← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 216 OF 218

Sashe 216

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Hajiya Shafa
atu tace
a wallahi mun y
breakfast, ruwan ma ya isa, mu da ba a ma san muna hanya ba, ai ba komai ruwan ya wadatar maa sha Allah Aunty Farida ta tafi dakin Umma tayi mata magana ta fito su gaisa, Sai da mazan nan suka shigo da tsadaddun akwati daddaya har ashirin da hudu parlon su Mama Zubaida da Mama Shatu na kirgawa a zuci, Hajiya Zaliha sai cewa take
Maa sha Allah
few bozes aka bude ana duba uban kayan ciki sama sama, Hajiya Zaliha ta ja Aunty Farida zuwa kitchen tana kallonta tace
Farida ko dai snacks din da nayi nace za a rarraba ma jama
a kawai a dauko a ba ma bakin nan don bai kamata a bar su haka ba duk da ba a san da zuwan su ba, amma gwara a fito kunya ka yaya kika ce Aunty Farida tace
lo Aunty hakan ma yay
, ni dama duk jikina yayi sanyi wallahi ban san me za a basu ba Hajiya Zaliha tace
Bari in kira Mai aikina kawai su kawo snack din dama har anyi packaging a foil an rufe, sai a biyo da shi ta kitchen kawai, akwai ruwan goran da yawa ne a gidan nan?

Aunty Farida tace
Pure water ne, na goran bai wuce pack biyu ba
Hajiya Zaliha tace
Toh bari in yi waya su kawo min, sannan kun san fa ana bada tukuici, shi kuma ya za ayi?

Aunty Farida tace
Toh, kamar ya kike ga za a bada Aunty?

Hajiya Zaliha tace
Wannan kaya haka Maa sha Allah kyau ace ko Miliyan daya ne a basu, amma kar a takura kai, ko dubu dari biyar ce sai a basu in zai ywu Aunty Farida tace
lah akwar cash dama na ciro sai ayi hatan Hajiya Zalsha tace
To ki koma parlon bari ingi waya yanzu Aunty Farida tace
Juyawa tayi ta koma Parlon don har taji sanyi wannan solution da new neighbor din tasu ta kawo, mata me kirki, Haj
ya Zaliha tayi wayar da zata yi, tana ta tsaye kitchen har sai da mai aikinta da yan matan ta biyu suka taha da snacks din, meat pie, cup cake, samosa, Doughnuts, Spring rolls, duk haka aka yi packaging dinsu separately kuma ba lai
i suna da Clan yawa, nan suka dire su a kitchen din, Mai aikin ta koma dauko pack din ruwa da lemo da tace su taho da, ko da Aunty Farida ta dawa kitchen din kasa cewa komai tayi don ita bata zata Small chaps din sun kai haka ba da Neighbor din tasu tay, gadiya ta fara yi mata, Hajiya Zaliha tace
Naga jiya an saya kaji, in da inda za a dibar masu shi ma a diba masu A Cooler me dan girma Aunty Farida ta dibar masu kajin ta cika shi dam, sannan suka fita da snack din parlor da Hajiya Zaliha don har suna shirin tafiya ne za su koma Bauchi wai a ranan, sosai Hajiya Shafa
atu ta nuna jin dadin snacks din da carton din ruwa da Lemo me dan dama da aka ajiye masu banda Hajiya Sumayya da ko uffan bata cewa a parlon, a haka aka kai masu packaged snack din da drinks da coolern nama zuwa mota, Nenne na kallon Hajiya Shafa
atu cikin nutsuwa tace
To Hajiya, da yake bamu san ya tsarin gidan naku yake ba, shi ne nace yanzu can Bauchin za aje yi mata Jere ko kuwa ya abun yake Hajiya Shafa
atu tace
a kaka, in ma jere ne idan ya bude gidansa na nan Kana sai a baku makulli a kai kayan nata can, ai yana da gidansa a nan, barin kayan a nan Kano zai fi sauki akan ace sai anje kai su Bauchi, balle yanzu dole masarauta za a kai ta, kun ga ai babu abinda za a bukata a can, in dai ba gidansa na Bauchin ba
Nenne tace
To Madallah, hakan ma ba laifi Hajiya
a haka su Hajiya Zaliha da Aunty Farida da Nenne da ma sauran mutanen parlon suka masu rakiya har zuwa gun motocin su ana masu Allah ya kiyaye hanya, bayan sun bar gidan Nenne ta kalli Hajiya Zaliha tace Lallai kin fidda mu kunya Zaliha, da sai dai a kulla masu koko da kosai a leda, sai da nace ma Parida ayi su cin cin da alkaki da dublan tace ta bada ayi a duniya yau za a kawo wai yanzu haka ake yi an dena ba kai wahala, to har yanzu ban ga idon cin cin ba balle Alkaki, da ya za mu yi da kunya yau ni Dije, lallai kin rufa mana asiri wallahi, Allah Ubangiji ya maki albarka ya raya maki zuria, mu ina muka san haka ake yi banda ke Hajiya Zaliha dai murmushi kawai tayi tace
Haba dai, babu komai Nenne
nan suka fara duba kayan lefen Khaleesat a tsanake a parlon, Hajiya Zaliha taga duk kayan babu na banza, kaya ne masu suna kaya ga uban yawa, har da tsadaddun Alkyabba biyar da lapaya babu adadi, Nenne har da hawaye ta ma rasa abinda zata ce don farin ciki da murna, da ta tuna irin yanda Abdul ya auri Khaleesat a gantale ko akwati daya basu gani ba a sunan lefe sai ta rushe da kuka, su Mama Shatu suka hau bata hakuri, ita dai Aunty Farida duk jikinta yayi sanyi sosai ko don saboda yanda aka daura aure babu nutsuwa ita kam bata yi expecting za a kawo wani lefe ba, tafi tunanin may be a bar mata a dakinta a can masarautar, a karamin kit Hajiya Zaliha taga dala dubu biyar, tana kallon su Aunty Farida tace
Wannan duk yanda aka yi kudin dinki ne suka saka
Nenne tace
Amma naga ba irin kudinmu bane ai ko kuskure aka yi
Hajiya Zaliha tayi dariya tace
In kika ji nawa ne wannan idan aka canza ai sai kin kama baki Nenne
Nenne ta saci kallon su Mama Zubaida sai kuma tace
Toh yi shiru Zaliha, Allah Ubangiji ya nuna na yan baya haka, kema Allah ya kawo ma yan matan ki mazaje na gari
Hajiya Zaliha na murmushi tace
Ameen Nenne
Nenne ta gyara zama tace
Kin san daga inda kayan nan suka fito?

Hajiya Zaliha tace
a hankali Nenne tace
Masarautar garin Bauchi
Da mamaki Hajiya Zaliha tace
Kai haba Nenne?
Chapter 216 · 0% Book details