Sashe 114
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Gaskiya a yanzu dai baya nan, amman lafiya dai?�
Ba su ce masa komai ba suka juya, sai da suka kusa kai wa gurin motarsu sai zuciyarsa ta raya masa ba lallai ne dan wahala da yi kiransa ta sake kiransa ba, idan kama sa za ayi ai da Police za a zo ba da dogarawa ba, idan kuma rabo ne yak kiransa ya ki amsawa ba, what if wani samu ne yake kwankwaso masa kofa yaki budewa.
“Kai ku dakata ni ne Sardauna�
Kusan a tare suka juyo suna kallonsa da mamaki.
“Ban san ku ba ne shiyasa na boye ina fatar dai ba wani laifin ba ne�
“Kasan daga inda aka aiko mu kiranka har kake mana karya?�
Dayan su ya fada yana nuna shi.
“Ayi hakuri dan Allah, ka san duniyar ce yanzu sai da haka�
“Kai dan talakawa ka shiga hankalinka ba ayi ma gidan sarauta karya, yanzu nan zamu koya maka hankali�
“Gafarce ni dan Allah ayi min afuwa�
“Shiga mota muje�
“Okay bari na fadawa Yayata�
Ya juya da sauri ya koma cikin gidan, ko da ya shiga ya samu Anti Rabi a tsaye dafe da kirji tana sauraren abun da zai fada mata domin hankalinta be bata sallamar Allah da Annabi ake musu ba.
“Su waye?�
“Daga masarauta suke�
Ta dafe kirji tana zaro ido.
“Masarauta kuma? Me kai? Ko ka sake zuwa ne bayan abubuwan nan da suka faru?�
“Wallahi ban sake ba, ni ko hanyar masarautar ban sake bi ba, amman da yanzu zan je na ji dalilin kiran�
“Aa karka je, baka sani ba ko wani abun ne aka shirya maka�
“Idan ban je ba ai wulakanci za su min, kara naje na ji ko minene dai�
“Allah ya tsare, muna ta zancensu aje suna kan hanya da wani kiran, Allah yasa wannan kiran alheri ne, ya tsare�
“Ameen�
Ya amsa sannan ya shiga dakinsa ya canja tufafin jikinsa daga karamin wando da vest zuwa dogon wando ta jallabiya. Ya fito zuwa waje, har bakin kofar waje Anti ta bishi tana kallo tana jifarsa da addu'a kariya. Daidaikun mutanen da suke waje ne suka rika binsa da kallon ganin dogarawan sanye da tufafi har su uku kuma ga sy da mota mai kyau sun saka Sardauna a gaba. Sai da yai addu'a sannan ya shiga motar suma suka shiga mai tukin yai ribas suka juya. Ba su faka a ko'ina ba sai cikin masarautar, sai dai hankalin Sardauna ya dan kwanta ganin a bangaren Ammy suka faka ba bangaren Hajiya ba. A cikin motar suka bar shi har sai da dayan ya fita ya shiga ciki ya fito sannan ya bude masa motar.
“Fito�
Sardauna ya fito da tunani kala kala, sai dai zuciyarsa ta fi raya masa cewar Ammy zata masa tambayoyi ne akan abubuwan da suka faru, ko kuma Nana ce ta saka a dauko shi saboda tana son ganinsa wata kila ita ma ta yi missing dinsa kamar yadda yai nata. A dakin aje baki na musamman aka kaishi na bangaren Ammy, har ya zauna saman kujera sai kuma wata zuciyar ta raya masa ya zauna kasa kamar ko wane talaka. Cikin mintunan da ba su fi talatin ba hadimai suka jera masa kayan marmari ta soyayen namam kaza da na rago ga farfesun kayan ciki, ga jalof ta ji kayan lambu da kayan ciki sai kamshi take, a gafe daya kuma ga kayan sanyi da plates an aje masa.
“Ammy ta ci ka ci abinci kamin ta fito�
Dayat hadimar ta fada sannan suka fice tare da sauran, at first ji yai kamar mafarki yake, tun a kawo shi falon dake cike da kayan alatu da akai kadai ya isa ya sanar masa cewar kiran alheri ne ake masa, balle kuma yanzu da aka kawata zuciyarsa da abubuwan da take so, baki yai arba da abubuwan da suka dade ba su ga juna ba.
“Ammy suke nufi ko Nana dai?�
Ta tambaya kansa cike da kwankwanto, har ga Allah yana son duka abubuwan da aka jera masa sai dai a karon farko ya samu kansa da kasa taba komai, a tunaninsa a zuwa yanzu ya kamata ya rika kawar da kai akan wasu abubuwan musamman wadanda za su zubar masa da kima. Gorar ruwan kawai ya bude ya sha, shi ma saboda ya samu ya jika makoshinsa ne. Ya kusan awa daya a dakin sannan aka turo kofar dakin wata hadima ce a gaba wanda ta rikewa Ammy kofar ta shigo ta zauna a kujerar dake fuskantar Sardauna. Cikin natsuwa Ammy ta zauna tana kallon Sardauna, wanda ya sadda kai kasa ya kasa dagowa ya kalleta, sai kokarin risinawa yai yana mika mata gaisuwa irin gaisuwar da be taba yi ma wani ba.
“Lafiya Kalau�
Ammy ta amsa masa da kanta tana dagawa Hadimar dake kokarin amsawa a madadinta.
“Je ki kira min Nana�
“An gama ranki ya dade�
Hadimar ta juya da sauri ta fice, Ammy ta kalli Sardauna da duba irin na tsanaki ta ce
“Ya sunanka ma?�
“Ahmad Abubakar, amman anfi sanina da Sardauna Hajiya�
Ya amsa mata da sauri yana jin faduwar gaban da ba ta tsoro ko shakka ba face kwarjini da jin kunyar Ammy.
