← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 218

Sashe 77

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da yamma haka nan suka sake komawa gidan bayan Lauyan su yayi requesting su tambayi matan Malam Ali ko da akwai wani written debt forgiveness document kuma original one din da kotu ta bashi bayan masu karansa sun janye karar, cause in dai babu takardun to sai dai ayi case din biyan bashin da yake bin Alhaji Musa amma ba dai su yi karan sa ba, Bayan Ajay yayi parking ya juya yana kallon Jay yace "Zan jira ka" Er dariya Jay yayi yace "Toh ai da baka biyo ni ba kayi zaman ka a gida kawai" Bai jira cewar Ajay ba ya sauka daga cikin motar ya nufi cikin gidan, yau ma dai kamar jiya ba su kadai suka zo unguwan ba don securities da suka biyo su har sun fi na jiya tunda basu san ko Abdul na da Spy a unguwan ba, infact bazai ma rasa ba, definitely za a basa labarin wasu sun zo gidan su Khaleesat jiya, so they are not loosing guard by any means, and they are never going to let him take them unaware, A takaice Jay ya gaida Kishiyoyin Umma dake zaune tsakar gidan sun yi rashe rashe da su, yau ko murhu basu kunna ba don dawowar su kenan daga wajen Malamai, tun asuban fari suka bar gida sai yanxu suke dawowa, duk suka bi Jay da kallo, Jay dai yana tafe yana kallon Islam da Noor dake ma Umma wanke wanke a tsakar gidan don ko ba a gaya masa ba yasan siblings din Khaleesat ne duba da pheomelanin din su, a tare suka gaishesa ya sakar masu murmushi yace "How are you?" Murmushin kawai suka yi basu ce masa komai ba Islam na wanke wanke Noor na mata dauraya, Jay ya isa har kofar dakin Umma yayi sallama, Umma da ta gama gyara dakinta kenan ta saka turaren wuta na tsinke ta amsa sallaman sa, a kullum in zaka shigo dakin Umma a haka zaka tarar da shi fes fes, duk da ba komai bane a dakinta don ta siyar da komai nata amma kullum a gyara zaka same dakin da turaren tsinke, Jay ya shiga dakin Umma na kallonsa tace "Sannu da zuwa" Tabarma ta dauko ta shimfida masa don bata yi tunanin zai dawo yau kamar yanda yace mata jiya ba, Jay ya zauna yana murmushi ya gaisheta, Umma ta zauna kan dardumanta ta amsa gaisuwar sa, har a sannan zaka ga damuwar dake tare da ita alamar karfin hali kawai take, sai kuma ta mike tace "Bari in kawo maka ruwa" Ruwa ta debo masa a cup din stainless ta karaso ta ajiye masa a gabansa sannan ta koma ta zauna, yace "Nagode Umma"
an murmushi kawai tayi, Mama Zubaida da Mama Shatu suka yi tsit a tsakar gida ko wacce ta kasa kunne ko zata ji abinda ake cewa a dakin Umma, Ajay ne ya shigo gidan duk suka zuba masa na mujiya, sau daya ya kallesu ya dauke kai ya nufi dakin Umma, yau dai tsakar gidan a bushe yake bai yi gaja gaja da ruwa ba da yake basu yi girkin siyarwa ba, Islam na tsaye bakin kofar dakin Umma bayan ta shiga da kayan wanke wanken da suka yi da twin sis dinta, Ita kuma Noor na share inda suka yi wanke wanke, Idan Ajay ya kalli Noor sai ya kalli Islam, ya amsa gaisuwar da Noor ke masa tana rike da tsintsiya, yana isa bakin kofar dakin Umma ya ja dogon hancin Islam don ita ce ke mugun kama da Khaleesat har bakinsu iri daya ne, murmushi tayi tana kallonsa yace "How are you?" Ta sauke idonta bata ce komai ba yanda dai Khaleesat ke yi, da sallama ya shiga dakin Umma, Jay ya daga kai yana kallonsu don bai yi tunanin zai shigo ba, Umma ta amsa sallamansa, ya zauna daga gefen Jay sannan ya gaisheta, Umma ta amsa da murmushin karfin hali tana masa sannu da zuwa, after some seconds Jay ya fara magana a hankali yace "Umma akwai wasu takardu na yarjejeniyar kotu na yafiyan bashin da aka yi ma Mai gidan nan, Allah yasa kun san in da takardun suke ana bukatarsu ne" Umma tayi shiru, can tace "To, amma wallahi ban sani ba sai dai ko a duba dakinsa ko suna nan" Jay yace "Eh a duba Umma, Allah ya sa a gani" Umma tace "Ameen" Mikewa Umma tayi ta fita daga dakin, Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi ta da kallo har ta shiga dakin Malam Ali, after almost 8 mins sai ga Umma ta fito da wasu takardu wanda bata san ko na menene ba dai zata kai masu su duba ko akwai wanda ake nema a ciki, a haka ta wuce Kishiyoyinta da idanuwansa duk ke kanta, ta koma dakinta ta mika ma Jay takardun sannan ta koma kan dardumanta ta zauna, Jay ya dinga duba takardun daya bayan daya, yaga har da takardun makarantar Malam Ali, ashe har Degree garesa a Agriculture, kafin nan kuma sai da yayi diploma, yana ta dai duba tulin takardun har daga karshe yaga wasu takardun da yake saka rai na yarjejeniyar yafiyar da aka yi ma Malam Ali a kotu na biyan bashin Mahaifin Abdul ne, ya mika ma Ajay shi ma ya amsa yana duba takardun, Jay ya kalli Umma yace "Ina jin wannan ne takardun da muke nema" Umma tace "To Alhamdulillah" Jay yace "To za mu koma, duk yanda ake ciki za mu dawo in sha Allah" A hankali Umma tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma sai dai akwai wata uwar dakina da bata ji ba bata gani ba yan sanda suka tafi da ita shekaranjiya har yanxu ba a ma san wani caji ofis din aka kai ta ba" Ajay dake kallonta yace "Ko Baabar nan ta Hotoro?" Cike da karfin hali Umma tace "Ita, wallahi bata ji ba bata gani ba aka je aka tafi da ita" Ajay yayi shiru yana kara mamakin stupidity din Abdul, he don't think that guy is okay in anyway, after some seconds ya kalli Umma a hankali yace "Za mu bincika inda aka kai ta mu yi bailing dinta in sha Allah" Umma ta share hawayen da ya kawo idonta ta kasa cewa komai, Jay yace "Ki kwantar da hankalin ki Umma, in sha Allah komai zai wuce da izinin Allah" Cikin rawan murya Umma tace "Allah ya sa" Jay ya kalli Ajay, tsabar tausayin Umma kawai yaga gwara su gaya mata gaskiyar inda Khaleesat take ko zata
an samu sukuni a ranta, Jay ya sauke idonsa a hankali yace "Sannan Umma akwai maganar da zan gaya maki yanxu, amma don Allah kar ki gaya ma kowa har zuwa sanda za mu gama abinda muke" Ajay ya juya ya wani kallesa don har ya gano maganar da Jay zai gaya ma Umma, Umma na share idonta tace "To in sha Allah" a hankali Jay yace "Halysaah na Lagos, amma don Allah ba ma son kowa yasan hakan Umma, ko makusantan ki kar ki gaya ma tukun....." Umma da zuciyarta ke bugawa tace "Lagos kuma?

