← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 172

Sashe 140

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Sirleem karka bar ni dan Allah, idan ka tafi ban san ya zan kasance ba, kai ka kadai ne gata a yanzu kai ne rayuwata...�

Ta fada tana jin wanin irin yanayi da bata taba jin kanta a ciki ba, idonta har wani hayaki suke.

“Ni kuma mahaifiyata ita ce rayuwata, ba zan iya jabar ki na bar mahaifiyata ba, ban taba ganin Hajiya a irin halin da na ganta a yau ba, ba zan jama silar bakincikinta ba...�

Ya saka dayan hannunsa ya banbanre hannunta da ta rike hannunsa na dama da shi, ya fice daga dakin cikin sauri. Faduwa tai kasa tana wasu kalar hawaye masu zafi da kona fuska sai ta matse jikinta ta rumgume kanta tsantsa, ta sauke idonta akan hoton mahaifiyarta.

“Ma... Ma... Ma... Mama...�

Ta furta daker muryarta na rawa, wani irin abu ta ji kamar zuciyarta zata kone mata kirji, faduwa tai durkushe ta kasa yarda Sirleem ya rabu da ita a lokacin da ta fi tsananin bukatarsa. Mikewa tai tsaye ta fita dakin da gudu, yadda ta sauko downstairs din ma sai da ya ba Momy tsoro kamar zata tashi sama haka ta nufi kofar falon ta bude, ta bi motar Sirleem dake kokarin fita gate tana wani irin kuka tana kiran sunansa.

“Sirleem.... Sirleem.... Sirlee....�

Bata karasa sakamakon shakewar da muryarta tai sai ta fadi a harabar ta fashe da matsanaicin kuka. Momy ta fito da sauri ta yo kan Falmata ta kamata.

“Lafiya?�

Kamar mai jira sai ta juyo da sauri ta kama hannayen Momy ta rike gangam.

“Momy ya sake ni, Sirleem ya tafi ya bar ni dan Allah Momy ki ce ya dawo...�

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un�

Momy ta furta cikin rudani da rashin fahimta. Sirleem ma tukin yake yana hawaye yana jin jikinsa kamar ba shi ba numfashinsa har kokuwa yake da shi.

Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number   08032350261  banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa ,tana saida kayan gyara kamar su Al'ajabu,shu'umar humra wannan inbakida aure Bama saida maki,hadin kaza me yasin,akwai na mallaka wanda wannan ana rubuta shi atafin hannu ke zakiyi wannan,turaren wuta,kulacca,da sauransu
Mazauninsu nanan a samaru Gusau Zamfara state
Muna aika kaya kowace jaha da wajen kasar nan cikin aminci da yardar Allah kunememu kusha mamaki

https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*

Tana yunkurin ta tashi sai ta ji cikin ya mata nauyi kamar an jefa mata katon dutse a ciki, da farko ta yi tsammanin ko dan ta cinye naman ne duka duk da ta san bata saba haka ba, ko mugun ci tai yana da wahala ta gagara tashi. Jinginawa tai da gadon tana dan hutawa na mintuna kamin ta sake yunkura ta ji ya fi na dazun nauyin gashi ba ciwo yake mata ba. Kallon cikin tai da mamaki yana da da girmansa kamar da, amman ya mata nauyin da bata isa ta mike tsaye ba. Hannunta ta kai ta bude rigarta tana duba cikin.

“Aa wai ya haka ne?�

Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsa, sai kuma ta rufe cikin ta sake mika dukan karfinta ta yunkura ta tashi nan ma ta kasa, ta sake yunkurawa a karo na hudu nan ma dai ta kasa tashin.

“Ma ke faru da ni?�

Ta sake tambayar kanta, kamin ta sake yunkurawa sai ta ji nauyin ya sake karuwa fiye da dazun ma, shiru tai tana ta tunanin dalilin faruwar hakan a gareta bayan taba taba hakan ba, sam ba ta kawo cewar saboda ta ci kurwar Maijidda ba ne, har sai da ta ji kankarun dake cikinta na maita sun fara mata motsi, a firgice ta kai hannu ta dafa cikin tana zaro ido.

“Miye haka kuma? Miyasa na ke jin haka yanzu yanzu?�

Kadan kadan suke motsa mata sai kuma su tsaya, sau uku suna mata wasa a ciki sannan ta ji abun ya tsaya mata, a nan ta sake yunkurawa da dukan karfinta sai gata ta mike a tsaye nauyin da take ji duk ya daina ta koma normal kamar da, sai dai mamaki be bar ta domin bata taba yin haka ba kuma bata yi tunanin akwai wani abu da zai saka ta tai haka ba.
  Kwantawa tai saman gadon tana ta tunani kala kala, wata zuciyar na raya mata wata kila iyayen Maijidda sun bata magani mai karfi ne ta sha bayan ta kama kurwarta shiyasa ta ji haka, wata kila kuma wani izon ne akai mata, da wannan tunanin bachi yai gaba da ita, ta kwashi bachinta mai dadi har sai da ta hatse bata barka ba sai kusan la'asar, kamar wanda ta tuna wani abu haka ta sauko saman gadon da sauri.
  Bandaki ta shiga tai wanka da ruwan sanyi duk da kasancewar akwai sanyi sanyin hadari a garin, tana fitowa bata ko tsaya shafa komai bata saka wasu tufafin ta dauki tsohon gyalenta ta yafa ta saka talkami ta fito ta shiga dakin Zainab. Kwance ta same ta ruf da ciki tana ta aikin kuka.

