← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 218

Sashe 182

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan kusan minti talatin sai ga Nenne ta shigo gidan, cikin dubara Khaleesat ta
an matsa daga kusa da Jay, Nenne ta bude Cooler din tana kirga tuwon ciki tace "Kana nufin guda daya kacal ka ci tuwon?" Jay yayi dariyar da bai yi niyya ba yace "Ai na koshi ne kaka" Bata san tare ma suka ci guda dayan da Khaleesat ba, Nenne tace "Ban ji dadi ba gaskiya, duk tunanina zaka tashi da malmala biyu, ai don kai nayi tuwon wallahi" Khaleesat na murmushi tace "Ba ya cin abinci da yawa fa Nenne" Nenne tace "To wa ya sako da ke, Allah ya sa ma bake kika sa guda dayan a gaba kika ci ba" Jay ya shafa kai yace "A'a Kaka, ni na ci" Nenne ta nemi waje ta zauna tace "To sai a juye maka sauran a leda ka tafi da shi kawai" Shi dai murmushi kawai yake, Nenne tace "Ya labarin innar ka, da fatan tana lafiya, da yan uwa da abokan arziki" Yace "Alhamdulillah Kaka" Nenne tace "To madallah, Allah Ubangiji ya maka albarka, ka ce min a can Bauchi kuke da zama ko?" Jay yace "Eh can muke" Nenne tace "To kuwa in sha Allahu za ku gan ni a Bauchi kwanan nan don zan je duba wata 'ya ta, tana da yarinya me laluran shafar aljanu, gashi er ta zama budurwa abun dai ba dadi, in de na shiga Bauchi zan neme ka, dama in zan je Parida ke min rakiya tunda da wayewarta, a wace unguwan ku ke a Bauchi?" Jay na murmushi ya kira mata sunan wata unguwa daban, don har sannan dai Nenne bata san
an wani family bane, Nenne tace "Ai ko cikin kwanan nan zan shigo garin naku, rabona da zuwa yau kusan shekara biyu kenan" Jay yace "Allah ya kai mu lokacin Kaka" Nenne tace "Ameen" After some seconds ya daga kai ya kalleta yace "To yanxu Kaka tunda ta dawo yaushe za ku koma can Tudun Yolan?" Nenne tayi kasa da murya tace "Ai in sha Allahu nan da kwana uku za mu bar unguwan nan da daddare, don mutan unguwan ba yan arziki bane, bana son ma su san inda muka koma, kaga da daddare ai yafi sirri, zuwa gobe zan kira yan uwa da dangi duk a basu adireshin sabon unguwan mu hade a can ba sai sun taho nan yi mana rakiya ba tunda bama son yan unguwan su san inda za mu koma, shi dai Malam Ali har yanxu dar dar yake banda ni da nake tausan sa gaskiya da bazai bar unguwan nan ba, don yana gudun abinda zai je ya dawo, nace masa da xuciya daya kayi mana alkhairin nan ya cire komai a ransa, ba komai tattare da kai sai alkhairi don kai
an halaq ne" Jay yayi shiru don bai ma san me zai ce ba, ko da ya kawo ma mahaifin Khaleesat takardun gidan
in amsa yayi ya nuna masa he is much okay with where he is leaving with his family, yasan kawai yana gudun abinda zai je ya dawo ne, shi kuma da zuciya daya ya siya masu gidan ba don yana son anything in return ba, Nenne ta marairaice tace "Mu dai wannan abun arziki da ka mana
an nan Allah ya iya maka duniya da lahira, Allah ya raba ka da sharrin masu sharri, yayi maka albarka ya bude maka hanyoyin samu, Allah kuma ya ji
an mahaifinka ya sabunta masa rahama" A hankali Jay yace "Ameen" Nenne tace "Iya abinda za mu iya ce maka kenan
an nan, kuma babban dalilin da yasa ko yan unguwan nan bana son su san inda za mu koma shine kusan duk bayan kwana biyu sai
an iskan yaron nan Awdul ya zo unguwan nan, haka zai samu ubanta yayi ta masa magiya wai mu zai kara yaudara, har nan ya zo min na koresa da tabarya shi ne bai sake zuwa min ba sai dai yaje can gidan Malam Ali da ya raina, kuma ni ban ga alamar nadama a tare da shi ba, sam ba alkhairi ya dawo da shi ba, kaga tunda bamu san me ke ba
ar zuciyarsa ba tunda har yarinyar nan ta dawo kasar nan gwara tun wuri mu lallaba mu tashi cikin sirri babu wanda zai san inda muka koma, Shikenan mun rabu da shi lafiya, don wallahi ban yarda da yaron ba, sam babu Allah a ransa, da kyar in ba wani shirin yake ta yi ba, kaga kuwa ai dole mu ba er nan kariya kar ya sake cutar mana da ita" Jay yayi shiru ya kasa cewa komai yana kallon Nenne, sosai hankalin Khaleesat ya tashi jin abinda Nenne ke cewa kan Abdul, ta juya ta kalli Jay a sanyaye, ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "In sha Allahu komai ya zo karshe Kaka"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
Ur evidence 07087865788
HALYSAAH PAGE 85
Karfe tara da kusan rabi na dare Khaleesat ta shigo dakin Ummanta da sallama tana rike da ledan tsire wanda babanta ne ya siya mata, tun bayan isha'i take wajen baban nata tare da Nenne sai yanxu ta dawo daki, Jay sai da ya jira har Malam Ali ya dawo suka gaisa sannan ya bar unguwan daxu, zaunawa Khaleesat tayi kusa da Aunty Farida tana bude ledan naman tace "Su Islam har sun yi bacci" Umma dake kallonta tace "Nennen "Ne inen ta tafi ne?" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a tana can bata tafi ba" Aunty Farida tace "Baza ki ci tuwon naki ba?" Khaleesat ta langwabe kai tace "Nama zan ci" tuwon masara da miyar kuka Umma tayi, tana ganin tuwon daxu kawai tasan bazata ci ba, Aunty Farida tace "Ina kawarki Hajiya Safiyyah" Murmushi Khaleesat tayi tace "Tana can Maryland" Aunty Farida tace "Haba?