Wajen wa a Lagos?" Jay yace "Tana wajen sister din ki ne, amma mun ce mata kar ta nuna maki tana wajenta har sai sanda komai ya dai daita, shi yasa ma har yanxu bata gaya maki ba" Umma tayi shiru, amma fa ji tayi wani nutsuwa ya zo mata, lkci daya kuma taji hankalinta ya kwanta kamar an yaye mata kashi saba'in na damuwar da take ciki, Umma tace "In sha Allahu babu wanda zai ji hakan daga gare ni, yanda ku ka tsaya mana ku ma Allah Ubangiji ya tsaya maku haka, Allah ya saka maku da alkhairi..." Umma ta kasa ci gaba hawaye masu zafi na sauka idonta, A haka Ajay da Jay suka fita daga dakin Umma za su koma Office din lauya din su da takardun hoping shi ne kotu zata bukata, yau ma dai Ajay ji yayi kamar zafi zai kashesa a dakin Umma amma haka ya dinga daurewa har suka fita daga dakin sannan ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan da yayi, ya kalli Islam dake zaune bakin kofar dakin Umma da takardan makaranta a hannunta alamar karatu take, Noor kuma na hura gawayi a can gefe, ya saka hannu a aljihu ya ciro kudaden da bai san ko nawa bane ya mika ma Islam yana kallonta yace "Ku raba ke da er uwarki" Islam taki amsan kudin, ya hade rai yace "C'mon collect it" Jay dake kallonta shi ma ya sakar mata murmushi yace "Karba mana cutie" Islam ta kalli Noor amma still taki amsan kudin, Ajay ya zare mata ido yace "Kee, amsa nace" A hankali ta kai hannu ta amshi kudin, Ajay da Jay suka fita daga compound din, Kishiyoyin Umma suka dinga kallon uban kudin da aka ba Islam kamar idanuwansu za su fito ko kiftawan kirki basa yi, Islam ta tashi ta shiga dakin Umma da kudin a hannunta, Mama Zubaida ta mike ta ma Mama Shatu alamar su shiga daki, duk suka shiga dakin Mama Shatu sannan suka sake labule, Mama Zubaida ta rike haba tace "Anya kuwa Shatu baza mu san yanda za mu yi Abdul ya samu labarin abinda ke faruwa a gidan nan ba?
Chapter 77 · 0% Book details