← Book details Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 218

Sashe 1

Halysaah Part 6 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
1....

Tsaye take ta jingina da trunk din bishiya a wani babban garden dake dauke da shukoki iri iri da suka kawata wajen, tsuntsaye sai shawagi suke a garden din happily making a chirping sound as the sun set slowly, the view was so beautiful and breathe taking, duk da yanda ta kafe view din da ido gaba daya hankalinta baya gun, she was just staring at the setting sun absentmindedly, tayi nisa cikin tunanin da take, daga gefenta wata ma'aikaciyar asibiti ce in her mid 40, likitar ta dafa ta tana kallonta cikin kwantar da murya tace "Magariba ya gabato mu je kiyi alwala ko" Kallon likitar kawai take babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda take cewa ba, sai ga hawaye ya fara taruwa idonta tana sauke numfashi a hankali, likitar ta kama hannunta ta jawota jikinta calmly tace "C'mon sweet heart, are you breaking ur promise already?" ta kwantar da kanta jikin likitan hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, likitan ta lumshe ido tana patting dinta duk jikinta a sanyaye, a tare suka juya jin footstep a garden din, ya tsaya daga inda yake bai karaso ba yana kallonsu, likitan ta fara gaishesa cikin girmamawa, zame jikinta tayi daga na likitan ta juya masa baya alamar ko ganinsa bata son yi hawaye na zuba idonta, ji take kamar numfashinta zai dauke kamar ko da yaushe, ta fashe da matsanancin kuka ta dafe trunk din bishiyar dake gefenta, ko amsa gaisuwan likitar bai yi ba ya juya ya fice daga garden din, da sauri likitan ta kamota ganin faduwa zata yi, ta fara kokarin zaunar da ita akan lallausan carpet dake shimfide wajen trying to calm her down tace "Haba kanwata, me yasa baza ki cika min alkawarin da kika daukar min ba?" Muryarta na rawa tace "Kiyi hakuri bazan iya ba wallahi" Rungumeta likitan tayi tana bubbuga bayanta a hankali wani mugun tausayinta na shigarta, tayi attending to different cases in her career as a medical Doctor amma babu wanda ya ta
a daga mata hankali ya tsaya mata a rai irin na baiwar Allahn nan, she wish she can take away her pains, she wish she can make her happy once more, she wish she can make her forget the past and face the present, a hankali likitar tace "Halysaah...." khaleesat ta daga rinannun idonta tana kallon likitan, likitan tace "Kiyi hakuri Halysaah, kiyi hakuri" Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, likitan ta daga ta tana rike da hannunta suka bar garden din zuwa babban compound din gidan.

Few years back!

"Talk to Abdul about it, nasan bazai ta
a yarda da haka ba, and he will definitely find a way out for u immediately..." Khaleesat ta daga manyan idanuwanta tana kallon kawarta Safiyyah, kamar bazata ce komai ba sai kuma ta sauke idonta a hankali tace "That will be another huge burden Safiyyah, u know how expensive apartment can be in this state, gida da akwai tsada sosai, kuma na fa ce maki ni bazan sake tambayarsa komai ba, ko kuma ince yayi min wani abu...." Safiyyah tace "Cabdi, to in ba ki tambayesa ba kina da wanda zaki tambaya?

Balle ma kinsan halinsa lokaci daya tsaf zai juya situation din nan against you, i think gwara kawai ki sanar masa yafi maki kwanciyar hankali" Khaleesat tayi shiru tana nazarin abinda Safiyyah ta ce, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai tace "It's fine Safiyyah, ba sai na gaya masa ba i will cope in sha Allah, after all we have just a year and a half to go" Safiyyah na kallonta ta kamo hannunta tace "Ko zaki dawo wajena sai in gaya masu kawata zata zo ta
an zauna da mu zuwa wani
an lokaci?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Let not inconvenience them Safiyyah, kar ki damu kawai, i will sort my self out...." Safiyyah tace "No, i will talk to Ya Musty about ur current situation khaly, nasan bazai ce a'a ba, matarsa ce dai gagarumar er iska, and do i even care?

Ba ki ma san me take min ba yanxu a gidan, duk dare bata girki da ni sai dai in nemi abinda zan ci tunda kinsan Ya Musty night shift yake, ni kuma dama kin san i prefer junk food, kawai sai in hada cornflakes in sha abu na" Khaleesat tayi murmushi tace "Shine kike son in bi ki zuwa gidan a haka ko?

You are very funny" Safiyya ta juya ido tace "So what?

Naga ai ba kanta zaki zauna ba in kin dawo gidan, Yaya Mustyn nan fa is my cousin brother ko kin manta ne?

