← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 172

Sashe 138

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya amsa mata yana bude motar ya fita, sai ita ma ta bude ta fito tana mamaki kato gida kamar wannan ga tsari da kyau kamar gidan minister. Yana gaba tana binsa sai kalle kalle take gaba daya ta zama bakauya har da kai hannu ta shafa fentin da take ganin yana ta wani haske. Bata kara raina kanta ba sai da suka shiga cikin falon, kamar yar gida haka ta zama domin ta riga Muhseen isa gurin kujeru sai dai bata zauna a kai ba ta zauna a kasa ganin manyan kujeru ne na alfarma, Muhseen kuma ya zauna a daya daha cikin kujeru kamin yai mata magana yace ta taso ta zauna akan cushion dina, har ta mike tsaye ita ta zauna akai tana kallon fuskarsa ta ga ko hanata zai yi ko kuma yace ta sauka, haka ta daga kai tana ta kallon falon mamakin duniya ya cika ta, irin gidan da bata taba gani ba yau ga ta a ciki.

“Ku nawa ne a nan gidan nan?�

Ta tambaya tana mamakin katon gida kamar wannan ace na mamansa ne, Muhseen ya nuna mata Mama Fulani da ke saukowa rike da tissue da alama hawayen mutuwar yar kanenta be tsaya mata ba har yanzu. Fadime na ganin Mama Fulani ta san ba irin iyayen nan ba ne masu daukar nonsense ga ta da jikin dake nuna arzikinta a fili tufafin jikinta ma kadai sun isa shaida. Saurin sauka tai ta zauna a kasa tana gaishe ta tun kan ta karasa saukowa.

“Sannu da zuwa Ina wuni�

“Lfy Kalau Yasmin�

Mama Fulani ta amsa sannan ta nufo kusa da Muhseen ta zauna, har lokacin bata kura Fadime na gani ba, domin hankalinta be kai kanta sosai ba.

“An dubata ta?�

“Ba zancen dubawa yarinya ta tashi�

“Kamar?�

Ya nuna mata ita, tana kallon Fadime sai Fadime ta sakar mata murmushi, Mama Fulani ta kalli Muhseen ta sake kallon Fadime.

“Tana gani kenan?�

“Ba gani kadai ba har komai ta tuna�

“Magani kuka bata?�

“Aa...�

Ba karamin mamaki ne ya kama Mama Fulani ba, da Muhseen ya labarta mata abun da ya faru, can kuma ya tsakuro daga labarin da Fadime ta bashi ya samman Mama Fulani inda be yi daidai ba Fadime ta gyara masa, daga nan ya sakar mata linzamin ta labartawa Mama Fulani komai. Kamar almara haka Mama Fulani ta ji abun mamaki da al'ajab suka rufeta lokaci daya.

“Ashe ita take cinye mana zuri'a? Ba sididi ba sadada daga gamon tsintsiya da zagga? Ban zumuntar uwa ba ta uba take mana wannan sherin ba duk abun alherin da aka mata?�

“Ita da yarta mayyu ne, har yar mayya ce�

Fadime ta fada tana tsina fuska domin ita har ga Allah ta dauka Zainab mayyace.

“Lallai kuwa ai biri yayi kama da mutum, tana zaune a gida tana cinye mana zuri'a ko wannan ma waya sani ko ita ta cinye ta tun da Waziri ya fada min ya bawa Shattima ita? Tabbas ita ce ita Ammy ma take ne Fisabilillahi? Wace iri mata ce wai? Ta san da wannan ta zuba bata yi komai ba? To Wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa, Allah ya kai ni Yola gobe lafiya Na rantse da Allah sai Iya ta bar garin nan, ta koma can inda ta fito, ba dan ma guduna alhaki ba ba zan barta da rai ba�

“Ashe ma ba ma yar garin ba ce amman yarta har wulakanci take wa mutane tana cewa kar a hau mata a kujeru ta barin mutun ya kwanta ba ko abun lullubi�

Fadime ta fada tana tuna abun da Zainab tai mata. Sai Mama Fulani ta biye ta kamar mai fira da sa'anta.

“Ba yar nan ba ce, waya san ma inda ta fito wata kila maitar tasa aka rokota ta zo nan ta lake har suke mata gata, amman shi Mai Martaba ya san da wannan zancen?�

“Wai daman shi Sarkin yana da rai? Ai na dauka ya mutu saboda wannan matar Hajiya Babba ta tafi tace a kashe shi kashe Shattima...�

Fadime ta fada tana kallon Mama Fulani da ta mike tsaye tana nuna ta, Muhseen ma gyara zama yai yana mata wani kallo.

“Keeee idan kika min karya sai na saka an yankaki an daddatsa namanki an zubar ni nan Fulani ba uban da isa yai komai�

Fadime ta sako mata ido hantar cikinta na kadawa, Mama Fulani dai ba tai mata kama da mayu ba, duk da kasancewar gidan yana mata kama da na masu yankan kai, to amman me ya kawo maganar yanka da daddatsewa daga bada labari, ta fara kuka.

