← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 172

Sashe 98

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka gama karyawa sannan Momy ta shiga ta shirya ta nufi gurin aikinta, ta bar Falmata ita kadai a gidan bayan ta fada mata ta dafa duk abun da ranta yake so da rana. Tana zaune falon tana kallo har 12 na rana, can kuma ta tashi ya fara gyara falon, domin tun shigowarta da suka gama karyawa Momy bata ce mata ta gyara komai ba, bayan kuma ta dauke ta ne aiki saboda haka, wata kila tana jin kunyar yi mata magana ne. Ita kuma hankalinta be bata wannan ba sai a yanzu, sai da ta gyara falon tsaf sai ta nufi upstairs, bata karasa dakin Momy ba ta tsaya cak tunawa da tai da abun da ya faru, a wacan karon bata tunanin halin Momy zai zo daya da na su, sai dai be kamata ta shiga ba tun da ba ita ta bata umarni ba.
Juyowa tai ya sauko kasa ta nufi kitchen din ta wanke kayan da suka ci abinci da su, sannan ta yi share tai mopping, ta maida komai a muhallinsa sannan ta fito falon, ta zauna ta cigaba da kallonta, sai da aka yi sallah sannan ta ta tashi a nan kuma ta rasa inda zata shiga tai alwala, domin bata san kan dakunan ba, kuma a ganinta be kamata ta shiga ba tare da izinin Momy ba, fitowa tai waje tunawa da masarautar ma akwai Garden, inda take alwala wata kila Momy ma tana da ita, sai da ta gama zagaye gidan da fadinsa amman bata ga Garden ba, sai dai ta hango fanfo a gurin da tankin gidan yake, gurin ta nufa ta bude fanfon tai alwala ta dawo cikin falon ta shimfida dankwalinta tai sallah, bayan ta gama ta tashi ta shiga kicin din, sai ta rasa me zata girka, Momy ta bata umarnin da girka duk abun da take so, amman bata fada mata inda kayan abincin suke ba, kuma tana tsoron kar tai bude bude tai laifi, magi man kuli, albasa da sauransu ta ga inda Momy take ajewa, shimkafa da sauran kayan masarufi ne bata san inda zata buda ta gansu ba. Har ta juyo da zimmar fitowa daga kitchen din sai kuma wata zuciyar tace ta mata ta bude karamar kofar kicin din mana, domin kofa biyu ne a kicin din data store da kuma ta fita wajen gidan, sai kuma kitchen cabinets da suke rufe, su ta fara budewa kamin ta nufi kamar kofar ta bude, sai tai arba ba babba daki mai cike da kayan abincin kala kala. Wasu an bude wasu kuma suna a rufe, rufewa tai ta nufi inda kayan miyar suke ta deba ta zuba a turmi ta daka sannan ta kunna gas ta dora tukunyar da take kyautata zaton zata wadatar ta zuba mai ta soya... A natse ta hada komai na jallof sai dai bata yi karabanin saka nama ko kifi ba duk kuwa da kasancewar ta ganshi a firizar dake kicin din.
A gurin ta zauna ta tsare girkinta har sai da ya dahu sannan ta sauke ta kashe gas din, dan karamin plate ta dauko ta zuba nata, ta dauko wata kula ta zubawa Momy, ta sake dauko wata ta zubawa Sirleem duk da bata da tabbacin zai dawo ko akasin hakan, haka nan dai take son ya zo ya ci girkinta.
Sai da abinci ya sha iska sannan ta dandana, tana jin yayi daidai ta daka wani tsalle ta dire tana jin wani irin dadi, ta dauki abinci ta fito falo ta zauna ta saka abinci a gaba ta ci abunta ta koshi, sannan ta koma kicin din ta wanke plate din ta aje ta dauko cup ta kunna fanfan ta tara ruwan ta sha, sannan ta aje kofin ta dawo falon ta zauna.

Momy bata dawo gidan ba sai kusan la'asar, a lokacin Falmata na kwance a kasa tana bachi, Momy kamar ta sani ta saka makulli ta waje ta bude kofar ta shigo, sai da ta kawo tsakiyar falon ta tsaya tana kallonta, ta takure guri daya tana ta bachi, irin yadda marasa galihu suke yi, hakan yasa tausayinta ya kara shiga zuciyar Momy, a ganinta kamata yayi ace tana gaban mahaifiyarta ko kuma gidan mahaifinta, amman tana a nan rakube tana bachi.

“Fulani�

Momy ta taba ta, sai ta farka a firgice, ganin Momy yasa ta tashi zaune.

“Sannu da zuwa Momy�

“Yauwa, ki hau kam kujera mana ki kwanta ya zaki kwanta a kasa sanyin tiles din ai sai ya shiga jikinki ga kuma sanyin ac�

“Tau na gode�

Ta mike tsaye ta hau saman kujera ta kwanta, Momy kuma ta hau sama ita da tufafin aikinta, bata sauko ba sai da tai wanka ta shirya cikin wasu tufafin kuma ta sauke nauyin sallah, la'asar sannan ta sauko kasa, ta shiga tashin Falmata.

