Sashe 112
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Ni Wallahi bana son ka, Wasim nake so�
Yayi murmushi tare da kai hannun ja labban nata.
“You cute ji labbanki�
“Ka daina taba ni ba kyau tana matar wani�
Kansa ya daga sama yai dariya marar sauti sannan ya sauke kai ya kalleta.
“Me kike son na riko miki idan zan dawo?�
“Ni dai kyale ni�
Ta fada hawaye na cika idonta, maganar da yai sai ta ga kamar gaske ne, ita kuma har ga Allah Wasim take so.
Ta juya da sauri ta tana lalabe, sai ya kai hannunsa a hankali ya kama nata ya ja a hankali ya koma da ita hanyar da ta Jekadiya ta fito da ita, sai da suka kusa shiga falon sannan ya tsaya ya saka hannunsa ya share mata hawaye.
“Daina kuka Kanen mahaifina yayi min mata, wasa nake miki�
“Tau...�
Ta fada tana jin sanyi a ranta, sai ya sake murmushi.
“Kurciyarki na burgeni, i like you serious�
Ta yi dariya, da waya ya kira jekadiya ya zo ta kama hannunta. Sai a lokacin ya tuna da zancen Falmata.
“Ina Falmatan take?�
“Tana nan Falo ranka ya dade�
“Je ki kirata, saki wannan�
“To ranka ya dade�
Ta saki Fadime ta wuce da sauri, tsaye yai yana kallon Fadime fuskarsa da murmushi, haka nan yake samun kansa cikin nishadi da sakewar zuciya.
“Fateema ko?�
Ta yi dariya tare da saka hannayenta ta rufe idonta.
“To ba na zo birni ba�
Yayi murmushi yana kallon fuskarta sai lumshe ido yake, Falmata ce ta shigo tare da jekadiya suka zube kasa, take Shattima ya hade fuska kamar be taba murmushi ba. da hannu yai ma Jekadiya alama da ta tafi, sai ta mike tsaye ta fice.
“Ya sunanki ma?�
“Falmata�
Ta amsa da sauri tana sanda kai kasa.
“Zan tambaye ki wani abu, kuma gaskiya nake son ki fada min�
“To ranka ya dade�
“Kina ganin wata alama a gurin su Labib?�
“Eh wani a farkon zuwana suna zabura, amman da nake musu addu'a sai suka daina har yawan kukan da suke�
“Okay, idan kin kaisu gurin Iya tai musu wanka kina ganin wani abun?�
Kamin Falmata ta bada amsa Fadime ta zaro ido.
“Oh ashe yayanka ne Iya take bibiya, ashe ita take cinye maka mata kenan? Ke ma wannan Falmata kin shiga uku Hajiya Babb...�
Bata karasa ba Shattima ya saka hannunsa ya rufe mata baki. Falmata kam kanta na kasa bata son kallon Shattima gudun kar tai laifi.
“Ina jinki�
“Gaskiya idan na musu addu'a idan na kaisu bata karba, kuma daga baya sai ya zamana kamar tana tsoron tabasu ma�
“Shine kawai abun da kika sani?�
Falmata ta yi shiru tana tunani,tana son ta fada masa cewar ta hada goro da furen tufafi ta ci ta ga Iya na gudunta, sai dai tana tsoron kar abun ya wuce nan a kirata kotu ko wani gurin ta kasa maimaita haka.
“Shikenan abun da na sani�
Yayi mata alama da ta fice, sai ta tashi da sauri ta fice daga gurin jikinta na rawa sai mamakin tambayar take. Sai da ta fice sannan Shattima ya dauke hannunsa daga bakin Fadime.
“Falon mu kowa na shigowa har da Iya idan ba ki iya bankinki ba zata ji, kuma Hajiya babba ma tana shigowa, kuma kin san idan ta ji zata ja miki wahala ne, dan haka ki kama bakinki ban da yawan magana�
“Da gaske, dan Allah kace a aje ni daki�
“Tau
Ya fada yana murmushi sannan ya kira Jekadiya a waya ta zo ta tafi da ita. Dafe take da hannun Jekadiya har suka isa cikin falon, Jekadiya ta zaunar da ita kasa kusa da ita, Fadime ta zauna ne kawai ba dan tana so ba. Jin Jekafiya ta tashi sakamakon buga kofar falon da akai yasa ita ma ta mike tsaye tana kallon inda take jim sautin takun tafiyar Jekafiya. Jekadiya ta karasa gurin kofar ta bude ganin Kausar tare da wasu mata uku yasa ta bude musu kofar tana musu sannu da zuwa.
“Ammy na nan?�
Kausar ta tambaya sai jekadiya ta amsa mata da sauri.
“Eh tana ciki, ayi mata magana ne?�
“Eh su Hajiyan Zariya ne za su mata gaisuwa�
“To�
Jekadiya ta juya da sauri ya nufi hanyar dakin Ammy ta kwankwasa mata kofa, sai da bayan minti biyar Ammy ta bata izinin shiga. Sai ta tura kofar dakin a hankali ta shiga ta sanar mata. Ammy ta amsa ba tare da ta juyo ba domin bata son Jekadiya ta ga idonta ya yi ja saboda kukan da ta sha.