“Wai ke yaushe za ki daina kukan nan ne?�

Zainab ta dago ta juyo tana kallonta da idanuwanta da sukai ja sosai saboda kuka.

“Babu rana, domin babu ranar da bakincikin nan nawa zai gushe, dan haka babu ranar da wadannan hawayen za su tsaya�

Iya ta tabe baki tana mamakin yadda Zainab take son wahalar da kanta.

“To idan kin gama kuka sai ki ta tafi gidan Waziri ayi gaisuwa da ke�

Zainab ta tashi zaune da sauri tana kallon Iya cike da mamaki.

“Waya rasu?�

“Maijidda yar wajen Hajiya Talatu�

Baki sake Zainab take kallon.

“Maijidda matar za a aurawa Shattima? Yar wajen Baba Waziri?�

“Ita fa, rai yai halinsa kin san kowa da lokacinsa�

“Waya fada miki ta rasu?�

Iya ta dauke kai ta juya ta fita ba tare da tace komai ba. Zainab na ganin hakan tai saurin saukowa saman gadon ta biyo bayanta

“Hakan na nufin ke kika kasheta kenan?�

Iya ta juyo ta kalleta.

“Duk abun da zuciyarki ta raya miki ki dauka shi din ne, domin ba zan iya wanke kaina daga zarginki ba�

“Ba zargi na ke ba, na san ai ke ce, amman ban yi tsammanin za ki sake aikata irin wannan abun ba, ko dan halin da na shiga, ammn hakan be dame ki ba, bayan duk zargi da kyamar da aka fara nuna mana? Kuma yanzu duk wannan be dame ki ba? Har zaki iya takawa ki je musu gaisuwa? Iya ke wace irin halittace?�

Zainab ta karasa cikin kuka.

“Idan ban tafi ba ai su ma sai su zarge ni kamar ke, kara na shiga ayi komai da ni, na watsar da komai nawa yanzu babu ruwana da wani Shattima balle danginsa har ta kai ga matar da zai aura, idan kim ga dama ke ma ki zo ki musu gaisuwa, domin babu ruwan Hajiya Talatu da abubuwan da suka faru bata mana komai ba�

Zainab ta share hawayenta cikin wani irin bakinciki da takaici marar misaltuwa.

“Ba zan zo ba, kuma ba za ki dawo ki same ni ba�

Tana kaiwa nan ta juya ta shige dakinta, Iya kam bata ce komai ba ta saka kafata ta fice daga gidan, a tunaninta Zainab ta yi hakan ne kawai saboda ta hana ta tafiya. Jikin window Zainab ta tsaya tana kallon Iya har ta fice daga gate din da mai gadin ya bude mata.

“Ya isa haka yanzu kan, komai ya kare�

Ta juya cikin damuwa ta fice daga dakin ta shiga dakin Iya, wardrobe dinta ta bude ta soma bincikar kayanta har ta kai gurin atamfar da ta nade tukunyar tsafinta ciki, dauko dankwalin tai ta bude ta fiddo tukunyar tana kallo jikinta sai rawa yake, sai da ta hade yawu sannan ta dora tukunyar a saman gadon Iya tana ta jin tsoro. Can kuma ta tashi ta nufi wardrobe din tana ta kara dubawa ko zata ga wani abun, sai da ta zazzage komai na ciki ta duba bata ga komai ba, sai ta koma gurin da take yan komatsanta wato karkashin gadonta ta soma janyo abubuwan da suke nan, yawanci duk kayan cin abinci ne sai yan ledodi da talkalmi, mikewa tai tsaye ta dage katifar ta yadda zata ga komai, sannan ta dawo tana ta bude bude kwanonon, har ta bude kwanon da Iya ta zuba naman Maijidda a ciki, ganin maskin yasa ta dauka ta shinshina tana mamakin na inda ta samu nama domin ita har yau bata san ta kan maitar ba balle ta san Iya na cin kurwa ne, a tunaninta kashewa kawai take. Aje kwanon tai ta bude wani babu komai a ciki ta sake budewa shi ma wayam, hka ta rika budewa duk wani abu mai murfi ta kai ga kitsen da iya ta aje, shi ma shinshinawa tai ta aje tana mamakin inda ta samu nama ta soya ta cinye ba ta bata ba, bayan bata saba mata haka ba. Hannunta ta kai ta bude kwaryar dake rufe da faifai sai tai arba da aci balbal a ciki na gwangwani sai tsohuwar kaya da allurar, allurar ta fara dauka ta duba zuciyarta na raya mata cewar wata kila iya na tsafi da ita ne, sannan ta dauko kayar ita ma ta duba har ta yi baki sabar tsufan da tai.

“Me take da wannan abubuwan kuma?�
Chapter 140 · 0% Book details