← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 172

Sashe 95

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“I don't care, ko ka aureni ko na bata maka suna, ba zai yiyu na gina ka ba, wata karamar yarinya ta karbe min kai, you always telling Maman ka ce bata son aurenmu amman yanzu na gane ba ita bace kai, saboda kana soyayya da karamar yarinyar kuma har a cikin gidanku, and ba zai yiyu ace mamanka bata sani ba�

Mansura ta fada daga dayan bangare.

“Wow... Awesome... Haka zuciyarki ta raya miki? Kin manta waye Sirleem a gurinki? Yarinyar da kike dorawa laifi babanta auren dole zai mata so what's your problem?�

“You're my problem, idan ba ka rabu da yarinyar ba, i swear to God zaka ja mata matsala, ka san ni Sirleem�

“Yeah and you know me too�

Ya katse wayarsa yana mamakin yadda Mansura ta kasa masa uzuri.

After Sirleem ya fita daga kitchen din Momy ta dauki dankalin ta saka a fanfo ta wanke, sannan ta kalli Falmata.

“Matsa kusa ki ga yadda ake kunna gas din�

Falmata ta matsa kusa da ita sosai tana kallo har ta kunna, ta kashe sannan ta sake kunnawa.

“Kin ga yadda ake yi?�

“Eh�

“Good dauko kwai a firjin din can ki fasa min ki saka magi da yaji da albasa sai ki kunna wannn bangaren ki soya, ai kin iya soyar kwai ko?�

“Eh�

Momy ta bita da kallo, gaba daya rasa na zaba tsakanin burinta maganar Hajiya Umaima da kuma bijewa zuciyarta. Tabbas gaskiya Hajiya Umaima ta fada this is last chance da take da shi, this is the only hope da za tai fatan cika burinta? Amman a sirinsa ba tare da sanin Falmata ba ko kuwa da saninta? Idan ta sani zata aminta ne? Idan kuma tai mata a boya zata sake yarda da ita? Anya ya dace ya jefa rayuwarta cikin matsala bayan wacce take ciki? Ya zata kalli Sirleem nme zata fada masa? Wane hali zata kara jefa Falmata? Anya lokaci yayi da zata aikata haka? Yaushe ma yarinyar ta zo? Amman idan ba tai a yanzu ba sai zuwa yaushe za tai?

Haka ta jerowa kanta tambayoyi man da ta dora saman wuta yana ta soyuwa bata sani, ba, can kuma wata zuciyar ta bata amsa.

‘Duk abun da zai faru indai har na samu biyan bukata! Komai zai zo da sauki, zan dauki dawainiyarta zan tallafi rayuwarta, na yi mata duk abun da take so�

Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Falmata dake numa mata man yana konewa.

“Oh Sorry hankalina yana can wani guri�

Ta fada da murmushi a fuskarta, sannan ta fara zuba dankalin tana kallon yadda Falmata take soya kwan kamar daman can shi ne aikinta.

“Fulani baki yi karatu ba ko?�

“Eh ban yi ba�

“Kina son ki yi?�

“Eh amman yanzu ai a yi girma sosai�

“No ba a girma da karatu, zaki iya shiga a haka kuma idan kika maida hankali har jami'a sai ki je?�

“Jami'a? Karatun da ake zama likita?�

Maganar likita da tai yasa Momy ta tuna cewar ai bata ji sosai.

“Yes, Fulani yanzu kina ji da kyau ne?�

“Eh�

Ta amsa tana murmushi. Momy ma ta yi murmushi.

“Mashallah haka ake so, daman ina sa ran haka saboda maganin mai tsada ne kuma yana aiki sosai, Allah kara lafiya, sauran makaranta na nema miki ko?�

Falmata ta kalleta da sauri.

“Makaranta?�

“Eh ko baki so?�

“Ina so sosai ina son idan na ga abu na karanta ko na rubuta, ina so sosai�

“To zan nema miki inshallah, har jami'a idan kina so zan sama miki, ni ma kuma ina fata idan na nemi abu wajen ki ba zaki min ba�

“Me kike so Momy?�

“No ba yanzu ba, wata rana dai�

“Inshallah zan miki ko minene, ba zaki same ni mai butulci, ko dan Sirleem kin cancanci komai a gareni�

Momy ta mata wani kallo. Kamar tai magana sai kuma ya fasa ganin Sirleem ya dawo kitchen din.

“Baka wuce ba?�

“Eh yanzu dai zan wuce�

“Ba zaka tsaya ka karya ba?�

“No thanks�

Be tsaya jiran abun da zata fada ba ya juya da sauri ya fice daga kitchen din with so much confused. A tare Momy da Falmata suka hada breakfast din, sannan Momy ta saka Falmata ta jera masu a dinning, what Falmata thought Momy zata zuba mata nata dabam ne ta ce taje ta ci, but to her surprise sai Momy ta bukaci ta zuba da kanta wanda zai isheta kuma ta zauna a dinning din ta ci.
Duk wani abu da suka hadawa na breakf Falmata kadan take zubawa gudun kar Momy tace ta cika, beside ba a tana aje mata komai ace ta deba ba, ba a taba mata wannan gatan ba.

“Ki zuba mai isarki, idan sun kare kara siyowa za a yi, feel free ki ji kamar a gidanku kike, ni kuma ki dauke ni a matsayin mahaifiyarki�

Dagowa Falmata tai ta kalli Momy sai hawaye ya cika idonta, lallai bayan rasa uwa a yau ta samu wata uwar, Tumba na matsa mata tana musguna mata wata dabam bare tana son taimakonta. Momy ta shiga hada nata tea tana jin rauni a kudurinta, bata yi ma Falmata wannan gatan kadai dan tana tausayinta ba sai dan daman can halinta ne kawaici da girmama dan adam, gashi tausayin Falmata ya shiga zuciyarta yayi kwance.

