← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 211 OF 218

Sashe 211

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ni ne zan iya reaching dinta kenan, ina ce same network muke using, in baka sameta ba ai nima haka, better still ka aika yaro cikin gidan ya kirata mana" Jay ya dau wayar Ajay dake ajiye, shi dai Ajay kallonsa kawai yake, number Khaleesat yayi dailing sai ga suna ya fito anyi saving as Jay's girl, Jay ya daga kai ya kallesa, dariya Ajay yayi, shi kansa bai ma san me ya basa dariya ba, May be the way he saved the contact, can dai ya fixge wayar yayi sending kiran, Jay yace "Sunanta ne baka sani ba?" Ajay yace "Oho, Haseenah kake ce mata ko Haseelah" kiran na shiga bayan
an lokaci Khaleesat ta
aga amma tayi shiru, Ajay yace "Ke kika saka min katin zaki yi shiru Malama?" A hankali tace "Good evening" Yace "Ana jiran ki a waje" Tace "Wa?" Yace "Kar ki bata ma mutane lokaci Malama" Daga haka ya katse wayarsa ya daga kai ya kalli Jay dake kallonsa, bayan kusan minti shidda sai ga Khaleesat ta fito tana sanye da hijab har kasa, kallon motar kawai take kamar bazata karasa ba can dai tana tafiya a hankali ta nufi gun motar, Ajay ya kunna fitilar cikin motar, shi dai Jay kallonta kawai yake suna hada ido ta sunkuyar da kai, kamar munafuka ta zaga ta wajen driver seat inda Ajay ke zaune, shi kansa kallon mamaki ya bi ta da shi har ta iso side dinsa ta tsaya tana kallonsa tace "Ga ni" Ajay ya juya ya kalli Jay da ya
an yi murmushi kawai don ko kadan bai ji haushin hakan da tayi ba, Ajay ya sake kallonta yace "Me zan maki?" Duk da abinda take ji a ranta sai da ya bata dariya amma bata yi ba ta wani kallesa kafin ta saci kallon Jay taga kallonta yake, sunkuyar da kanta tayi, Ajay ya hade rai yace "Malama you are obstructing the air from reaching me, matsa daga nan" Ta wani kallesa tace "To ai kai ne ka kirani" Ajay ya juya ya kalli Jay da yaki cewa komai, can ya bude motar, ta matsa gefe har ya sauko, tsayawa tayi gabansa ganin barin wajen zai yi kamar zata yi kuka tace "Toh ba kai ne ka kirani ba, why did you call me?" Da mamaki Ajay yace "Wai ina wasa dake ne, kinga na saba kiran ki dama?" Juyawa yayi ya bi ta gaban motar ya wuce ta bi sa da kallo, can ta saci kallon Jay suka hada ido, sauke idonta tayi lokaci daya jikinta yayi sanyi,
an murmushi yayi ya bude motar ya sauko sannan ya zagayo inda take tsaye, ta
an koma baya a hankali tace "Ina yini" Yace "But you know what happened few days ago wasn't intentional right?" Gyada masa kai tayi, cikin sanyin murya yace "To kiyi hakuri Halysaah, it's the work of the devil" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, yace "Kin hakura?" Ta gyada masa kai, yace "Ta yaya zan gane hakan?"
an murmushi tayi ta jingina da motar bata ce komai ba, yayi kasa da murya yace "Kin riga kin ba Ajay insight cewar we had issues ai" Ta
an kallesa tace "Ai bazai sani ba...." Yace "Wa yace maki, ur reaction says it all..." Ta girgiza masa kai tace "Zai yi tunanin i am just pulling his leg saboda shi ne ya kira wayana" Jay yace "To shikenan Halysaah, just came to check on you, hope there is no problem" Ta gyada masa kai kawai, a hankali yace "Ki ci gaba da mana addu'a kin ji Housemate?

We need it most at this point" Tace "In sha Allah, but...." Yace "But what?" A hankali ta jingina jikin motar cikin sanyin murya tace "No matter what ka zamo me yi ma Mahaifiyarka biyayya, may be aurenmu babu alkhairi ne shi yasa bata so...." Hawaye ne ya cika idonta ta kasa ci gaba, Jay dake ta kallonta da mamaki yace "Saboda me zaki ce aurenmu babu alkhairi Halysaah?

Me yasa zaki ce haka?

Kuma wa yace maki Mami bata son auremmu, ita kawai cewa tayi ga particular time din da take son ayi auren, Ajay ne ya gaya maki abinda ke faruwa har kika aiko min text din nan few days ago?" Cike da karfin hali Khaleesat tace "Da yaushe muke magana da shi har zai gaya min abinda ke faruwa, Kasan ai baza a boye min abinda Mom dinka taje tayi a gidanmu ba" Jay ya dinga kallonta babu ko kiftawa zuciyarsa na bugawa jin abinda tace, da kyar ya bude baki yace "Gidanku kuma Halysaah?

