Sashe 156
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hawaye ne ya sauko mata, har ga Allah a lokacin da Bappa yai mata maganarsa ba ta ce bata son shi ba, tace dai ita tana son Wasim, domin har kusan dukanta Bappa yai a lokacin amman bata dauka aure yake nufi ba.
“Kuma ai cewa yai Fulani za ki iya auren ranka ya dade be ce yana so na ba�
Ta fada tana jin wani irin kololin bakinciki na ta so mata kamar ta hade zuciya ta mutu. Mikewa tai tsaye ta nufi bukkarta hawaye na sauko mata, if ta san Bappa yana nufin Shattima yana son ta ta ya za a iya cewa aa? Tana tana son Wasim amman shi ma Shattiman ai tana sonsa musamman a irin wannan lokacin da yake kawar mata da kewar Wasim, kuma yake yawan faranta mata rai.
“Kenan yanzu wata zai aura?�
Hawaye ya sauko mata, sanin cewar ba za ta iya fadawa Bappa cewar yanzu ta aminta ba, ko ma ta aminta ai ba a a fasa auren ba, amman shi be fada mata haka ba kuma be fada mata cewar zai yi aure ba.
“Yanzu ai zai dinga ganin na masa butulci...�
Ta fada kamar gaske irin na yan matan nan da suka dade tare da sarauya daga karshe suka yaudare shi.
“Daman ba ni da sa'a babu mai cewa yana so na, Wasim ne kawai ya ce haka shi ma kuma ya tafi ya bar ni wannan ma haka�
Ta dauki wayar ta jefar a kasa iya karfinta tana jin wani kololon bakinciki na taso mata, hakan be wadatar da ita ba sai da ta saka fada ta taka wayar tana hawaye.
“Bana son wayar bana son komai�
Ta fashe da kuka marar sauti tana jin cewar laifin na Bappa ne, da be fahimtar da ita ba har ta gane. Fitowa tai tana kuka ta zo gurin Inna tana fadin.
“Kuma Wallahi ba zan je bikin nan ba...�
Inna ta yi dariya ta soma mata magana da halshen fulatanci.
“Kishi kike kenan?�
“Ni bana kishi kawai dai ina jin bakinciki, kenan ni ba zan yi aure ba? Ba ni da farin jini... Ban san wa na gado ba�
“Ubanki kika gado, waya ce ki ce ba ki so? Ke wai har yanzu ba za ki daina halinki ba ko Fulani?�
“To a dawo baya a tambaye ni, ni ba cewa na yi bana so ba, cewa na yi ina son Wasim shi ma ai da ne, yanzu na rasa kowa�
Inna bata sake bin ta kanta ba, domin maganar cewa bata san wa ta gado ba ya batawa Inna rai kuma ta san da ita take.
“Inna dan Allah idan Bappa ya dawo ki ce masa a bar wacan maganar, amman karki ce ni na ce�
“Sai ki fada masa da kaki�
Tashi Fadime tai ganin da gaske Inna take zancen auren Shattima, daukar abun tai ta saka a rai kuka ta sha b dan kadan ba tana tunawa yadda tai ta fama a baya babu saurayi mai sonta, tun da ta shigr ciki dakin bata fito ba har akai sallah azahar sannan ta fito tai sallah, Inna na fadin ga abincinta bata kula ba ta koma ciki ita ala dole abun duniya ya isheta. Gashi sai tunanin Shattiman take yadda yake mata da kuma dan zaman da tai a can ta sabo da shi, bayan shi yanzu kan bata da wanda take ganin zai iya zuwa ya ce yana sonta ko ya so ma. Kuka tai sosai har sai da fatar idonta ta soma ciwo, Inna bata dauki abun da gaske ba har sai da akai la'asar ta ga Fadime ta fito ta yi alwala ta koma ciki ta yi sallah kuma bata fito ba.
“Fulani Fulani...�
Tana jin Inna na kiranta ta ki ta amsa, domin ta daura damarar kin cin abinci da sakewa saboda abun da Inna ta fada mata. Inna ta yunkura zata tashi kenan sai ga sallama wata bakuwar fuska tare da wata Lanti yar'uwar Amo, sosai gaban Inna ya fadi ganinsu a cikin gidan. Ta amsa musu a sanyaye tana mika musu gaisuwa cikin karfin hali zuciyarta na raya mata ko dai wani abu suka zo su yi ma Fadime ko ita ko kuma Amo suka maido dakinta.
“Sannu da zuwa�
Inna ta fada sannan ta nufi bukkarta ta dauko musu tabarma ta shimfida musu, ko kallon tabarma ba su yi ba suka ce.
“Aa ba zama ya kawo mu ba, ina maganar zama aure ya kare�
Inna ta ji gabanta ya fadi.
“Kaya mu ka zo kwasa?�
“Lafiya dai?�
“Allah dai ya kyauta idan Jauro ya dawo ai sai ki tambaye shi�
Lanti ta sake fada sannan ta bukkar Amo ta bude rufin da akai ta dage labulen zanen ta shiga ta fara to da kayanta, yan tsuman kara sai yan tarkacenta, wanda suke tare kuma tana shirya kayan tana kullewa a zane, ta dauka ta kai wajen mai yar gof din da suke tare yana sakawa har suka kwashe komai tsab Fadime bata leko waje ba, Inna kuma na tsaye tana kallon ikon Allah zuciyarta na raya mata abubuwa kala kala, sai dai fi tunanin mutuwa Amo tai duba da tsawon lokacin da aka kwashe ba amo ba labarinta.