‘Ina bukatar nai tunani, kuma ina bukatar shawara, kar na aikata abun da zai zame mana na nadama, kar na cutar da wata kuma na cutar da kaina, i need to think�

A ranta take wannna tunanin tana jin ya kamata ta nemi shawarar mijinta, domin har ga Allah bata jin natsuwa a abun da take tunanin aikatawa.

ZAINAB POV.

Zaune take bakin kofar shiga falon, tana sanye da kananan kaya, kanta sanye da wular sanyi, iska na kado mata a hankali.
A hankali murmushi ya cika fuskarta, kana kallonta kasan tana cikin nishadi da walwala abun da yai kaura a gare kwana biyu da suka wuce. Ta tattara hankalinta gaba daya ta maida akan system din dake gabanta, hotunan da ta dauka a garin su Wasim take kallo, al'adarsu na da kyau a gurinta, yadda suke rayuwarsu abun ya burgeta.

“Oh... �

Ta yi murmushi mai sauti tunawa da tai da abubuwan da suka faru, jinginawa tai jikin kujerar, ta kalli zaren da Wasim ya daura mata har yanzu yana a hannunta ta samu kanta da kasa cire shi, murzashi take a hankali tana tunanin abubuwan da suka faru a lokaci. Kamar an cikare ta sai ta tashi ta shiga cikin falon, kai tsaye ta nufi kitchen tana shiga ta dauko cup ta bude firji ta dauko ruwa, a kokarinta na rufewa ta hango Iya jikin icen abaya da be gama girma ba ta juya mata baya ta sirina a gurin. Mamaki ne ya kamata, me zai kai iya gurin? Ko maybe tana son shuka wani abu ne? Shine abun da zuciyarta ta raya mata, sai ta zuba ruwan a kofi ta aje gorar ta fito rike da kofin waje. A saman teburin data dora laptop dinta ta aje ruwan ba tare da ta sha ba ta zagaya ta inda Iya take. Kamin ta karasa Iya ta mike tsaye ta juyo rike da wuka, dayan hannunta kuma rike da tantabara har biyu. Tsaya tai cak kamar yadda Zainab ma ta tsaya cak tana mata kallon mamaki. Sai da tai da gaske sannan ta iya tattaro karfin hali da dakakkiyar zuciya irin ta maye ta cigaba da takawa tana furta.

“Ni har kin tsorata ni, tafiya ba sawu kamar mai sata�

Zainab bata ce komai ba har Iya ta zo ta wuce ta, sai ta juyo ta bita da kallo, abun da bata taba gani ba yau take gani a gurin Iya, ta yanka tantabara har biyu da kanta, me za ta yi da tantabara? Idan kwadayi take ji why not ta ce a siyo mata kaza? And when ma aka shigo da tantabaru gidan? Takawa tai ta bi bayan Iya tana tafe tana tunani har ta shigo cikin falon, sai ta ji motsinta a kitchen tana kokarin kunna risho, wani abun da ya bata tsoro bata bata saka ruwan zafi ba ta fige tantabaron a haka ta saka su a cikin wata roba, gasu yan kanana kamar wani karamin tsuntsu.

“Iya? Me zaki yi da tantabara?�

Iya ta kalleta.

“Me zan yi? Me ake da tantabara ba ci ba? Na yi kwadayinta ne�

“Amman kuma kanana haka? Kuma ki yanke da kanki�

“Ke bana son tambayoyin ki yau mace ta fara yanka? Wadannan yan tayin zan kira wani ya yanka min? Yaya ne fa! Ni dai ki saka a canja min abubuwan bandakin can bana jindadin amfani da su, kuma ki samo mai rika mana aikin gida�

Zainab bata sake cewa komai ba ta juya ta fita, Iya ta mike tsaye da sauri ta leketa, a zatonta dakinta zata shiga sai ta ga ta nufi hanyar waje, komawa tai ciki ta cigaba da gyara tantabarun.
  Zainab fitowa tai waje ta zauna, tana ta tunani domin bata gamsu da abun da Iya ta fada mata ba, me zai saka tai haka? Why zata siye kanana? Tunawa tai da tukunyar da ta gani a dakinta, sai kuma tai saurin girgiza kai domin bata son tai wani tunani marar kyau akan mahaifiyarta. Ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da duba hotunan wannan karon kan na Fadime data dauke ta a idansu idonta ya sauka, sai a lokacin ta tuna da ita.

“Ko tana ina ma?�

Ta tambayi kanta tana tabe baki, hakan nan take jin yarinyar bata mata ba, ta cika rawar kan tsiya. Ta mitsa sosai gurin duba hotunan tana gyara su amman hankalinta ya kasa kwanciya, ta kasa samu natsuwa da abun da Iya tai. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin gate din. Mai gadinta dake zaune rike da redio ta nufa, yana ganin ta nufo shi ya mike tsaye da sauri ya aje radio.

“Hajiya?�

“Ali kai ka tsiyowa Iya tantabaru?�

“Aa Wallahi ba ni ba ne�

“Ka ga lokacin da aka shiga da su?�

“Aa ban gani ba Hajiya, ai bayan kawarki da ta zo jiya babu wanda ya sake zuwa babu wand ya shigo�

“Okay�
Chapter 95 · 0% Book details