“Yayi kyau, Nana na fada mana abun da kai, kuma na jidadi sosai na yaba�
Ammy ta fada sai kuma yai shiru tana kara sanar da shi isa da izza irin ta matan sarakuna.
“Akwai aikin da kake a yanzu?�
Kamin ya bata amsa Nana ta turo kofar dakin ta shigo, wani irin jan numfashi tai tana zaro da sauri taje kusa da Ammy ta zauna can kuma ta ji zaman be mata ba ta rumgume Ammy tana jin kamar ta je ta rumgume Sardauna, bata tabbatar ta yi missing dinsa sosa ba sai a yau da tai arba da fuskarsa.
“Aa bana aikin komai a yanzu gaskiya�
Ammy ta yi shiru tana karantar natsuwarsa.
“Ka yi karatu?�
“Eh na yi diploma�
“Kana son ka cigaba?�
“Ina so ranki ya dade, burina kenan�
After some sec Ammy ta ce.
“Wace makaranta kake so? Ko kuma aiki kake so?�
“Idan zan samu karatun na fi son sa gaskiya, kuma ba ni da zabi duk inda na samu damar cigaba da karatu zan yi farinciki�
“Zaka iya karatu a waje?�
Sardauna be san lokacin da ya dago ya kalli Ammy ba, sai kuma ya kalli Nana wanda ita ma kallon Ammy take da mamaki.
“Zazzzazzz.....zan iya�
“To zamu bincika maka best universities da suke waje, inshallah zam dauki nauyin karatunka sai ka kawo takardunka da wuri�
Da sauri Nana ta rumgume Ammy tana murna, Sardauna kam mantawa yai ya mike tsaye sai kuma ya fadi zaune kamar ta rude, i cant believe ba mafarki yake ba. Take a gurin yai ma Allah sujada godiya ya dago da hawaye a fuskarsa yana kallon Ammy.
“Na gode na gode na gode, Wallahi ban san abun da zan fada ba zan san iya addu'ar da zan miki ba, na gode Allah ya biyaki da aljanna�
“Ni ma na gode, ka cancanci komai daga garemu, bayan shi akwai abun da kake so?�
“Kin gama min komai Hajiya�
Sardauna na fada har lokacin idonsa na cike da hawaye. Nana ta yi karaf tace.
“Aa Ammy, ba ki gama ba, a gidan Yayarsa yake zaune kuma gidan duk ya lalace, aAmmy dan Allah ki yi wani abu�
“Wannan kuma za a sanarwa Mai Martaba, na san zai yi wani abu akai inshallah�
Nana ta sake rumgume ta tana murna.
“Thank You so much Ammy na gode�
Ammy ta yi murmushi, Sardauna ma murmushi yake yana kallon Ammy yana jin kamar ace yana da damar da zai rumgume ta saboda murna da jindadin abun da tai masa.
***
Kamar yadda suka tsara washe garin ranar Bappa da Kawu Dan iroro suka shirya suka tafi Katsina, bayan mota ta sauke su suka tari napep suka fada mata inda zata kaisu, wato unguwar su Shattima har ba kin gate din gidan Mai Napep din ya sauke su, sai da suka kira Shattima ya sanar musu yana cikin gidan sannan suka sallami mai napep, suna waje tsaye mai gadin ya bude gate din ya shiga da su, shi yai musu iso har cikin falon Shattima, kallon kallo Bappa da kawu suka rika da ma juna kamin su koma kallon tsarin falon da uban dukiyar da aka zuba.
Shattima ya sauko sanye da manyan kaya shadda da hula sai kamshi yake zubawa kamar wani sabon ango, da kansa ya dauko musu lemu sannan yai musu izinin zaman kan kujerar tsabanin kasa da suke zaune. Kalamai na natsuwa da mutuntawa yake musu duk tambayar da suka masa sai ya basu amsa, daga karshe ya kira Ammy video call ya ce ta saka akaiwa Fadime saboda kawai su yarda da shi kuma su samu natsuwa. Ganin Fadime a video call din ya tabbatarwa su Bappa gaskiyarsa, tana jin muryar Bappa ta hau murna tana jindadin jin muryar mahaifinta duk da kasancewar bata ganinsa hakuri ta hau bashi tana ta kuka da hawaye sai fadin take ya zo ya dauke ta.
Bayan sun gama Shattima ya karba yana ta kallon fuskarta ba tare da yace mata komai ba, sannan ya kashe wayar. Da kansa ya tabbatar musu cewar zai siye musu tickets na jirgi na zuwa can Yola din tare da shi, har waje ya rakosu ya saka direbansa ta kaisu har garin Bandalo bayan yayi musu kyauta 100k.
Cikin far'a da jindadi suka isa gida suna da godiya ta sakawa Shattima albarka da yaba halinsa. Tun a daren ranar Shattima ya siya musu tickets kuma ya kira Bappa ya fada masa cewar ya shirya da safe zai aiko direbansa ya dauke su, washe gari tun 6am direban Shattima ya kama hanyar zuwa garin Bandalo dan dauko su Bappa ko da ya isa har sun shirya, suka shiga motar ya juyo da su zuwa Katsina, maimakon a wuce da su airport sai da aka fara biyawa da su gidan Shattima suka karya da lafiyayen abincin da yai musu order sannan suka shiga wata motar ta alfarma tare da shi zuwa airport.
Ba su wuce 30 min da isa airport din ba jirginsu ya tashi zuwa Yola...
FALMATA POV.