Sashe 117
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta nufi dakin Hajiya talatu cikin taku na alfarma da kokarin danne damuwarta. Da waya makale a kunne ta shiga tana fadawa Kausar ta rufe mata dakinta ta manta ta fito bata rufe dakin ba. Tun kamin ta zauna Hajiya Talatu ta saka salati tana dora hannu a kai saboda abun da Jurry ta fada mata
“Mun shiga ukun mu, Allah ni kaina idan Waziri ya ji wannan maganar aurena ya kare kenan, ba zai dubi yaya ko shekarun da akai a tare ba, akan Mai Martaba da Ammy baya jin asss bale kuma ya ji zance har da neman kisa? Gashi na je nemawa Mai jidda maganin hana auren? Wallahi kenan nan tawa ta karewa�
Hajiya ta tabe baki.
“Ta mu ta kare zaki ce, ni kina tunanin idan Mai Martaba ya sani zama zai yi da ni? Korani zai yi ya barwa Ammy gida ita kadai, daman abun da take nema kenan, sannan na shiga a bakin duniya...�
Kamin Hajiya ta karasa Jurry ta jarba tana kuka.
“Ni kuma ba zan samu mijin aure ba, kuma Mai Martaba tsine min zai yi, na zama zakka a gidan nan�
Hajiya Babba ta kalli Hajiya Talatu zuciyata da mugun nauyi.
“Na fada miki ki aika a dauko matar nna yau yau ba sai gobe ba, ta zo nan ta yi mana duk abun da ya kamata, haka mu kai wasa a baya har Falmata da Sardauna suna mana tsaye a wuya, domin su na su duk mai sauki ne ba kamar wannan ba�
Hajiya ta ce.
“Ai kina kirana na kira matar da ta san gurin na ce ta bar abun da take ta dauki shatar motar kasuwa taje ta dauko ta, domin idan na aika tare da direba wani karin tonon asirin ne, amman gaskiya wannan bokan ya iya munafurci, ta ya zai mana haka? Daga neman taimako?�
Jurry dai sai kuka take Hajiya Babba kuma ta nutsa a duniyar tunani tana ganin abun kamar ba gaske ba.
FADIME POV.
Sai da suka wuce take tambayar Jekafiya.
“Wacece wanda ta tambaye ni?�
“Ba ki santa ba�
Jekakadiya ta amsa mata a takaice haka take mata a duk lokacin da ta tambaye ta, ba ma ita kadai ba har wasu da ba Ammy ko Shattima ba idan suka tambaye wani abun gudun laifi ko ace ka yi sai ta ba shi takaitacciyar amsa, hakan da Jekadiya tai ba karamin kufula Fadime yai ba, daman ta lura a duk lokacin da ta tambaye ta wani abun sai ta amsa mata kamar bata son amsarwa ko kuma ta takaita, cikin bacin rai Fadime ta bi ta har suka isa inda Sarkin gida yake ta gabatar masa da sakon Shattima, sai ya zabura da sauri ya ya shiga gaba suna binsa a baya har suka isa gurin da ya sauke su Bappa, shi da kansa ya shiga karamin falon da sallama suka amsa masa, suna bata cikin hakkinsa. Fadime na jin muryar Bappa ta fara kokarin sakin Jekadiya tana kiransa.
“Bappa...�
Kamin ya fito har Jekadiya ta kama hannunta ta shiga da ita cikin falon, ganin Fadime yasa idon Bappa cika da kwalla ita kam tu ni nata hawayen suka fara zuba sai hannu take mikawa ta taba shi.
“Bappa... Kai ne�
Ta fada cikin kuka da shauki, sai ya amsa mata da yaren fulantanci yana kama hannunta.
“Fulani...! Har nan kika kawo mu? Fulani baki jin magana dubi yadda kika koma?�
Sai ta fashe da kuka tana taba fuskarsa.
“Dan Allah Bappa ka yafe min, na yi dana sani kuma ba zan sake ba, Bappa idona na ya rufe bana ganin komai tun ranar idon be bude ba har yanzu, Bappa ba dadi bana ganin kowa, sai dubu kullum komai zan yi sai dai na yi lalabe�
Ta kara fashewa da kuka sosai, sai lalaben fuskar Bappa take, Jekadiya na ganin haka ta juya ta fice tare da Sarkin gida.
“Ai rashin jinki ne ya ja miki, daman wanda be ji bari ba zai ji hoho... Ko ina ke ce Fadime ke ko tsoro baki ji�
Cewar Kawu dan iroro cikin fada yana tsude hannu, Fadime na jin haka ta kama Bappa ta rike tana kokarin rumgume shi.
“Bappa dan Allah karka min fada, ka ga bana gani yanzu, dan Allah kar ka ga laifina, zan fada maka gaskiyar komai da komai Wallahi na rantse�
A gurin da take tsaye ta zauna ta fara labarta musu abubuwan da suka faru na gaskiyar inda ta san ta yi karya sai ta fashe da kuka tace Bappa ya yafe mata ita ma ba da son ranta tai ba, duk abun da ta fada kwatankwacin abun da Wasim ya fada musu ne, sai karin wasu abubuwan da Wasim be fada ba domin ita zai ta fede daga biri har wutsiya, sai da ta kai karshe sannan ta tsaya tambayar Bappa tambaya mai nauyi.
“Bappa zaka bar ni na auri Wasim?�
Kamin Bappa yace komai Kawu ya kwatseta ta hanyar daka mata tsawa yana zaginta da hannu kamar tana ganinsa.
