← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 172

Sashe 38

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata karasa ba ta ji muryarta ta zama kamar ta shanuwa saboda kara da munin sauti, da sauri ta rufe bakin ta fara hawa saman dutsen tana nemansa amman ko alamar sa bata gani ba, ta sauko a firgice ta nufi gida bata ko bi ta kan shanun ba.
Kamar wacce aka koro haka ta iss gida, Inna na zaune da Rammu Fadime ta shigo gida babu ko talkami.

“Ke lahiya Fulani abun ya tashi kuma?�

Har ta bude baki tai magana sai kuma ta rufe bakin ta fara mata na kurame, tana nuna mata bakin nata. Inna ta taso da sauri tana fadin.

“Bude na gani�

Ta hangame bakin tana hawaye kamar ba ita ba.

“Ke babu komi ciki Fulani ya kai ne wai?�

Bata son ta yi magana Inna ta ji murya, ita kanta tsoron muryar take dan ji take kamar ba a bakinta take fitowa ba. Babu juyin duniya da Inna ba tai ba amman Fadime ta ki magana sai dai tai nuna. Shanun ma Hajjo aka tura ta dawo da su gida, hankali Inna duk yabi ya tashi, a zatonta Fadime ta daina magana ne, gashi ita kadai cikin gidan dan Amo bata nan kuma bata son kiran makota kar Bappa ya dawo ya hau ta da masifa, tun da komai cewa yake sirrinsu ba sai wani ya ji ba.

Sai daf da magarina Bappa ya shigo gidan da yar tsarabarsa, daman a duk lokacin da yaje burni ya dawo sai ya musu tsaraba, Bappa irin mazajen nan ne da basa son shigowa gida hannu sake. Sai dai tashin hankalin da ya tarar a gurin amaryarsa ya kawardar komai, domin kuka ya tarar tana yi kamar yadda Fadime ma take kuka. Bappa ya nufo Fadime cike da mamaki da kuma tsoro a lokaci daya.

“Fulani ba zaki iya magana ba?�

Kasa cewa komai Fadime tai sai hawaye take, tsoro take kar tayi magana ta sake jin murya, ga kuma tsoron Bappa kar yace zai kira mai karatu ko ya daketa.

“Zan iya�

Ta fada da muryarta mai ban tsoro, gaba daya Bappa jin yai kamar muryar ta cika duniyar nan gaba daya, be san lokacin da ya jefar da kayan hannunsa ba ya riko rigar Inna wacce ta kusa wuce da gudu ya dawo ta ita baya ya kara ma kafarsa giya.

FALMATA POV.

Tana zaune ya turo kofar dakin ya shigo hannunsa rike da takeaway da robar ruwa, mikewa tai tsaye da sauri tana kallonsa, kallo daya yai mata ya dauke kai ya aje mata abincin ya fice. Bata bukatar ya fada ci zata yi a yadda take jin yunwa ko da guba aka saka a abincin zata iya cinsa. Naman kazar ta fara cinyewa rabon da ta ci nama har tun na sallah, shimkafar ma sai ta ji kamar ta fi ko wace wane abinci dadi saboda bata cin abinci mai dadi a gida.
Ruwa kan kadan ta sha saboda ta riga ta cika cikinta da ruwan fonfon da ta sha na bandaki. A maimakon ta hau saman gadon ta kwanta sai ta kwanta a kasa, tana ta kallon pop bachin yace mata ba dai shi ba, yadda ta ga rana haka ta ga dare, babu komai a cikin ranta tunanin kudin Tumba data taba idan ya maida ita gida yace guduwa tai ta san Baba zai iya saka wuka ya yanka ta ne, wasa wasa ta ji ana kiran sallah asuba, kamar yadda tai a jiya haka ta shiga bandakin tai alwala ta fito ta sake shimfida dankwalinta tai sallah. Tana cikin addu'a Sirleem ya turo kofar dakin ya shigo. Tea mai kauri ya aje mata da bread sai sake mikewa tsaye kamar dazun tana kallonsa.

“Dan Allah karka maida ni gida�

Uffan be ce mata ba, daman kuma be da niyar ce mata komai yana aje mata tea ya juya ya nufi kofa.

“Wallahi idan ka maiyar da ni Baba ya ji cewar na gudu sai ya yanka ni, kuma Umma sai ta kusa kashe ni saboda na taba mata kudi�

Daf da zai fice ta fadi haka, sai ya tsaya cak ya juyo ya kalleta, tausayinta ya kama shi how old she is da zata zabi guduwa da bar gidansu? Ko bata fada masa ba ya san ana azabtar da ita tun da har ta zabi barin garinsu da gidansu ta zo inda bata san kowa ba, amman rayuwarta yake ji kar ta aikata irin abun da Mansura ta aikata ya zame mata tabo, a kurciyarta zata iya lalata rayuwarta, amman idan tai hakuri da wahala zata ci riba kuma zata wuce kamar ba ayi ba.
Juyawa yai ya fice daga dakin, ita kuma ta zauna ta fara kuka tana tunanin irin mugun dukan da Baba zai mata, bata tunanin zai barta ta rayu ma idan ko har ta rayu to sai dai ta zama musaka.
Misalin 6:30 ya sake turo kofar dakin, ya tsaya daga jikin kofar yana kallonta, ya same ta a yadda ya fita ya barta, tana kuka kuma bata taba tea ba.

