Sashe 101
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gajiya da tai da zaman dakin yasa ta mike tsaye ta fara lalaben hanyar fitowa zuwa falo. Ta fara sabawa da yanayin gidan, domin ta san inda bandaki yake ta san yadda zatai ta fita daga dakin ko kuma ta shiga, ta kuma san ta inda zata bi ta fita kofar falon, sai dai ta saka saboda da mutanen gidan, ta ki ta saki jiki da su, babu ranar da bata kuka. Tun da Wasim yasa kafa ya tafi Zainab bata sake kula Fadime ba duk kuwa da kasancewar ya fada mata ta kular masa da ita, bata mata komai sai kyara, idan ta zauna a kujera zata ce mata ta sauka kasa, bata taba saka hannu ta rikata da sunan kaita bandaki ba ko kuma dakin da take kwana wanda babu komai a ciki sai tile, balle har ta dauko abinci ta bata, kwata kwata Fadime bata kwanta mata ba, jininta be gadu da nata ba. Abinci sai dai Iya ta bata, bandakin ma Iya ce ta nuna mata inda yake haka ma dakin da take kwana duk aikin Iya ne, ita kuma tana yi ne saboda Wasim, kwana ukun da sukai suna zuwa gaisuwar Labib kullum a gidan take wuni ita kadai da yunwa, har sai sun dawo sannan Iya ta dafa wani abu su ci har ita.
 Da lalabe ta fito falon har ta karaso inda kujerun suke ta lalaba karamar kujerar ta zauna, Zainab dake kwance a doguwar kujera rike da waya, ta cire Bluetooth din da yake dayan kunnenta tana shan waka tare da dakawa Fadime tsawa.
“Wai ke wace irin marar jin magana ce, bana fada miki ki rika zama a kasa ba? Tun da kika zo gidan nan baki yi wanka ba, kin bi sai lashe kujeru kike�
Fadime ta sauka da sauri ta zauna a kasa, idonta na cika da hawaye, ita dai bata sam Zainab ba bata taba ganinta amman ta fahimci ta tsaneta tun da ta zo gidan, bata mata komai sai kyara.
“Yunwa na ke ji, tun abincin safe ban sake cin komai ba�
“To ba a dora girki ba, ki ci wuta, ke dai kin cika damuwar mutane Wallahi Mtchssssssss�
“Yi hakuri�
Fadime ta bata hakuri a sanyaye, sai ta sake jan tsaki, ba tsanar Fadime ne kawai a ranta ba, har da gaskiyar data gano ta ita, duk da kasancewar har yau ba ta yi ma Iya maganar ba, abun ka da rashin kunya irin ta maye ita ma Iya bata ce mata komai ba, kuma ta wanyance sai harkokinta take, Zainab tana kara jin haushin Fadime ne saboda a ganinta da ace bata zo gidan ba, da yanzu bata ji mummunan labari ba akan mahaifiyarta, domin a yanzu ta rasa ta wace hanyar zata zauna da ita, gashi ta kasa samu natsuwa da iya duk dai ita dai bata san abun da ake nufi da maita ba, sai dai ta san ba abu ne mai kyau ba, kuma ta san tsafi ne. Sai dai abun da ya tsaya mata a rai kuma ta kasa tambayar Iya shine dalilin Iya na daukar maitar, da kuma boye mata asalinta na gaskiya.
 Bayan yunwa har da kishin ruwa Fadime tana ji sai dai jin alamar Zainab ce kadai a falon ta san ko ta fada ba zata bata ruwan ba, hakan yasa ta mike tsaye ta fara lalaben hawaye na bin fuskarta ta koma dakin, da lalabe ta shiga bandakin ta duka kasa tana lalaben buta dayar data fara dauka bata da ruwa, dayar ce da ruwa sai ta dauko mai ruwan ta kafa bakinta a kai ta sha mai yawa sannan ta aje, ta juyo ta fito.
Tashin Fadime yai daidai ta kwankwasa kofar falon da Mai gadin yai.
“Shigo�
Zainab ta fada daga kwancen da take, sai ya turo kofar ya shigo cikin girmamawa da taka tsantsan irin na bawan gidan da ubangidansa.
“Hajiya Wani ne ya zo da mota a waje yayi horn sau daya, sai na leka na ga motar da bakin gilashi na leka na ga ko waye be sauke gilashin motar ba, har kwankwasa masa na yi be bude ba�
Ya dago.
“Wace kalar mota ce?�
“Baka ce, Mai bakin gilashi�
Tana jin hakan ta gane Shattima ne domin shi kadai zai zo da mota a gate din gidan kowa yai wannan abun, ta san kuma a cikin motoci black ita ce fav dinsa, domin most of him cars duk black color ne sai dai designs da price ya banbanta.
“Bude masa gate da sauri Shattima ne�
“To ranki ya dade�
Ya juya da sauri ya fita jiki na rawa, ita kuma ta mike tsaye da sauri ta nufo kofar falon. Ko da ta fito Mai gadin ya bude masa gate din shi kuma ya kunno kai cikin gidan, a daidai inda take tsaye ya faka motarsa sai da yai minti biyar a cikin motar doing nothing sannan ya bude ya fito, tana ganinshi ta saki murmushi.
