Sashe 42
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya Falmata ta sauke ta kalleta sau daya ta dauke kai ta nufi hnayar fita. Ina aka ganki yaushe kika dawo shine abunda kowa yake tambaya domin Tumba ta yada cewar wai dan Baba ya daketa shine ta ji haushi ta gudu, sai a lokacin ne wasu suke fahimtar Falmata bata ji sosai domin sai sun yi da karfi take jin abunda suke fada, shakku ya fara shiga zukatan mutane game da irin rikon da Tumba take mata, duk kuwa da kasancewar Falmata bata taba fadawa kowa matsalarta ba bayan kawarta Khadija, sai dai labarin da Tumba ta yada da kuma ganin Falmata ta dawo har ta fadi cewar kadeta akai ya ba mutane mamaki.
Babu wani abun kirki a cikinta kasancewar bata karya batun suka taso a gidan Momy kuma cornflakes kawai ta sha har yanzu bata jin jikinta da karfi, sai dai karfin zuciya da Sirleem ya sama mata a yanzu, ita kanta ta san dawowarta yafi tafiyarta a yanzu duk kuwa da irin wahalar da take sha.
A yau kam kallo daya zaka mata ka fahimci tana cikin farinciki da annushuwa, abun da ya dade be rabe ya ba. Ta shiga cikin gidan tana tsara yadda zata shimfida musu karyar da Sirleem ya koya mata. Kamar kullum yau ma gidan na cike da mutane kowa sai shanin gabansa yake, ita ma ta nitsa kai tana tafiya har ta isa gate din Ammy. Tana shiga ta ci karo da Iya tsaye ita da Zainab da alama wata maganar suke, wani irin faduwa gaban Falmata yai sakamakon ido hudu da suka yi da Iya har sai da kanta ya sara, addu'o'i ta fara karantawa tana kallon Iya wacce tai saurin dauke kai ta juya gurin flowers kamar ta rude ta fara taba su, Zainab ma ta lura da hakan sai ita a tunaninta Iya tana tsoron Falmata ne.
“Barka da yamma�
Falmata ta fada tana risinawa Zainab. Wani uban tsaki taja ta dauke kai ta nufi gurin mahaifiyarta.
“Wai tsoronta kike ji ne Iya?�
Iya bata yarda ta juyo ba sai da Falmata ta shige falon farko.
“Ba tsoronta nake ji ba, makircinta nake tsoro, domin zata iya zuwa tace na harareta, kuma tun da har ba ni da gata a gidan nan Ammy zata iya yarda wata kila ma ta koreni ta daga masarautar nan�
Zainab ta juya tana kallon falon da Falmata shiga kamin ta juyo ta kalli mahaifiyarta.
“Haba dai Iya, a yadda kike a cikin gidan nan har wata ta isa ta zo a kwana biyu tace zata saka ki tsoronta?�
Iya ta dafa ta.
“To ai ta fini gata ne Zainab�
“Kamar ya?�
“Kina tunanin ina da gadon sarautar gidan nan ne?�
Zainab ta girgiza kai alamar a'a.
“Kina tunani ni ko ke akwai wanda za a bawa gadon Mai Martaba idan ya mutu?�
Nan ma kan ta girgiza.
“Na isa na samu Ammy da wata magana da dauka? Tsawon shekarun da nai ina bauta musu?�
Zainab ta dan yi shiru.
“Eh ai wani lokacin ma Ammy tana neman shawararki a wasu abubuwan�
Iya ta yi murmushi tana girgiza kai.
“Karki yaudari kanki, tana daukar shawarata ne idan ta yi daidai da abun da take so, ban isa nace ga yadda za'ayi ba ayi sai dai yadda aka yi ni na bi, shiyasa kullum nake nuna miki hanya kin kasa gani, ina son na samu matsayin da zan iya cewa eh babu mai musa min, idan kuma na ce aa babu mai daga ido ya kalle ni balle yace dan me? Shekarun da nai ina bauta a gidan nan kar su tashi a banza�
Har Zainab ta bude baki tai magana sai wayarta tai kara, kiran Auwal ya shigo mota, murmushi ne ya kayata fuskarta ta amsa kiran da sauri daman abun da take jira kenan.
“Hello Baby�
“Na'am yakike?�
“Gani a waje�
“Okay ina zuwa�
Ta sauke wayar sannan ta kalli Iya cikin jindadi.
“Gashi nan ya zo, Iya ki je dakinki zai shigo ku gaisa�
‘Kin kuwa ja masa mutuwa�
Iya ta fada a ranta a fili kuma sai ta sakar mata murmushi ta gyada mata kai, sannan ta nuna ta da yatsa da fuskar dake nuna ba da wasa nake ba tace
“Tau na ji, amman zancen tafiyar nan a bar shi karki waiwayi garin nan�
Zainab wacce har ta juya ta juyo ta kalli Iya da mamaki a fuskarta.
“Ban gane kar na waiwayi garin ba, daman na taba zuwa ne?�
Iya ta daga mata hannu.