“Fito muje�

Mikewa tai tsaye ta nufi kofar hawaye na sauko mata kamar dan irin wannan ranar kawai ta tanade su. Bata ce me zata ce masa ba, tun da har ya kasa sauraranta ta san ba zai fahimce ta ba, a yanzu ba ta da wanda zata karantawa damuwata balle ya nade mata kuncinta. Ta yarda a gidansu bata da gata, a nan din ma bata da gata. Da kanshi ya bude mata gidan gaba ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa ya ja motar.

Tun da ya fara tafiya wata kalmar bata shiga tsakaninsu ba, daji take kallo tana share hawayenta lokaci zuwa lokaci, ta sadakar kuma ta yardar da kaddarar da ta rabo da gida, ta yarda wata kaddararce take bibiyarta a yanzu na fadawa wata damuwa. Tun yana tukin tana kallon titi har bachi ya sallama mata ita kuma ta amsa masa cikin sauki, daman tun jiya basu hadu ba. Sai da ya tabbatar da bachin nata ya yi nisa sannan ya faka motarsa gefe ya fita ya zaya gefenta ya bude mata a hankali kwantar mata da kujerar ya rufe, kamin ya dawo motar ya ciro wayarsa ya kira Mansura bugu daya ta dauka.

“Sirleem ina yarinyar nan ta kwana?�

“Tun jiya na saka ta a motar Yola�

“Ina ta kiranka baka dauka ba tun jiya, kuma ka san zan samu�

“Shiyasa na kira ki yanzu�

Ya fada yana kallon Falmata ta cikin farin gilashin motarsa, bachinta take hankali kwance kamar wacce bata da damuwa. Ta saka hannu ta share hawayen idonta.

“Kana ina kai�

Ya daga kansa yana kallon katon dajin.

“Somewhere.... Anjima zan kira ki�

Be jira cewarta ba ya yanke wayar ya maida aljihu ya zagaya ya shiga motar ta cigaba da tukinsa. After every deep breath sai ya kalli Falmata wacce ke ta ranko bachi har ya shiga garin Yola.
Kai tsaye ya nufi GRA, a gaban wani katon gate ya faka motarsa sannan ya fita ya doshi gate din yai knocking, babu bata lokaci mai gadin ya leko.

“Ranka ya dade kai da kanka kake buga gate�

Sirleem ya dan yi murmushi.

“Allah yasa Momy dai tana ciki�

“Yanzu yanzu ko ta dawo�

Mai gadin ya fada yana matsa masa daga kofa. Sai da ya danna key mota yai ta shiga lock sannan ya shiga cikin gidan. Kato gida mai yanayi da na turawa domin babu hayani sai kukan tsuntsaye dake saman itatuwan da suka zagaye harabar gidan su kai masa ado, ga wasu manyanna alfamar. Entrance din ya hau ya isa gaban kofar yai knocking.
Wata kyakyawar mata ce ta bude masa kofar fuskarta dauke da murmushi matar zata yi 40 to 42 years tana sanye da farar atamfa, sai farar t labcoat dake saman atamfar.

“Celebrities ganinku sai da ticket, sai kuma idan kun so kawo ziyara�

Dan murmushi Sirleem yai ya naso kafarsa cikin falon mai cike da sanyi ac.

“Ba ma ziyara na kawo ba ni alfarma na zo nema�

“To yau kuma a gurina�

“Na san ke kadai zaki min ai�

Ya fada yana kokarin zaunawa.

“Yanzu yanzu na dawo daga aiki, lemme go and change�

Sai da ta aje masa lemu da ruwa sannan ta nufi upstairs ta shiga dakin farko. After like thirty minutes ta fito sanye da Hijab din dake nuna alamar sallah ta gama, sai da ta sauko kasa ta zauna sannan Sirleem ya kalleta yace.

“Wata yarinya ce na hadu da ita a Kaduna, ban ji labarinta ba amman a yadda na fahimta tana shan wahala ne a gurin rikon nata ko gurin Babanta, saboda tace min mamanta ta rasu, kuma ta gudo ne daga gidansu zuwa Kaduna, bayan kuma bata san kowa a can ba, so idan na kyale ta a can rayuwarta zata iya lalacewa shiyasa na zabi dawo da ita gida saboda yar nan Yola ce�

Iya nan ya tsaya yana sauke numfashi a hankali, tun kamin ya gama labarta mata abubuwan ta soma jin tausayinta.

“Allah mai iko ina yarinyar take?�

“Muna tare a mota, ina son kije gidansu ne tare da ita, ki ce ke kika kadeta kuma hankalinta ya gushe sai yanzu ta farko ta fadi gidansu kika kawo ta, saboda ta nuna min idan ta koma gida Babanta ya ji cewar ta gudu zai yankata, kuma ta taba kudin ko waye i don't know zan tambaye ta kudin sai na bata�

“Allah mai iko, wasu suna neman haihuwa wasu kuma suna wulakantawa�

Momy ta fada cikin rashin dadi rai, Sirleem yayi murmushi yana kallonta cike da tausayinta, kamin ya mike tsaye.

“Bari na shigo da ita�

“Okay�

Fita yai daga falon, ko da ya isa gurin motar ya tararda ta farka tana ta kalle kalle, unlock din motar yai sannan ya bude side dinta.

“Fito�
Chapter 38 · 0% Book details