Ita bata dawo hutun ba kenan?" Khaleesat tace "Yayanta yace sai next week za su taho gaba daya" Aunty Farida tace "Allah sarki, Allah ya kawo su lafiya, na zata tare ku ka dawo ai...

Wai saura wata nawa yanxu ku kare karatun gaba daya?" Khaleesat tace "Bai wuce wata hudu ba, final semester kawai ya rage mana" Aunty Farida tace "Toh Allah Ubangiji ya baku sa'a, ya sa ku gama lafiya, ai kun kusa" Khaleesat tace "Ameen Aunty" Aunty Farida tace "To amma me yasa baku dawo har Junaid ba ya riga ku tahowa shi" Umma ta rike haba tana kallon Aunty Farida tace "Ikon Allah, kika san uzurinsa?" Ita dai Khaleesat murmushi kawal tayi bata ce komal ba ta matsar da takardan naman gabanta kusa da Aunty Farida bayan ta debar ma Umma nata....

Bayan Khaleesat taje tayi alwala ta dawo dakin Umma tayi shirin kwanciya, ta kwanta ta dau wayarta zata bude WhatsApp don rabonta da hawa tun da asuba da suka sauka Abuja kuma tasan Safiyyah dole zata yi mata magana, tana shiga WhatsApp din ta ga status din Ajay, sosai tayi mamaki don bata yi zaton yayi saving numberta ba, ta bude status din, daily reminder quote taga ya dora, ta tura masa Sticker sai taga yana ma online, WhatsApp call tayl ma Safiyyah bayan sun gama magana still bal mata reply ba, dama bata sa ran zai yi ba ta kashe data dinta ta kwanta.

Washegari Khaleesat na idar da azkar din da take ta kira Jay, don yace mata karfe shidda zai wuce Bauchi kuma driving zai yi, bayan sun gaisa tace "Are you still leaving early?" Yace "In sha Allah Halysaah, har na gama shiryawa ma" Tace "Toh Allah ya tsare hanya, Allah ya kai ka lafiya, don't forget to pray please...." Yace "I won't dear" Tace "Amma kayi breakfast?" Yace "Yea, I took tea, idan na fita gida zan kira ki in sha Allah, ko za ki koma bacci ne?" Ta girgiza kai tace "A'a" Yace "Ohk then, I will call you" Daga haka ya katse wayar.
Chapter 182 · 0% Book details