Sashe 81
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Haka na yi niya daman, na fadawa Jarma a saki yaron, yau idan ya dawo zan masa maganar zuwa garin, kuma tun yau zan fadawa Mai Martaba cewar Hajiya Hansai bata da lafiya ina son naje dubata jibi, sai mu wuce kawai domin zama be gan mu ba, kin ga idan muka je ma sai su fada mana wacece Fadimen har ita din mu yi maganinta, tun kam ma ta shigo ciwon kan ya mana yawa�
“Eh haka ne, sai dai wani hanzari ba gudu ba, kin san Jarma be san da ni ba a lamarin nan idan ya san da ni za a tafi asirina zai iya tonuwa�
“Karki ji komai, ai ba fada masa zan yi cewar ga abun da zai kaiki ba, zance zaki rakani ne kawai, ke kuma sai ki fara shirinki tun yau�
“Eh tun yau zan fara, gobe zan bar gidan daman ina da zimmar yin yaji saboda auren nan, to daga gobe ma zan bar gidan na koma gidan Yaya Rakiya zan fada mata komai ta nan zan samu hanyar zuwa, domin na san halin Waziri wani irin murdaden mutum ne, ba zai nemi ba sai an kwana biyu�
Hajiya Babba ta kalli tsadaddin kulolin abincin dake gabanta tana fadin.
“Ni mamakina ta ina Sirleem yasan yarinyar nan? Har yana fadar wai ban san halin da take ciki ba?�
“Shine abun mamaki ai, amman dai idan muka je can ai zamu ji�
“Bari ma na kira Jarma tun yanzu�
Hajiya ta dauko wayarta ta lalabo number, bata dade tana ringing ba ya daga.
“Hello Hajiya, na fada musu a sake shi, gani nan a mota gani nan hanyar zuwa Masarauta yanzu�
“Tau yayi sai ka iso�
Ta sauke wayar tana wani kankance ido, irin na manyan matan nan dake cikin damuwa.
“Yace gashi nan a hanya, sai ki wuce kamin ya iso�
Hajiya Talatu ta mike tsaye da sauri tare da daukar jakarta.
“Kara na tafi kar ya tararda ni a nan kam, duk yadda kuka yi sai ki sanar min a waya�
Kai Kawai Hajiya Babba ta iya daga mata, ta maida dubanta gurin window dakin, abubuwan nan biyu sun tsaya mata a rai.
Hajiya Talatu bata dade da fita ba, Jarma ya shigo dakin da sallama, kamin ya zauna Jurry ta turo kofar dakin ta shigo ita ma, ta zauna kusa da Hajiya. Jarma ya zauna yana kallonta domin duk abun da suke be taba magana da Hajiya a gabanta ba sai dai idan ya tashi Hajiya ta labarta mata komai. Kamin Jarma yace komai Hajiya Babba ta kalleshi cike da damuwa ta ce.
“Jarma ina son zuwa garin mutanen nan jibin nan�
Jarma ya kalli Jurry kamin ya kalleta.
“Jibi fa kika ce Hajiya�
“Eh mana Jarma, baka ga halin da muke ciki ba? Ina da tabbacin mutanen nan ne kadai za su iya man maganinta, tun ba aje ko'ina ba mun fara ganin lalacewar shiri balle kuma nan gaba? Me kake tsammani? Daman kace sun fada Falmata Sardauna da kuma Fadime za su lalata mana shiri ga shi kuma mun fara gani tun yanzu, ba kuma lalacewar shirin ba tonuwar asiri wanda zai saka mu ji kunya�
Jarma ta sauke ajiya zuciya yana kallon Jurry, so yake yai magana kuma yana jin nauyinta domin be taba irin wannan maganar da Hajiya a gabanta ba, ganin yadda yake dari-dari da Jurry yasa Hajiya tace.
“Karka damu Jarma, Jurry ta san komai na san ka sani, tafiyar nan ma da ita za ayi da yardar Allah, ka sake jikinka kai magana�
“Hajiya kina ganin tafiya jibi jibin nan be yi sauri ba?�
“Ba wani sauri ni idan zan samu dama ma yau zan tafi Wallahi, yanzu haka ji nake kamar a kaya, idan fa mu ka yi wasa za mu ga wasa�
“Haka ne gaskiya, to ai ni bani da matsala, sai na fara shirina tun yanzu, ba ma sai mun je da wannan abokin nawa ba gudun kar ya ganki ko kuma ya gano wani abu, sai mu tafi kai tsaye a can Katsina din, in ya so kamin mu shiga garin sai na sami abokin wannan wanda yai mana jagora ya sake mana�
“Haka za'ayi, Juwairiyya zata siya mana tickets din jirgin Katsina, sai mu hadu a airport amman fa shirgar burtu zaka kai dan kar wani yace ya gan ni tare da kai�
“Haba Hajiya kamar ba ki san ni ba, na san yadda zan yi ai, sai dai matsalar kar sai mun sauka can wani ya fadawa Shattima ya gan mu tun da kin san a Katsina yake aiki�
“Ai ba shiga zamu yi cikin garin katsina mu zauna ba, kuma tun kam mi isa zan fadawa Hajiya Amutu ta sama mana mota mai bakin gilashi, ni idan son samu ne ai ranar da muka je Kt din mu isa garin mutanen washe gari sai mu dawo, har tickets din dawowa Juwairiyya sai ki siya mana, ni wlh na matsu na ganni garin mutanen nan�
“Okay ba matsala Hajiya, duk yau zan siya inshallah�
Cewar Jurry tana amsawa Hajiya Babba.