“Sannu da zuwa�
Be amsa ba har sai da ya rufe motar sannan ya nufi entrance din yana wata irin tafiyar kasaita da be san ma yanayi ba, biyo tai a baya har sai da ya shiga cikin falon yai makansa mazauni sannan ta zauna tana facing dinsa. Tana ganin yadda yai ignoring dinta ta san ta masa laifi ne. Yana zaune a gurin rike da wayarsa Fadime ta fito tana lalabe, da gangan yaki dago kansa duk da be san ko waye ba har sai dai tai kokarin zuwa kusa da kujerar da yake zaune.
“Wai ke miyasa baki da hankali ne? Ba zaki zauna a daki ki natsu ki zauna a daki ba sai kin rika saka mutane magana, ko kujerar nan kika taba sai na ci ubanki...�
Fadime ta tsaya cak.
“Yi hakuri dan Allah�
Ta furta tana jin wani irin rashin galihu da tausayin kanta, domin ta kai yau har ta zagi ubanta. Dagowa Shattima yai ya kalli wanda ake zagin sai yai arba da abun da be zata ba, mutuwar zaune yai yana kallon Fadime da tsananin mamaki marar misaltuwa, mamakin da be san yadda zai misaltashi ba, sai dai hakan be saka shi nuna ya santa ba.
“Who's this?�
Ya tambaya yana kallon Fadime data juya ta fara tafiya da zimmar komawa cikin dakin.
“Fadime ta zo zama ne kawai na kwana biyu�
“Zo ki zauna�
Ya fada still yana mamakin da be yarda ya bayyana a fuskarsa ba. Abun ka da mai nema sai ta juyo da sauri daman zaman dakin ya isheta saboda kadaici, sai dai taba zo ta zauna din ba sai ta tsaya.
“Tace na zo?�
Fadime tayi abun da yafi komai batawa Shattima rai, ya baka umarni kace sai ka jira umarnin na kasa da shi.
“Ni nace ki zo ki zauna?�
Ya fada calmly, hakan yasa Fadime ta kara takawa tana lalaben, ko bata umarni ba ta san wanda yai maganar ya isa da ita tun da har ya furta a gabanta. Sai da ta iso kusa da shi har yana jin kamshin turarensa daya cika falon ta lalaba kasa ta zata zauna.
“Zauna kam kujera�
“Tace na zauna hawa kan kujerarta fada take�
Ta zauna kasa tana jin kamar ta taba jin kalar kamshin turaren da muryar amman a ina? Zainab ta mike tsaye ta nufi kicin dan dauko masa lemu duk da ta san ba sha zai yi ba. Tashinta ya bawa Shattima damar tambayar Fadime.
“Yaushe kika zo nan?�
“Wanene kai?�
Ta kai hannu tana lalaben inda take jin muryarsa na fitowa. Sai ya kai bakinsa saitin kunnenta.
“Kin san mutumen daya kadeki da mota kika ce ya siya miki kaza da yogurt?�
Fadime ta zare ido kamar tana ganinsa tare da bude baki.
“Kai ne?�
“Eh�
Ya amsa mata yana murmushi kamar tana ganinsa.
“Kai kadai ne?�
“Eh ta shiga kicin�
Ta yi saurin riko kafarsa.
“Dan Allah ka taimaka ka kai ni wannan tashar sai ka saka ni motar garinmu, bana jin dadin zama nan, dakin ba komai haka nake kwanciya, kuma basu bani abinci sai na ji yunwa sosai yanzu ma yunwa nake ji, kuma kyamata suke yi ita wannan sai ta tai min fada ko ban mata komai ba, kuma tun da na zo ban yi wanka ba, bani da wasu tufafin canjawa kuma...�
Sai ta rage murya ta dogo kasa kasa kamar an fada mata Zainab ta fito daga kicin din da doso inda suke rike da lemu.
“Kuma tsohuwar gidan Mayya ce, wai ta cinye matan wani mutum kuma yanzu yayansa ta cinye wai shi take bibiya, kuma ina ganin ita ma yarta tana yi, dan Allah ka dauke ni kar su cinye min kurwa, bana son na mutu yanzu ka taimaka min ka ji�
Babu abun da Zainab bata ji ba, har wani dauke numfashi tai saboda kunya da rikicewa a lokaci daya, sai ta rasa me zata ce, domin a tunanin Fadime karya tai na fadar ta cinye matam wani mutum kuma yanzu ta cinye yayansa saboda ba a gabanta Iya ta fadawa Wasim hakan ba. Shattima kuma be ce uffan ba ganin Zainab din, hakan kuma sai ya bawa Fadime damar cigaba, domin ba ta yi tunanin Zainab ta dawo falon ba, hankalinta be bata ta saurara ta ji takun tafiyarta ba.
“Ko Wasim daya kawo ni cewa yai gata nan idan kin ga dama ki cinye idan kin ga dama ki aje, kaga kenan mayya ce ko? Dan Allah ka dora mu a hanyar garinmu kaji?�
Still Shattima be ce mata komai ba, sai hannu yai wa Zainab alamar ta zuba lemun data aje, ta mike tsaye tana jin jikinta kamar ba nata ba tsabar kunya kanta yayi mata kato ji take kamar kasa ta bude ta shige ciki. Ta duka ta zuba lemun a zaton Fadime shi ne yake zuba lemun, sai ta zuba ta koma ta zauna sai Shattima ya dauki lemun da kansa ya kama hannun Fadime ya saka mata glass cup din.
“Sha lemu