“Ina zuwa, a kaisu karamin Falo�
“To�
Ta juya ta fita da sauri. Ta karaso inda suke ta sanar musu Ammy na fitowa.
“Bismillah muje karamin falo�
Fadime ta na jin haka ta kira sunan Jekadiya.
“Jekadiya su waye suka zo?�
Sai da Jekadiya ta kalli Kausar sannan ta amsawa Fadime.
“Kausar ce da baki�
“Ni dai ki dora ni akan kujera, ba Shattima yace ki kula da ni ba? Kuma ya ce ki boye ni kar Hajiya Babba ko Iya ta gan ni�
Daga Kausar har Hajiyar Zariyar da Kawayenta biyu sai da suka kalli Fadime.
“Wacece Wannan?�
“Wallahi ban san sunanta ba, ke amsa kina jin ana magana�
Jekadiya ta fada, aiko Fadime ta kama baki ta tsuke taki tai magana.
“Hajiya Bismillah ku...�
Suka bi bayanta suna kallon Fadime cike da mamakin wacece ita.
NANA POV.
Littafai ne ta zube a gabanta hannunta rike da biro, ta dukufa sai karatu take saboda exam din dake tafe, tun daga lokacin da tai wa AA alkawarin zuwa makaranta ba ta taba fashi zuwa ba, and no matter how zata ga kudi Ammy ko na wani tana kokarin ta hana kanta tabawa, duk wani son kudi da take a yanzu tana kokari ta yaki abun a ranta, domin ko kadan bata son tsaba alkawarin Sardauna a iya ganinta ta haka ne zata saka masa da abun da yai mata. Turo kofar dakinta akai a hankali tana dago kai tai arba da Ammy, dan sauke idonta tai kasa tana tunanin laifin da dai, domin ba kasafai Ammy take zuwa dakin dubata ba sai dai yi mata fada ko saka ta wani aikin. Ammy ta zauna kusa da ita tana kallon littafan dake gabanta.
“Karatu kike yi�
“Eh muna da exam Monday�
“Yayi kyau�
Ammy ta fada sai dai wannan yarta take kallo cike da tausayinta.
“Ammy wani abun nai?�
“No kawai na zo na duba ki ne�
Nana ta yi shiru tana dan mamaki, Ammy ta kai hannu ta dauki daya daga cikin littafan tana dubawa.
“Nana ba ki da kamar ni a duniyar, kina da wata damuwa ko kuma akwai abun da kike so, ki fada min kai tsaye na miki alkawari matukar abun nan be fi karfina ba zan miki shi�
“Yaya ya ce miki Wani abu ne?�
“Be fada min komai ba, kawai dai na ga baki da gatan daya wuce ni, na fahimci damuwarki a yanzu, kina bukatar kulawa da soyayyar mahaifiya�
Nana ta dago tana kallonta.
“Wani abu ne ya faru?�
Idon Ammy ya cika da kwalla ta fara kirga yatsun hannunta.
“Ban jidadin rashin saurarenki da nai ba, ya kamata nai hakuri na kai zuciya nesa, amman na kasa, wani lokacin abubuwa suna min yawa a akaina, na kan rasa ta ina zan samu natsuwa, kuma ban taba tunanin ki na yin wasu dabi'u ba ne saboda wasu matsalolin, a tunanina kina yi ne kawai dan ki bakanta min, amman yanzu na gane ki yi hakuri kin ji�
Sai Nana ta ji wani iri ganin hawaye na saukowa a idon mahaifiyarta.
“Ammy ki daina kuka dan Allah, Sardauna yace na daina bata miki rai�
Ammy ta share hawayenta wasu na sauko mata.
“Sardauna yaron da ya cece ki ko?�
“Eh, Ammy...�
Sai kuma tai shiru. Ammy ta kai hannu ta dago fuskarta.
“Fada min matsalarki Nana, ki dauke ni kamar kawa�
“Dan Allah ki taimaka Sardauna ya dawo, yayarsa taceba zata bari ya dawo ba, amman ni ina son ya dawo kuma shi ma yana so�
“So kike ya dawo?�
Ta daga kai.
“Zai dawo Nana na miki wannan alkawarin, kuma zan masa gatan da baki taba zaton mahaifiyarki zata iya ba�
“Ammy da gaske?�
Ammy ta daga mata kai hawaye na sauko mata. Nana ta rumgume ta da sauri.
“Thank you so much Ammy Thank You�
Ammy ya kwantar da kanta kirjinta ta rumgumeta sosai tana hawaye.
“Nana ki min alkawari kullum da safe zaki yi addu'an tsari, akwai husnil muslim a dakina zan kawo miki, ki tsare addu'a safe da yamma, kuma kar Hajiya Babba ta sake baki wani abu ki ci ko ki sha ko shafawa kinji yata?�
“Daman Sardauna yace min na daina zuwa bangarenta ma�
Ammy ta lumshe ido hawaye na sauko mata tana yaba kyautatawar Sardauna a ranta.
03/12/2021, 18:56 - ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*