Saboda haka ko taki ko ta so dole in zauna a gidan har in gama karatuna, very wicked and self centered woman, wallahi kar ki wani damu in dai nayi ma Ya Musty magana kawai ki dauko kayanki ki dawo gidan ko zuwa gobe ne...." Khaleesat tace "Aa gaskiya don't even start that Safiyyah, i will cope with my present situation with time, nasan zan saba gradually, beside it's something that is normal kawai dai ni ce nake damun kai na saboda addinina da culture dina da dai wasu abubuwan da baza a rasa ba, any way... it's fine Safiyyah" Tana fadin haka ta kalli wayarta dake hannunta jin shigowar notification, tace "I think my Lyft is here Sophie, sai gobe in Allah ya kai mu" Safiyya ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk then, take care of ur self, i will stroll home too" a haka suka rabu, Khaleesat ta nufi Lyft din da tayi ordering zai maida ta gida.

Khaleesat na kitchen wajen karfe goma na dare ta gama girka Noodles da zata ci for dinner kenan taji alamar an bude kofar parlor, a hankali ta karasa juye Indomie dinta a plate ta dau fork ta saka sannan ta wanke pot din ta ajiye, ta bude fridge ta dau bottle water ta fita daga kitchen din, hanyar dakinta ta nufa direct, dai dai corridor aka bude kofar wani room that is just few steps away from her own room, ko kallon direction din bata yarda tayi ba tana kokarin bude kofar dakinta taji ance "Hi, good evening, we didn't get to meet when i was here in the morning I guess you've already left for school then, you can call me Jay, and i am ur new House mate, I moved in this morning...." Sai a sannan Khaleesat ta juya ta kallesa amma bata ce komai ba, ya gyada mata kai yace "Jay" babu yabo babu fallasa tace "I see" Ganin zata shige daki yace "A minute pls" Ta juya ta sake kallonsa da wani expression, a takaice yace "Ke bahaushiya ce?" Ta
an hade rai tace "I don't know what u are talking about" Yace "Oh ohk, i am asking for a permission..." Ita dai kallonsa kawai take, Ya gyara tsayuwarsa yace "As u can see it's late already now, can i use some of ur portable water and Beverages before i get mine tomorrow if you don't mind?" Khaleesat ta dauke kanta a takaice tace "Ohk" Yace "Alright" Daga haka ta shige dakinta ta kulle kofar ta saka key, ko da ta gama cin Indomie din bata ji zata iya bude kofa ta fita kai plate din kitchen ba, daga karshe kawai ta bar shi a wajen bayan ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta dauro alwala ta fito ta zauna edge din gadon dakin ta dau wayarta, Miss calls din Abdul ta gani har biyu wanda yayi mata tun karfe shidda, ta sauke ajiyar zuciya tana duba agogon wayarta dake nuna mata karfe goma da kusan rabi, meanwhile karfe kusan biyar kenan na asuba agogon Nigeria, bude WhatsApp dinta tayi ta dubasa taga yana online, hakan yasa ta masa WhatsApp call, yana dagawa tayi kasa da murya ta gaishesa a hankali, Bai amsa ba yace "Yanzu kika ga kirana?" Ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Kayi hakuri, yanzu naga kiran wallahi" Yace "You mean tun daxu wayarki baya gun ki kenan?" Tace "Not really, tun dai da na dawo schl nake karatu, in few months time zamu fara exams" Yace "I see, shi ne yasa kika ga ban yi deserving lokacin ki ba don zaku fara exams, ta yaya ma wayarki zai yi ring ki ce baki sani ba in ba rainin hankali ba?" Rasa abinda zata ce masa tayi, don wayar a silent yake kuma ya hanata barin waya a silent on several occasions, to avoid further issues sai bata ce masa wayar a silent yake ba, a hankali tace "Kayi hakuri, wallahi ba haka bane, i am sorry..." Yace "Sorry for ur self, malama so nake ki gaya min kina ina har wayarki rang twice baki ji ba? ur lectures today terminated by 4pm Baltimore time, so ina kika je daga nan?" Ta rufe ido ta bude don ta fara gajiya da tuhumar tasa, After few seconds ta marairaice tace "Ina parlor ne ina karatu, wayar kuma na daki" Yace "Kin fara zaman parlor kenan, when did that start?

House mate din taki ta dena shigowa da saurayinta ne gidan?" sai da gaban Khaleesat ya fadi, A hankali tace "Bata nan, taje LA jiya" Yace "Sau uku kenan ina kiranki a satin nan baki dagawa sai sanda kika ga dama ki biyoni, that nonsense shouldn't repeat it self again, a kanki aka fara karatu ko ni zaki gaya ma karatun Exams?" Shiru Khaleesat tayi lkci daya hawaye ya cika idonta, a
an fusace yace "Baki ji na ne?" Cikin sanyin murya tace "Naji, kayi hakuri hakan bazai sake faruwa ba in sha Allah" Yace "Good, you can go to bed" Tana goge hawayen da yaki tsaya mata tace "Nagode, sai da safe" Shi ya katse call din ta ajiye wayarta gefen gadon ta dora kanta a pillow hawaye na zuba idonta, after a while ta mike ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta dawo ta kashe wutan dakin tayi addu'an bacci ta kwanta....
Chapter 1 · 0% Book details