Kina nufin Mamina taje gidan ku??" Khaleesat dai ta dinga kallonsa don reaction dinsa ya nuna kwata kwata bai san Mami taje gidansu ba, hawayen dake makale idonta ya gangaro ta sauke kanta, jingina yayi da motar ya ma rasa abinda zai ce zuciyarsa na bugawa da karfi, Khaleesat ta goge hawayenta cikin sanyin murya tace "Ai ya ma wuce don har Mai martaba ya aika an ba su Babana hakuri, and he spoke to them on phone" Jay was more than shock ya dinga kallonta babu ko kiftawa don duk bai san da haka ba babu wanda ya gaya masa har Mai martaba, a hankali yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Khaleesat ta goge idonta cikin sanyin murya tace "I think it's better mu jira har sanda zata so aurenmu, but for now mu hakura kawai, haka Abdul ya aureni Mom dinsa bata so na, yan uwansa basa so na, yanxu kuma...." kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai bayan ta tuna abinda Mom din Abdul tayi mata, don yana daga cikin mamakin da har yau ya kasa barin ranta, Lokaci daya Jay ya rikice mata ya fara bata hakuri, zuwa yanxu ta fahimci halin da yake shiga idan yaga tana kuka hakan yasa ta dake ta hadiye kukan nata tana goge idonta, damuwa
arara fuskarsa yace "Kina tunanin zan iya hakura dake no matter what Halysaah?

Kinsan irin son da nake maki kuwa?

What do you think will become of me idan na yarda aka raba mu?" Ita dai Khaleesat ta kasa ce masa komai hawaye na zuba idonta tana gogewa, Yayi kokarin calming kansa cike da karfin hali "Kiyi hakuri Halysaah amma no matter what ni bazan rabu dake ba, in sha Allah komai zai yi dai dai da izinin Allah, zan kira Aunty Farida in basu hakuri, I knew nothing about this babu wanda ya sanar min Billah" Khaleesat ta
an yi murmushi tace "Ya wuce fa, abinda nace maka har gida Mai martaba ya aika a basu hakuri, ai kaga ya wuce kenan" Jay was speechless, bai ta
a tunanin abun Maminsa ya kai har haka ba, to menene yasa shi zata dinga masa pretending, wannan abun da take yi ne yake kara weighing dinsa down, shi abinda zata nuna masa daban abinda zata je tayi kuma daban, this is so heartbreaking to him, Ajay ne ya zagayo wajen yace "Pls I can't endure the mosquitoes in this area anymore, in baku gama ba ka samu nearest hotel kawai kayi lodging ni gida zan tafi" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, ya hade rai yace "Matsa min in shiga mota" Ta
an ta
e baki ta matsa, ya bude driver seat ya shiga, Khaleesat na kallon Jay a hankali tace "Shikenan sai da safe" Da damuwa yace "Ba mu gama magana ba Halysaah" Tace "Sai mu yi ta WhatsApp, ban gaya maka ba gobe da safe zamu tafi Kano da Aunty Murja da yarinyar kishiyarta sai Maman kishiyarta" Jay ya dinga kallonta, can yace "Amma shi ne baki gaya min ba all this while, gobe fa Friday" Ta
an yi murmushi tace "Na sani" Shiru yayi for almost 30 seconds kafin a hankali yace "In sha Allah zan zo da wuri sai in kai ku Kanon" Khaleesat ta
an bude ido tace "Tasha fa za mu je mu hau mota" Jay yace "Na ce zan kai ku, ku shirya da wuri..." A hankali tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen" Hannu ta
aga masa alamar Bye bye sannan ta bar wajen, Jay dai ya kasa ce mata komai ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gida, jiki a sanyaye ya zaga ya shiga front seat yana kallon Ajay with disappointment written all over his face yace "Nasan kasan cewar Mami taje gidansu Halysaah a Kano Amma ka boye min baka gaya min ba Junaid" Ajay ya
an kallesa yace "To meye amfanin gaya maka, me zaka yi?

She is ur mother babu yanda ka iya, Mai martaba did the needful, so babu amfanin gaya maka ayi ta jan magana....." Jay ya dinga kallonsa kawai, Ajay ya daga kafada yayi igniting motarsa ya fara reverse, har suka isa gida babu wanda yace komai cikinsu, har sannan jikin Jay a sanyaye yake ya rasa dalilin da yasa yaji ya fara loosing hope kuma yanxu, yaji ya shiga damuwa fiye da wanda yake ciki a baya, bai ta
a expecting haka daga Maminsa ba, Ajay na parking Jay ya bude motar slowly ya sauka, Ajay ya bi sa da kallo har yayi nisa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya kashe motarsa ya sauka shi ma, har ransa yake jin tausayinsa kuma shi dai yasan duk rashin kirkin Mami bata kai haka ba kawai Aunty ce ke instigating dinta tana exaggerating mata lamarin shi yasa take ta wannan abubuwan da take yi.
Chapter 211 · 0% Book details