“Ke arrrr Fadime, kina abu kamar ba ki sha nonon Fulani ba, duk wannan abun da ya faru da ke be isa ya saka ki natsu ba, ki yi hankali? Ke wace irin yace? Rashin kunya kiri kiri har kina tambayar aure? To shi Wasim din musulmi ne aka ce miki? Kuma mutumen da danginsa suka miki haka kina tunanin za su yarda ki aureshi ne? Tsafe ki za su yi ko ma su kashe ki gaba daya�
Ta dafa zuciyarta da karfi tana zare ido.
“Na shiga uku... Bappa ai zai iya musulunta kuma dan sarauta ne baka ga yadda ke masa ba�
Ta fada da iyakar gaskiyarta, domin ta gani da idonta irin yadda ake bawa Wasim girma a garinsu saboda yana dan sarki abun da ya kara mata son sa kenan a ranta, tana jin ita idan ta aure shi haka za ayi mata. Bappa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yarsa, gaba daya ya rasa a wane muhalli zai saka Fadime, tunaninta har yanzu be bata ta fara jin tsoron ta nisanta kanta da Wasim ba sai neman aurensa take, kuma kai tsaye take fada masa haka abun da ya tabawa al'adarsu ta fulani.
“Fulani natsu ki saurareni, kin girma ya kamata ace kina da hankali da tunani kamar sa'o'inki, ke yanzu mutumen da zuwa garinsu kadai ya maida ke haka har zuciyarki take miki shaa'war aurensa? Ki fara bari ki ga idon idan ya bude tukuna kika sani ko a haka zaki zauna har abada? Sanadinayar abun da kika aikata Allah kadai ya san halin da kika jefamu, Shatu har da ciwo tai ke kuma kin zama a haka ni da Kawu da ba mu taba mafarkin zuwa yola ba gamu a gidan babba sarki a yola saboda ke, to ya isa haka nan idan kina yin hankali da tunani ki fara tun yanzu idan kuma ba zaki yi ba, ni na san maganinki?�
“Menene maganina Bappa? Ai shi Wasim din ba zama zai yi a garinsu ba, zan fada masa ya dawo garin mu ya zauna tare da mu, Bappa dan Allah�
Bappa ta ji kamar ya dauke ta da mari sai kuma wata zuciyar ta hana shi ganin halin makantar da take ciki.
SHATTIMA POV.
Yana tura kofar dakin Ammy suka yi ido biyu da Baba Waziri, wani irin abu Shattima ya ji kamar ya fasa ihu ko kuma ya juya ya koma amman ba hali, yanayin yadda ya ga Ammy na murmushi ya san ba zai wuce zancen aurensu da Maijidda ba.
“Waziri samun dan'uwa irinka abu ne mai wahala a wannan zamani, kwata kwata kai ta kanka kake ji ba ta dan'uwanka�
Cewar Ammy tana kallonsa da murmushin irin yadda yake nunawa mai martaba da yayansa kulawa abun har mamaki yake bawa Ammy. Baba Waziri yayi murmushi.
“Ammy kenan, irin mu suna nan da yawa, ai ko'ina akwai mutanen kwarai, kuma rayuwar duniyar nan idan ba ka yi dan Allah da zumunta ba dan me zaka yi? Mu na yi saboda yaranmu su ma su gani su koya daga garemu, a can ba mu san kanmu ko yayan mu sai yayan yan'uwa su ne namu na mu kuma su ne na su�
“Allah ya saka da alheri ya kara hada kanku kuma ya hada kan zuri'ar gaba daya�
Sai da Baba Waziri ya gama magana da Ammy sannan Shattima ya mika masa gaisuwa yana kallon Ammy domin ta hanyarta yake gane labari mai dadi ko akasin haka, tsoronsa daya kar ace zancen aurensa ne Baba Waziri ke yi, tun da ya sanar masa tun a waya cewar ya fara shiri, Baba Waziri ya duba Shattima duba bana wasa ba, irin duban nan na babba da yaro ya soma magana cikin dattijantaka.
“Shattima ka yi hakuri, ban nemi shawararka ko izininka ba na tsayarda rana karshen watan nan, na san idan na tsaya neman shawararka zaka fara kawo wasu kabli da ba'adi ne, kuma ina jin na isa da kai shiyasa nai haka�
Shattima yayi shiru be ce komai ba, sai dai har ga Allah be son wannan hadin da Baba Waziri yai tsakaninsa da Maijidda, ya san tana tsoron ta aureshi ta mutu kamar sauran matan, kuma ko da babu mutuwa ba lallai ne a samu kwanaciyar hankali a tsakaninsu ba, domin shi be taba kawo ta a ransa ba, ita ma kuma bata taba kawo shi a ranta ba, ko da ma ace sun taba irin yadda Hajiya Talatu taka kin Ammy abu ne mai wahala ta bar su su yi zaman lafiya balle kuma ga wannan jarabawar da take tare da shi.
“Ba ka ce komai ba�
Baba Waziri ya fada jin yayi shiru ya kasa furta komai, ga fuskarsa bata nuna jindadi ko akasin haka ba. Shattima ya dago ya kalli Ammy sannan ya kalli Baba Waziri ya ce.
“Baba ita Maijidda ta amince? Idan har bata amince ba dan Allah kar ayi mata dole, ni akwai wanda zan iya nema a hadamu...�
Ammy ta watsa masa wani kallo mai kama da harara, Baba Waziri ma kallonsa yake.
ZAINAB POV.