← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 218

Sashe 164

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Don Allah ko da kun sake haduwa da shi a school kar ki ce zaki yi wani sa'insa da shi" Safiyyah tace "Wai Abdul?" Yace "Eh" Tace "Ai tun da yayana ya hanani ban sake ba wallahi, ko zagina yayi iyaka in kira masa 911 kar yaje ya min wani mugun abu, amma na dena kulasa" Yace "Good...." Mikewa yayi yace "Let me talk to your frnd in the kitchen" Tana
an murmushi tace "Ohk" Kitchen ya nufa bayan ya shiga ya kulle kofar ya jingina jiki ya rungume hannu yana kallon Khaleesat dake goge goge a kitchen din bayan ta gama stew din da take yi, ta kasa juyawa ta kallesa, a hankali yace "Weldone Halysaah" Ta
an yi murmushi kawai, yace "Let drop off your friend at home" Ta gyada masa kai alamar to, yana kallonta yace "Sai mu je park daga can ko?" Sai a sannan ta
an kallesa, sai kuma tayi murmushi ta juya masa, shi dai kallonta kawai yake, after some seconds a hankali yace "Get ready ina jiran ki" Daga haka ya bude kofar kitchen din ya fita, Tsaye ya tarar da Safiyyah tana jiran su fito ta kama gabanta don bata gane irin wannan kallon da taga suna ma juna ba, Jay yace "Ki jira ta shirya sai mu yi dropping dinki a gida" Komawa tayi ta zauna tana murmushi tace "Ai ko Nagode, bari in maza inyi cancelling ride dina" Yace "Idan ta shirya ku sameni a Garage" Safiyyah tace "Toh" Fita yayi daga parlon, Khaleesat na fitowa kitchen Safiyyah ta gaya mata abinda Housemate dinta yace, a tare suka tafi dakin Khaleesat, Safiyyah ta zauna gefen gado tace "I wish i have freedom like you in this country...." Khaleesat tayi murmushi tana duba kayan da zata sa tace "Yanxun ma ai abinda kika ga dama kike yi, gashi har da zuwa birthday din Dog" Safiyyah tace "A'a wallahi, kinsan da yanda na fito yau kuwa, ni da ma ayi sacking Mustapha a wajen aiki su tattara su koma Nigeria" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba, tana fiddo kayan da zata canxa Safiyyah tace "Waow, dadina dake in kika so akwai fashion, kina sa wannan kaya ai har ku dawo gida Housemate bazai gaji da kallonki ba" Khaleesat tace "To bazan sa ba" Zata maida kayan Safiyyah ta tare press din dakin tayi bake bake a wajen tace "Ke dalla wasa fa nake maki" Da kyar Safiyyah ta lallabata ta saka kayan daga karshe, bayan nan still tayi forcing dinta ta
an yi mata light make up a fuska, Safiyyah ta koma gefe ta rike ha
a tana kallonta tana nazarin ace ita Allah ya ba kyan Khaleesat irin abubuwan da zata yi a duniya ai sai Allah, can ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace "Kullum kika yi sallah ki dinga gode ma Allah Khaleesat, he created you differently, wallahi you are so beautiful...." Khaleesat ta wani kalleta, sai kuma ta tsaya gaban madubi tana duba abinda zata goge a fuskarta, just eye pencil da powder kadai Safiyyah ta shafa mata, sai lip gloss shi ma lightly, ta ma rasa abun gogewa a fuskar tata, cause there is nothing special, a hankali Safiyyah dake ta kallonta tace "Ji fa lips dinki wani ba sai ya rantse kin shafa jan baki ba kawata, wallahi ki dinga addu'a idan zaki fita don nasan mutane ne daddaya basa tanka ki a zuciya idan kika fita suka gan ki, duk da dai nan kasar kowa ma da hasken sa" Safiyyah ta zaro ido tace "Lahhh, mun bar Housemate dinki a garage tun daxu fa" Khaleesat ta marairaice mata tace "Ni wallahi kunya nake ji Sophie, i am not comfortable with the dress and the make up" Safiyyah tace "Naga jaraba, idan ku ka yi auren haka zaki dinga kunyar tasa?" Khaleesat ta bude baki tana kallon Safiyyah ta ma kasa cewa komai, Safiyyah ta fixgo hannunta bayan ta tayata daukan handbag dinta ta ja ta suka fita daga dakin, har suka fito daga apartment din Khaleesat taki sakin jiki, Safiyya ta kar
