← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 193 OF 218

Sashe 193

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ina kika samu wannan kudin da kika siyo turaren nan?" Khaleesat dake ta sauraronsa ta kyabe baki tace "For once kayi acting like how every other person will do, kawai godiya zaka min for getting u a present and Birthday card, shikenan...." Yace "To bana so, zan kuma bada a maida maki kayanki"
an murmushi tayi tace "Ka maido min da kudin dai...." Katse wayar taji yayi, ta ta
e baki, dama tasan he will never change kuma ko kadan bata ji haushin abinda yayi mata ba, in ma bai yi bane zata yi mamaki, although she sees him as the senior brother she never had, shi yasa bata jin haushinsa ko kadan, ko barin wajen da take tsaye bata yi ba sai ga Alert din 1M ya shigo wayarta, dakinta ta tafi ta zauna ta dinga dariya kamar ta
a, wato har da riba ya kara mata a kai, kamar ta kirasa tace saura Birthday Card din yaushe za a maido mata kawai dai ta kyalesa ta bar wayar a daki ta fita parlor, yaran Mama Shatu ne zaune kasan tiles din parlon suna kallo tunda Nenne ta hanasu zama kan Carpet wai kar yayi datti, Nenne ta fito dakinta tace "Ace har karfe tara Ali yaki shigowa gidan nan, yana can zaune kofar gida kan benchi wani ba sai yace Mai gadi bane" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba don tun dawowarsu gidan har yanxu fa Babanta dari dari yake, yaki sakin jiki da gidan, in yana unguwan to a kofar gida zaka samesa zaune kan Benchi da ya sa kafinta ya buga masa, Nenne tace "Wannan ai salon ya ja mana kallon raini ne a unguwan nan, sai ya nuna ma kowa talakawa ne mu kyauta aka bamu gidan nan sannan hankalinsa zai kwanta, kwata kwata yaki sakin jiki yayi kamar shi ne Mai gidan da ya gina gidan" Khaleesat ta koma daki ta dau mayafinta ta fita compound, ita kanta she is feeling somehow yanda Babanta yaki zama comfortable a gidan, da alama babu yanda ya iya da mahaifiyarsa ne yasa ma yake gidan nan, one thing about her father is bai yarda mutum yayi maka gagarumin kyauta babu wani dalili me karfi ba, shi yasa har yau bai sake yayi na'am da gidan ba, don yace bai san dalilin siyan gidan ba, kamar kullum yana zaune kan Benchi da karamar wayarsa da yake kunna Radio yana saurare ga carbi a hannunsa yana ja, ya juya jin an bude gate, Khaleesat ta karasa ta zauna daga gefensa tana kallonsa tace "Baba bbu sauro a nan kuwa?" Malam Ali yace "Ai shi yasa na saka Safata Jiddah, sauro kam ai ba a rasa su a ko ina" Khaleesat ta
an yi murmushi tace "Amma Baba me yasa baka son ka dinga shiga ciki sai dai kawai ka shiga idan dare yayi sosai, da sassafe kuma ka fita kasuwa" Malam Ali yayi murmushi yace "To ai zaman gida na mata ne Jiddah, ni yaushe zan ta zama a cikin gida tare da mata" Sauke idonta tayi cikin sanyin murya tace "Baba ka kwantar da hankalinka plss, tsakaninsa da Allah ya bamu gidan nan ba don wata manufa ba, trust me pls" Malam Ali yayi wani murmushin ya jinjina kai yace "Ke yarinya ce har yanxu Jiddah, haka kawai babu wani dalilinsa bazai siya mana wannan gida me tsada da komai na more rayuwa a ciki ba, babu yanda na iya da Baabata ne amma wannan gida ba gidan da za mu saki jiki a cikinsa bane mu zauna don komai zai iya faruwa in ma yanxu in ma nan gaba, shi yasa ma nayi amfani da wannan dama wajen fara gyaran gidanmu da muka baro a Mariri tunda babu kowa ciki, yanxu haka har an fara plaster a kasa, kuma duk za a canza zinc din gidan da Ceiling, sannan a kara girman window din dakunan, a fitar da inda ruwa zai dinga fita ya dena taruwa cikin gidan, duk abokaina na can ni bance masu gida aka siya min ba, na dai ce an bani gida in zauna har zuwa sanda zan gama gyara nawa gidan na Mariri" Khaleesat ta kasa cewa komai, amma duk jikinta yayi sanyi sosai, tasan bata da wani kalman da zata sake using wajen convincing Babanta, don his belief will be his belief, ita dai tasan daga
angaren Housemate dinta baza a ta
a samun matsala akan gidan nan ba balle tuni ya basu takardun gidan da komai, wasu motoci uku ne suka shigo layin a jere, Malam Ali da Khaleesat suka juya suna kallon motocin da suka dallaro masu hasken fitila, amma lokaci daya duk aka kashe fitilun motar masu haske wanda da alama saboda su aka yi hakan, haka kawai Khaleesat taji gabanta na faduwa barin da taga motocin all halted at the same time a kusa kusa da su, Malam Ali dai ya gyara zama har sannan yana kallon motocin shi ma, after almost 2 minute da tsayuwar motocin, motar dake gaba wani ya bude ya sauko daga front seat da alama dai Security ne, ya bude back seat wanda ke bayan motar ma ya sauko, Malam Ali dai sai kallonsa yake don kara tabbatar da shi din yake gani ko ba shi ba, can ya kalli Khaleesat yace "Tashi ki shiga ciki Jiddah" Gaba daya hankalin Khaleesat ya gama tashi ta girgiza kai tace "A'a baba I will remain here" Guard din mutumin na biye da shi a baya ya nufo Malam Ali da murmushi fuskarsa ya kai masa hannu yace "Assalamu alaikum Alhaji Aliyu" Malam Ali ya mike ya kai masa hannu yana mamakin me kuma ya hadasa da Deputyn garin nan, Khaleesat dai bata ma ganesa ba amma ta mance rabon da ta shiga tashin hankali irin na wannan moment din, me zai kawo su wajen Babanta da daddaren nan da motoci har uku, Deputy ya kalleta yace "Sannu yarinya" Dakewa tayi ta gaishesa ya amsa da fara'a sannan ya maida dubansa kan Malam Ali yace "Idan babu damuwa Alhaji Ali mun zo maka ne akan wani batu me muhimmanci, Allah yasa zaka bamu lokacinka ka saurare mu, in kuma lokacin da za mu dawo zaka saka mana to duk babu damuwa" Malam Ali yace "To ni dai Allah ya sa lafiya ranka shi dade" Deputy yace "Babu komai sai Alkhairi ka kwantar da hankalin ka, ni da abokina ne da sauran manyan mutane muka zo har inda kake muka same ka akan wannan batu da ke tafe da mu, amma sai dai muna baka hakuri mun maka zuwan bazata, and this could be sort of inconvenient....." Malam Ali ya dake don zuwa yanxu kam ya gama
aguwan yaji me kuma ya hadasa da manyan mutane kamar yanda Deputy yace, sannan me ya kawo Deputy da kansa inda yake, a ina ma ya san sa??