“Tashi ki yi sallah la'asar�

“Tau�

Falmata ta mike tsaye.

“Ki shiga dakina akwai bandaki a ciki ki yi alwala idan kin fito akwai carpet a gurin sai ki yi sallah�

“Tau na gode�

Momy ta bita da kallo har ta haye sama ta shiga dakin. Sannan ta busar da iskar bakinta ta nufi kitchen, ba karamin mamaki tai ba ganin Falmata ta yi girki, duk da ta san ta fada mata ta girka abun da take so, gas Momy ta kunna ta dauko tafassashen naman dake firgin ta soya sannan, ta soya kwai ta zuba saman shimkafar sannan ta zubawa Falmata nata dabam a plate ta dauko ta fito kicin din, ko da ta fito Falmata ta sauko tana zaune kasa tana kallo.

“Ungo ga wannan ki ci nasan dai kin ci abinci ko?�

Falmata ta saka hannu biyu ta karba.

“Na gode Allah ya saka da alheri�

“Daga yau idan zaki girki ki rika saka nama, wa ke da abincin kula daya?�

“Ya Sirleem�

Ta amsa kanta a kasa tana jin kunyar da bata san dalilinta ba. Momy ta yi murmushi.

“Ai yana da wahala Sirleem ya dawo yanzu, kin ba mai gadi?�

“Aa�

“To ki zube a wata kula tana nan rawaya ki zubawa a ciki ki kaiwa mai gadi�

“To�

Ta mike tsaye ta nufi kitchen din ba dan ta jidadin yadda Momy tace a bawa mai gadi ba, domin ba dan shi ta zuba ba, sai dai babu yadda ta iya dole ta bi umarninta, juye abincin tai a kular da momy ta fada mata ta dauka ta fito da shi.

“Ki bar kofar a bude ba sai kin rufe ba�

“Tau�

Ta amsa sannan ta nufi kofar ta wangale ta fita, kamar wacce bata son tafiya ko take bakincikin a bashi abincin haka ta isa inda yake ta gaishe sannan ta aje masa abincin.

“Momy tace na kawo�

“Tau Allah yayi albarka�

“Ameen�

Ta juyo ta dawo falon cikin rashin dadin rai. A inda ta zauna dazun ta sake zama ta fara cin nama sai da ta cinye tsokokin sannan ta fara cin kwan, shi kam kadan ta ci ta ji ya isheta ba dan bata son kwai ba sai dan cikar da cikinta yai, sakamakon abincin data ci dazun.
Tana zaune a gidan har dare, sai duk ta ji ta takura, sai ta ji tafi sakewa a masarautar duk kuwa da kasancewar a nan Momy tafi sake mata fuska da komai ba, amman acan tana wuni da su Labib suna rage mata kewa, kuma a can tana fita ta zagaya har garden din tana wasa da su, a nan kam wuni tai kallo, duk yadda take da son kallo sai ta ji a gudireta.
Ta inda abun ya zo mata da sauki ana kiran magariba sai ga mai daukarta ya iso ya aiko mai gadin kiranta.

“To gata nan zuwa�

Momy ta amsa masa sannan ta kalli Falmata tace.

“Tau sai ki je yana kiranki, kin koshi dai ko? Na ga ma baki ci tuwon da yawa ba, ko baki son miyar shuwaka ne?�

“Aa ina so, na ci ai ya ishe ni�

“To Allah ya tsare hanya�

“Ameen na gode sai da safe�

Ta fada sannan ta nufi kofa tana gyara Hijabinta, duk abunda ya faru a masarauta Momy bata da labari hakan yasa Falmata bata san komai ba. Bata tare da tsoro ko fargabar komai ba ta shiga gidansu bakinta kumshe da sallama, daga Naja har Tumba aka rasa mai amsa mata, Tumba ta ranka uban tagumi tana kallon kofar kamar mai jiran shigowarta.

“Makira... Macijiyar soshiya...yar bakinciki, ke wannna da dake nai kishi dana shiga uku.. Da yanzu ina can gidanmu ina zawarci�

Gaban Falmata ya fadi jin irin kalaman da Tumba take jifarta da su, sai ta tsaya cak tana kallon Tumba da fitilar touch light take haskawa. Sai ta rasa dalilin wannan kirari da Tumba tai mata, domin bata san ta aikata wani laifi ba kamin ta fita, sai dai inda sabo ya kamata ace ta saba da abun da ake mata a gidan, domin ko bata da laifi ana kakaro shi a dora mata.

“Daga gidan uban wa kika?�

“Daga gurin aiki�

“Gurin aikin ubanki, makira annamimiya, barauniya�

Jikinta ya fara bari zuciyarta ta shuga bugawa da mugun karfi.

“Gurin wasu mazan kike zuwa kenan?�

“Aa Wallahi daga gurin aiki nake�

Ta fada da muryar dake nuna kuka na kusanto, Tumba ta dauki butar dake kusa da ita ta jefa mata iya karfinta tana jin kamar ta saka wuta ta kone ta, Falmata ta kauce da sauri tana kuka.
Chapter 98 · 0% Book details