“Je ki tarbi bakonki zamu yi magana�
Zainab ta juya ta nufi hanyar fita tana sanye da doguwar rigar atamfa sai dan karamin mayafin dake kanta.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
03/12/2021, 09:21 - ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
UNCLE AA POV.
sai da ya fita daga Masarautar gaba daya yai nisa da ita ya tabbatar da babu mai jin abun da zai fada sannan ya sake kiran line, ringing daya Nana ta dauka sai ya marairaci murya kamar zai yi kuka, a zahirin ma zai ya kukan domin ya lura msarautar ba karama bace idan kuwa har ta tabbata ba zai yi driving din ba ai ba karamar hasara yai ba, sarki guda? Sarkin ma na Yola, ga yarsa da bata san zafin kudi ba.
“Nana na san kina son ki taimake ni ne saboda ni maraya ne, ba ni da uba ba uwa daga ni sai Yayata muka rage, kin ga wannan aikin da zaki sama min ba karamin taimako zaki yi ba, Allah kadai ne zai iya biyanki, kuma ni yanzu kin zama uwar dakina kuma uwata mai share min kukana, ban yi zaton za a hana ni aiki a gidan ku�
Nana dake zaune a falon baki tana jiran shigowarshi ta tashi daga kwancen da take.
“Miya faru�
“Ina shigowa na hadu da wata yarinya mai kama da bebin roba tace min wai ba za a dauke ni aikin ba, ba ki ji yadda na ji ba Nana, amman nasan ina da Allah, ina dake kuma zaki min gata ni kuma zan zama mai biyaya a gareki ba zan taba sabawa umarninki ba�
“Kana iya yanzu?�
“Na ma fita daga gidan na yi nisa kar ace na yi wani abun�
“Ka dawo yanzu gani nan fitowa�
Nana ta kashe wayar a fusace, wani irin dadi ne ya lullube shi.
“Allah na gode maka da ka hada ni da yarinyar nan Allah, Allah kasa ta rika jin tausayi na tana bani kudi, Allah sani bani da komai sai burge da wankan karya Allah ka min arziki ta hanyar yarinyar nan Allah�
Ya fada yana kallon sama, ya ci wanka kam iya wanka idan ka ganshi kamar dan wani shege, bayan ko har wuni yake da yunwa wani lokacin, juyawa yai ya nufi hanyar komawa cikin masarautar.
A fusace Nana ta isa Part din Hajiya, dan yana fadar mai kama da babin roba ta gane cewar Jurry ce dan tafi kowa rashin kiba a gida sai fari kamar zabiya, Hajiya na zaune tana tauna maganar Jarma wacce ta hanata sukuni ciki har da zancen tafiyar da babu dawowa wa zai yi tafiyar? Waye Sardauna waye Fadime balle kuma Falmata? Shigowar Nana yasa tai saurin daukar remote ta canja channel kamar da gaske kallon take.
“Hajiya kin ga Yaya Jurry ko? Wai ta kori driver na wai ba zai yi aikin ba�
Nana ta fada kamar ta fasa kuka, sai Hajiya ta mika hannu ta rikota.
“Jurry tace za a daukar miki sabon driver ko ni?�
“Ke�
“Then why maganarta zata taba ki? Je ki kira driver�
“Ya shigo yana harabar gida�
“To kije ki bashi key din, nawa ake biyan wacan?�
�35k�
“Wannan zamu ba shi 40k, zan kira Waziri na fada masa a saka shi a list�
Da sauri Nana ta rumgume Hajiya tana murna.
“Thank You Hajiyata I love you�
Sai da ta aje mata wayarta sannan ta fice daga dakin. Ta gate din Hajiya ta fito sai ta same shi kusa da gate din tsaye, tana kallonshi taji ya matukar burgeta saboda yayi wanka mai kyau, daman can kuma ko kallonsa tai nishadi take ji.
“Ka zo?�
“Eh�
“Na yi ma Hajiya magana tace za a baka 50k per month�
“Da gaske?�
Ba shiri AA ya zauna a dan simitin da aka zagaye fulawa da shi a gurin.
“To zan maka karya ne ko na taba maka karya�
Nana ta fada da dan fada fada, sai da yai kamar ya rama sai kuma ya tuna a inda yake sai ya dariya.
“Aa Hajiyata na gode sosai, yanzu na tabbatar da ke yar gata ce, amman sarkin ne Babanki ko kuma rikonki ake a gidan?�
“Ina ruwanka?�
Nana ta fada tana turo baki dan ita dai bata son yawan tambaya da bincike.
“Ba ruwana fa�
Ya amsa mata da sauri yana sosa kai.
“To bari na je na karbo maka makullin motar, amman nan ba gidan mu bane ka biyo muje gidan mu�
“To nan gidan su waye?�
“Wai ina ruwanka?�
‘Daga gani idansu wannan bebin robar ne shiyasa ta hana a dauke ni aiki dazun, kai no kila ma wanki take musu daman wadanda ba yayan kowa ba sun fi komai falako idan sun yi abu, ni ma nan da kwana biyu zan sayi mota ana fara budawa a gari�
Ya fada a ransa a fili kuma murmushi kawai yake yana kallon Nana wacce ta wuce apartment dinsu yana binta a bayata. A bakin gate ya tsaya ita kuma ta shiga ciki.
FALMATA POV.
sai da ta kusan minti ashirin a tsaye sannan aka bude mata kofar, sallama ce abun da ta fara yi sannan ta shiga cikin falo cikin tsoro tsoro kamar wacce tai laifi.
“Jekadiya tabo min yarinyar nan�
Wacce Ammy ta kira da Jekadiya ta kyafato Falmata da sauri tana nuna mata Ammy.
“Ku zo tare zan yi magana da ita