Duk da yasan Deputy mutumin kirki ne kuma kowa ya shaida amma fa hankalinsa yaki kwanciya, yana gyada kai cikin karfin hali yace "A'a ba komai ranka shi dade, bari a shimfida tabarma sai mu zauna a nan tsakar gida, hakan yayi ko?" Deputy yace "To babu laifi Alhaji Ali" Malam Ali ya kalli Khaleesat yace "Shiga ciki ki shimfida mana tabarma a compound Jiddah" Mikewa Khaleesat tayi jiki a sanyaye ta shiga cikin gidan don yin abinda Babanta yace tayi....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
07087865788
HALYSAAH
PAGE 91
https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM?mode=ac_t
Bayan Khaleesat ta shimfida tabarmin da Babanta yasa ta shimfida ta koma parlor ta nufi kujera zata zauna har a lokacin hankalinta ya kasa kwanciya duk da irin approach din deputy toward her dad but she was so tense and confused, gashi ita bata ma san ko su waye ba, Nenne na kallonta har ta zauna kan kujera sannan tace "Yanxu baki lallabasa kun shigo gidan tare ba kika bar sa zaune bakin gate?

Haka rayuwa zata ci gaba yana zaman kofar gida kamar Mai gadi kenan?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, she was trying all possible best to keep calm at this moment, Nenne ta kyabe baki ta dau remote ta danna inda Islam ta nuna mata ana dannawa idan za a canza tashan kallo, tana canza tashar duk yaran dake zazzaune parlon suka juyo suna kallonta, ta tsuke fuska, Mikewa Khaleesat tayi ta bar parlon ta tafi dakin Ummanta ta sameta zaune tare da Aunty Farida sai Mama Shatu dake zaune daga kusa da kofar dakin a zuwan ta shigo hira da Umma, tunda Khaleesat ta shigo Umma ke kallonta, ganin Mama Shatu kawai Khaleesat ta juya ta tafi dakinta, Aunty Farida ma ta bi ta da kallo, bayan kusan minti biyar sai ga Umma ta shiga dakin nata tana kallonta tace "Lafiya Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta har Umma ta karaso ta zauna gefen gado tana kallonta, sai ga Aunty Farida ma ta shigo dakin tana tambayarta me ya faru?

Da kyar Khaleesat tace "Baba ne yayi ba
i a motoci ban san daga ina suke ba" Umma ta kasa daina kallonta ita ma a
an tsorace tace "A motoci kuma?

Ke wa ya gaya maki?" Khaleesat tace "Muna zaune tare a waje sai ga su a motocin" Hankali tashe Umma tace "Yanxu yana ina Malam din?" Khaleesat tace "Ya ce in shimfida masu tabarma a tsakar gida, har ma sun gaisa da ba
in" Juyawa Aunty Farida tayi ta fita daga dakin, ta tafi can compound ita ma dai hankalinta a tashe, ai ko ta hangosu zazzaune saman tabarma su hudu sai Malam Ali na biyar da ya sinne kai ko me suke gaya masa oho, ta juya ta koma cikin gida.
Chapter 193 · 0% Book details