“To Amo dai zama ya kare sai ki shimfida tabarma dakinta ki kara, ki biya bukanki bukatarki ta biya�
Lanti ta fada sannan ta sa kai ta fice, Inna na maida mata da martani.
“Ba ni da boka ba ni da malam sai Allah, komai aka min Allah ne mai kare ni kuma mugun abun ta ne ya koma kanta�
Kalaman da Inna take ne yasa Fadime fito tana kallon bukkar Amo da aka bude, tana jin lokacin da ake kwasar kayan amman ta ki fitowa sai da ta ji Lanti na fadin zama ya kare. Zuwa tai ta leka bukkar ta ga babu komai ciki sai dan abunda ba a rasa ba marar amfani.
“Kenan mun huta mun huta mun huta�
Ta fada tana rawa kamar ba ita ba.
“Allah yasa ma ta mutu can mugun abun ta ya bita, mun huta da dangin mayu�
Rawa take har da juyawa jamar ba ita ce ta gama kuka ba, Inna dai sai kallonta take domin idomta ya nuna kuka tai amman yanzu tana murna an saki Amo.
 Bappa be dawo a sai yamma kamar yadda ya saba, tun kamin Inna ta labarta masa abun da ya faru ya fahimci sun kwashe komai domin alamu ya nuna haka, kuma daman can ya san za a rina tun da ya aika mata da takardar sakinta, domin har yanzu ciwon be barta ba sai an kwantar sai an tayar bata iya komai.
Inna har cikin ranta ta jidadin labarin da Bappa ya bata cewar ya saki Amo, daman can kullum tunaninta da zulluminta kar wata rana Amo ta dawo da zama a gidan, sai dai bata nunawa Bappa ba sai ta nuna masa bata jidadin hakan da yai ba.
“Haba Malam tana cikin ciwo kuma sai ka kara mata wannan? Da ma ka hakura har ta samu lafiya tukuna�
Uffan be ce mata ba ya dauki redio sa yana kamo bbc domin 8:30pm ta yi, bayan ya kama tashar ta aje redio ya dauko tuwon shimkafar da miyar kuka ga uban manshanu Inna ta labta masa abun ka da masu abu, ya bude ya dauki ruwan da ke cikin kofin ya wanke hannunsa ya fara cin, Inna sai gyara masa fitila take tana jinta kamar wata Amarya. (Na ce Ashe su Inna ba a son kishiya 🤣).
“Na yi magana da Sani mai jakkai na fada masa ya fara kawo mana yashi�
“Mashallahu aiki ya tashi kenan?�
“To me ake jira, tun da komai ya mallaka, Shehu ma ya ce abokansa zai dauko yan birni su yi aiki�
“Allah ya taimaka, ai haka yayi kara da ka siyar da wacan gidan ka dawo nan ka gina mana na zamani�
“Eh komai za a saka Inshallahu, na fada Shehu gida mai kyau kuma gina mai kwari na ke so, yace ko gidan Mai Garin ba zai kai nawa ba, yace har da tistis za a saka�
Fadime ta kyalkyale da dariya daga can cikin bukkar da take.
“Bappa tiles ake cewa ba tistis�
Daga Inna har Bappa dariya sukai domin ba su dauka tana sauraren firar ta su ba.
“Ja'ira, to tilis din har shi za a saka Inshallahu�
“Allah ya nuna mana an gama komai cikin kwanciyar hankali da tsawon rai, shi kuma Allah ya saka masa da alheri�
Fadime na jin haka sai ta tuno da zancen dazun cewar Shattima zai yi aure, take ta koma ruwa tana kukanta kadan kadan ta yadda babu wanda zai ji. Inna ba ta fadawa Bappa komai ba har sai da dare ya raba ta tabbatar a lokacin Fadime ta yi bachi sannan ta labarta masa yadda sukai da Fadime dazun. Bappa yayi murmushi.
“Ai hakan da tai ya taimaka mana, ina tabbatar miki da ace ta san da maganar nan da yanzu an yi garkuwa da mu ance mu kawo kudi, amman a haka sai ya taimaka mana babu wanda ya sani sai dai kwatsan su ji an yi ma Fulani amre�
“Ai haka yafi, daman magana ta yi yawa akanta sai fadar ake bata da miji, ai Wallahi hakan ya min dadi Allah ya bata miji ba karami ba, dan babba mutum kuma babban mutum mai mutunci�
Bappa yayi murmushi jin dadi yana jin wata kima na kama shi zai yi sakuta da sarki.
FALMATA POV.
Hannunsa na lakkame da wuyanta tana karanta masa abun da ta rubuta.
“Mamana, Babana Kakana�
Ya saka yatsansa ya ja kumatunta na dama.
“Ina mijina?�
Ta yi dariya sai ta kalleshi.
“Mantawa na yi�
Yatsan nasa ya saka mata a baki ta fara tsasa kamar sweet.
“Yanzu ki rubuta sunanyen mutanen kuma ki manta da mijinki? Teem Teem?�
Ta yi shiru tana murmushin da har dimple dinta ke lasawa saboda yadda ta samu guri in 3 months jikinta ya fara kyau, daman can abinci mai kyau ne babu da kuma kwanciya hankali.
“Zan rubuta fa sai aka kira sallah shi ne na tafi sallah sai ka dawo�
Ya kai bakinsa saitin kunnensa.
“Ban san ki da karya ba