daga motar tana kara yi ma Ajay godiya, Khaleesat ta bi bayan Nenne da sauri zata shige cikin gida, Nenne ta hade rai tace "Baki da kai ne, baza ki je ki gaishesa ba tunda kin riga kin kunyata mu, meye hadin ki da bishiyar mangwaro kamar mayya, yanxu da tare muke da Ahamad din shi ma haka zae ganki kamar almajira" Khaleesat ta wani turo baki tace "To haka zan je, ai ba sai na gaishesa ba" Nenne tace "Ina ruwan sa dake idan kin je a hakan?

Wannan ai ba sa'an yin ki bane, kina ganin mutum kamili ga nutsuwa wanda magana ma sai ya ga dama, ai ke Ahamad din shi ne dai dai ke shi zai dau ko wani kalar shirmenki da wauta tunda shi faram faram yake, yanxu banda shirme godai godai dake ki shige cikin yara kina tsalle zaki tsinko Mangwaro da kodadden zanin Murja" Khaleesat tace "Wallahi bazan je ba, ai ba wajena ya zo ba" Nenne tace "Ni zaki kunyata?

Mutumi ya gan ki kice baza kije ki gaishesa ba dubi yanda yayi ta sintirin zuwa unguwan nan da Ahamad suna zuwa duba ki, sannan ya zo yau ya dauke mu ya kai mu har gaban ubansa yau, ni dai ki rufan asiri ki je ki gaishesa, ai babu dadi haka Khaleesah, dama bai ganki bane wannan daban" Khaleesat ta kalli Aunty Farida dake tsaye jikin motar suna magana da Ajay, can ta fara tafiya zuwa wajen, tana isowa Aunty Farida ta wani kalleta sai kuma tayi ma Ajay sallama ta bi bayan Nenne zuwa cikin gida, Khaleesat ta jingina jikin motar tana kallon wani direction daban, dama tun shekaranjiya take jin haushinsa baya ce mata ya jiki duk ciwon da take ta yi, sai dai kawai ya zo yayi ta kallonta, tada motarsa yayi ita dai bata matsa jiki ba kuma bata kallesa ba, taji yace "Baza ki bar nan ba??" Sai a sannan ta juya ta kallesa, yana kallonta da kyau yace "In kika samu waje ba karamar kazama bace ke, i am telling you this for free...." Ita kanta bata san me yasa ta fara dariya ba kamar warce ake yi ma cakulkuli, reverse ya fara yi ta zaro ido ta koma baya tana kallonsa tace "Buge ni kake son yi?" ko kallonta bai yi ba a haka ya juya ya bar unguwan, kallon kanta tayi daga sama har kasa, sai kuma ta ta
e baki tayi wucewarta cikin gida yara na biye da ita da Mango din da suka tsinko...

Da daddare Ajay na zaune parlon Abbansa yana saurarensa kansa a kasa, Mai martaba yace "To amma ku menene dalilin ku na boye min gaskiyar lamarin gaba daya?

Ko kai ka basa shawaran kar ya gaya min gaskiya?

Sannan duk saboda yana son ya aureta ne duk yayi mata wannan hidima?" Ajay yayi kasa da murya yace "Ko daya Abba, need din fadin gaskiyar ne bai yi arising ba sai yanxu ranka shi dade, taimako kuma kai muka yi kwaikwayo don da haka muka san ka, nasan Jawwad duk abinda yayi mata ba yayi mata bane saboda yana sonta da aure at first, he did all what he did for God sake ba don ya aureta ba, tausayinta ne yayi leading har yaji zai aureta, kuma idan ba auren tayi ba tsohon mijinta will keep on hunting her" Mai martaba yace "Kuma duk zuwa biyun da nayi Amurka tare nake ganin ka da yarinyar a maimakon Jawwad din ae" Ajay ya kallesa, sai kuma ya sauke kansa yace "I helped him with some responsibilities too" Mai martaba yace "Then why were you trying to cover that up?

Kace komai shi yayi" Ajay yace "I am not hiding it sir, we were all protecting her from her Ex differently, shi yasa har kake zuwa kake samunta a gidan..." Mai martaba yace "Duk yanda zaka kare kanka you are very good at that Junaid, shi kuma Jawwad always take the Consequences no matter how deep it is for you" Ajay yayi shiru trying to understand what his dad meant, after some seconds Mai martaba yace "Shikenan....

Kai ya batun naka maganar auren?" Ajay yayi shiru bai ce komai ba don shi kansa ya gaji da tsara new excuse kullum, Mai martaba ya
an yi murmushi yace "Karyar taka ta kare kenan?" Ajay dai bai ce komai ba.
Chapter 202 · 0% Book details