Jarma yayi murmushi.
“Wani abun ma sai kin je Hajiya, bokan nan makaho ne, amman zai karanta miki komai kamar gabansa aka yi, ni kaina sai da na tsorata da lamarinsu musamman yanzu daya kasance duk abun da suka fada shi ke faruwa�
“Hmmmm�
Shine kawai abun da Hajiya ta fada tana dauke kai.
FALMATA POV.
Tun da Sirleem ya saka ta a motarsa ta kasa magana sai hawaye take, kana ganinta ka san a rikice take, irin rikicewar nan ta mai gaskiya daya rasa abun fada, ga bakinta yayi mata nauyi ji take kamar an saka super glue and manne bakin. Driving yake ba dan yasan inda za shi ba, ko kuma inda zai kaita, abun da kawai yake ganin ya dace shine ta yi nisa da gidan for a while. Slowly yake driving din yana kallon fuskarta, the way da hawaye suke mata zuba sai yasa jin wani iri gashi ta kasa cewa komai tun da suka shigo motar.
“Falmata�
Ta juyo daker ta kalleshi still hawayen na sauko mata, har yanzu ta kasa yarda ba mafarki take ba.
“Ki ce wani abu mana, ko da ban dauka ba, kazafi tai min, ko kuma ki fada min yadda komai ya faru�
Ya fada yana kallonta, can kuma ya kalli titi yana tukin, tsoro yake kar bakinciki yasa ta kasa magana gaba daya, gashi bata wani ji sosai, wannan kiran da yai mata ma da be daga murya ba da na zata ji ba. A zahiri motoci da gidaje Falmata take kallo a badini kam tunanin yadda Baba da Umma zasu yanka namanta su soya shi shi ne, ko kuma su gasa ta da wuta, idan har ta koma musu gida da wannan labarin, ta dayan bangaren kuma tana tunani irin korar wulakancin da Ammy da Shattima za su mata, ta san ba zasu taba zama da ita ba tun da har aka samu yan kunnen Luma a dankwalinta. Sai a lokacin ne ta samu damar tausayawa kanta har ta fashe da wani irin kuka.
“Me na mata miyasa zata min haka, miyasa ta laka min sata? Yanzu Ammy ba zata yarda da ni ba, kuma Baba idan ya ji zai iya min wani abun ko Umma ta saka ya koreni�
Ta fada daker kuka n cinta yana taushe mata numfashi. Sirleem ya kalleta ya sauke idonsa har gudin wuyanta, damarar daya gani a wuyanta ya matukar burgeshi yana son mace da damarar wuya.
“Ammy tace wani abu ne?�
“Aa... Aa.. Amman na san zata kore ni ne saboda ba da izininta na tafi ba, lokacin da zan tafi ban fadawa kowa ba, kuma ya bani yan kunnen yara tace na daure a dankwalina ta kwance min dankwalin a gaban Ammy tace na saci na yan kunnen Luma, kuma Wallahi ban dauka ba...�
Ta kara fashewa da kuka. Kallonta ya sake yi, ba tare da ya ce komai ba ya dauke idonsa ya cigaba da tukin.
“Na taba yin irin wannan kukan da kika yi�
Ta kalleshi still tana ta rera kukan a hankali.
“Lokacin da na zabi yin sana'ar waka, a lokacin ban wuce 14 years ba, My Dad yace ba zan yi ba, ya rufe a daki, Hajiya ma tace ba zan yi ba, wai abun kunya ne a gurinsu ace ina waka ina dan former vice president? A daki nake wuni bana fita ko'ina sai idan school zan je duk wata hidima za'ayi ni ina daki a boye, Dad dina ya dauka hakan zai saka na cire rai da abun da nake so, ni kuma hakan sai ya bani damar rubuta wasu wakokin da yawa�
Ya dan yi murmushi.
“Na sha wahala fa kamin na kawo yanzu, saboda family na basa so a wacan lokaci, but look at me now! Siblings dina har cewa su ke ni dan'uwansu saboda su burge mutane ne, and before my father died shi da kansa ya bude min studio�
Ya karasa still smiling. Daga haka be sake cewa komai ba har ya isa gaban gate din Hajiya, ya saba faka motarsa waje, ya fita ya shiga cikin gidan, sai dai ganin Falmata bata da mayafi a jiki gashi rana ne ba dare ba yasa yai horn mai gadin ya bude masa gate, ya shiga harabar gidan ya faka daf da entrance din Momy har lokacin Falmata kuka take marar sauti. Sai da ya kalli Ameer dake tsaye entrance din rike da jakar laptop sannan ya kalli Falmata.
“Jira ni a nan zan fito yanzu