e makullin apartment din a hannunta tace "Tafi ki shiga mota zan kulle gidan" Khaleesat taki tafiya, haka kawai aje bata kulle kofar da kyau ba Abdul ya samu hanyar shiga gidan, Safiyyah ta gama kulle kofar ta juya tana kallon Khaleesat tace "Don Allah ki dena yin abu kamar yan unguwan ku mana, America fa ne nan" Khaleesat ta kai hannu handle din kofar ta murda taji sa a bude, wani kallo tayi ma Safiyyah ta kwace makullinta ta kulle kofar da kyau, Safiyyah tace "Oho na zata ya kullu, mu je" Tunda Khaleesat ta nufi garage Housemate ke kallonta babu ko kiftawa, Safiyyah da taya bera bari ta bude mata front seat tana murmushi, Khaleesat ta wani kalleta sannan ta shiga motar ba tare da ta bari sun hada ido da Jay ba, Safiyyah ta koma bayan motar ta shiga, he wants to compliment her amma yayi shiru saboda Safiyyah, ya fara driving yana kallonta lokaci lokaci, daga karshe ya kasa hakuri yace "You look beautiful Halysaah" Safiyyah dake bayan motar ta fara blushing kamar ita aka ce ma haka, tana
an murmushi tace "Nima na gaya mata wallahi, amma ta zata am just pulling her legs, nace mata kyanta na daban ne a cikin kyawawa, duk mijin da ya aureta ya more a rayuwa, ko bacin rai yake ya kalleta zai ji ransa yayi fari
al, kuma ace ta samu miji me kyau kamar yanda dae kake din nan, waiiiii Allah kadai yasan yanda kids din ku za su zama don kyau..." Khaleesat taji da ma kawai hakura tayi da fitar nan gaba daya tsabar kunya, shi kam Jay murmushi kawai yake idonsa akan titi yana driving, Safiyyah ta bude jakarta ta ciro wayarta ganin Mustapha ke kiranta ta danna wayar a silent a fusace ta mayar cikin jaka, Jay ya kalli Khaleesat yayi kasa da murya yace "Wani park din kike son mu je?" Karaf a kunne Safiyyah, tace "Park za ku je Yaya Housemate" Yace "Yeah Safiyyah" Safiyya tace "To aje da ni mana don Allah sai in zama photographer" Khaleesat ta dafe kanta, Jay na murmushi yace "To nawa za a biya ki for the Job?" Ta kyalkyale da dariya tace "Haba, ko er lemonade ne kawai a siya min" Yana dariya yace "To an gama, amma baza a kira ki a gida ba?" Tace "A'a ba wanda zai neme ni wallahi" Ko da suka isa park din Safiyyah taki yarda ta zauna kusa da su Khaleesat wai za su yi inconveniencing dinta tana son ta nutsu tayi enjoying ambience din wajen da kyau, Khaleesat tasan duk scope din barin ta daga ita sai Jay ne yasa Safiyyah tace haka, shi ko Jay yaji dadin hankalin da Safiyyah tayi a nan, hotuna tace zata fara masu kar yamma yayi sosai, dadi kamar zai kashe Safiyyah ganin azababben kyan da hoton da ta fara masu yayi, can ta karasa inda suke tsaye tace "Ba fa wanda zai tsaya a space din nan da ku ka bari a tsakaninku gwara ku cike sa kawai" Khaleesat ta wani kalleta, Shi dai Jay Murmushi kawai yayi, Safiyyah tace "Ka
an matsa kusa da ita kadan Yaya Housemate so that the space won't make the picture look somehow" Slowly ya matsa kusa da Khaleesat yana kallonta yana murmushi, Khaleesat ta ganta er karama a kusa da shi ga daddaden kamshin turarensa da ya cika ta, tuni Safiyyah ta koma baya da gudu ta ci gaba da daukan hoton da take tana washe baki, farin ciki kamar ya kasheta, haka ta dinga controlling dinsu wajen daukan hotunan, tace su koma can, tace su dawo nan, ta tabbatar tayi masu hotuna masu bala'in kyau, har dai daga karshe Jay yace mata ya isa ita ma ta shigo su yi hoton, zai ba wata er Africa dake wajen wayarsa ta masu hoton har Safiyyah amma Safiyyah taki shiga tace "A'a kar in bata maku hoto ina ba
a da ni" Dariya Housemate yayi haka dai ya lallabata ta shigo aka yi masu hoton su uku, Safiyyah na murmushi tace "Amma fa tunda nake daukan hoto ban ta
a daukan wanda ya dauku kamar hotunan nan da na maku ba wallahi" Jay na murmushi yace "Dollar nawa za a baki to?" Dariya tayi ta tattara lemonade dinta da tacos da ya siya mata tace "Wannan ma da aka siya min Allah ya amfana" Daga haka ta kara gaba ta bar masu wajen, Jay was amaze at how Safiyyah snapped the pictures so well, ya kasa daina kallon Khaleesat a hoton, the pictures where so beautiful, Khaleesat tun da ta kalli hoto daya ta kasa ci gaba da kallon sauran ta koma ta zauna kawai, after a while ta daga ido ta
an kalli Jay taga kallonta yake, da sauri ta maida kanta kasa, a hankali yace "Halysaah" Bata dago kanta ba still tace "Uhm" Yace "Me yasa baki sakin jiki da ni yanxu?
Chapter 164 · 0% Book details