“Na shiga ukuna�

“Ba wani kin shiga uku fada min gaskiya, ta ya akai kika sani...?�

“Zan dafa miki qur'ane kuma na yarda ki kira Shattima ki tambaye shi Wallahi ba karya zan fada miki ba�

Maman Fulani ta koma ta zauna tana kallon Muhseen da ke kallon Fadime. Tun daga salsalar zuwa garinsu Wasim har zuwan su Hajiya Babba da duk abubuwan da suka yi har kawowa zuwanta gidan da yadda ta labartawa Ammy komai sai da ta fadawa Mama Fulani. Mama Fulani bata san lokacin da ta daki kirjinta ba ta sake daka har sau uku.

“Dan'uwan nawa za a kashe? Ita Hajiya Balki rashin imaninta har ya kai haka? Akashe shi a kashe Shattima? Yanzu ita Ammy ta ji duk wannan abun amman ta share take zaune ta saka musu ido? Ko kuma ita ma asirin suka mata da bata iya komai? Ba zan dauka ba, na san dai na yi rashin mutunci a baya ammn ban yi rashin imani kamar na wannan matar ba, mijinta na sunna? Saboda Sarauta? No wonder ciwo yai ma Mai Martaba yawa, Mata ta yi yan'uwa su yi jamar'ar gari su yi, ba ma wanda zai fi kamar n matarsa tun da dole ne ta bashi ya ci, ai dole ne gobe Mai Martaba ya ji wannan maganar kuma dole, za ki iya maimaita wannan maganar a gaban kowa ko?�

“Eh Wallahi zan iya�

Fadime ta fada with full confidence. Mama Fulani ta mike tsaye ta nufi upstairs sai bala'i take.

“Kuma Wallahi Nana ba zata auri danta ba, muguwar mata kawai mai bakar zuciya...�

Sai da ta wuce Muhseen ya baro inda yake zaune ya motsa kusa da Fadime ya kai hannunsa ya kama lebenta yana ja.

“Kin gani wannan bakin na ki, zai kai ki ya baro, daga ganin ki na san zaki yi surutu, i wonder how Shattima ya zauna da ke shi da baya son hayaniya, kin ga yanzu kin takalo wata fitinar Mama Fulani ba zata kyale wannan maganar ba, kuma at end idan karya kike kin jefa kanki a matsala ko ma da gaske ne, za su iya wanke kansu ke ki kwana a ciki, kin san waye Hajiya Babba kuwa? Wannan bakin na ki wata rana sai ya yanka ki, wata kila shiyasa akai miki wani asirin aka kawo ki Abuja aka mantar da ke komai�

Wani tsoro ne ya kama Fadime jikinta ya fara rawa.

“Kenan yanzu ni za a jefa a matsala?�

“Ban ce kuma, amman ki san irin maganar da kike fada, kin ga Mama nan bata saurarawa kowa kan nata, ina tunanin ma yanzu waya ta je ta kira, kin ga kin ta da rigima a gidan Sarauta, sai an zo gurin magana ganki yar ficika ba wani auki�

Fadime ta taba jikinta tana jin wata zababbbiyar yunwa na taso mata.

“Ni yunwa ma na ke ji�

“Wato har yunwa kike ji? Duk baki ga abun da kika yi ba hankalinki kwance ko?�

“To ni wai ina ruwana ba su suka je suka yi ba, dan na fada kuma sai ya zama laifi, ma na Taimakawa Mai Martaba ban ai sai a karramani�

Ta fada tana turo baki gaba, tsoro dai kam ta ji shi, amman sam bata ga laifi a abun da tai yi ba. Muhseen yayi murmushi yana kallonta kamar yadda take kallonsa da fararen idanuwanta.

SHATTIMA POV.

Shattima ya kalli Ammy bayan sauke wayar da yai a kunnesa.

“Fateema ce wai an ganta a Abuja hannun Muhseen�

Ammy ta kalleshi duba irin na mamaki duk da kasancewar bata cikin yanayin dadi, bata damu da hawayen da ke fuskarta ba ta ce.

“Wane Muhseen din?�

“Na Mama Fulani�

“A Abuja kenan?�

“Eh ina tunanin abun da nai ma Hajiya Karama ne yasa ta janye kudirinta a kan Fateema, ita kuma mahaifiyarta ta kashe Maijidda�

“Ba ka da tabbacin yarinyar ta bata ne saboda Zainab, sai na ke jin kamar babu sa hannunta a ciki, kuma be zama lallai dan Maijidda ta mutu ba ace Iya, domin Waziri ya fada min asibiti sun ce tafoit ce, amman na san mahaifiyarta da kowa kai zai zarga, idan har Iya ce ai ita sai ka aura suke mutuwa wannan kuma tun kamin ayi auren ta rasu�

“Mai son abun ka ya fika dabara Ammy, bana iya gane komai a yanzu, ba zan iya cire Iya daga zargi ba, kamar yadda zuciyata ta kasa aminta da Zainab�

“Ka tafi gurin jana'izar kar ayi ba kai�

A hankali ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fice daga dakin, Ammy ta share hawayenta ta mike tsaye ta nufi dan karamin dakinta dake gefen wardrobe inda take canja tufafi, wani yadi marar nauyi ta saka ta saka Hijabinta sannan ta fito, sai kuma ta zauna bakin gadonta ta dafe kanta, babu wanda take tunani sai Hajiya Talatu, da Waziri duk da kasancewar ta san Baba Waziri mutum ne mai tawakkali sai dai be zama lallai Hajiya Talatu ma tai ba daman can ba son ta take ba balle kuma yanzu da zata ga kamar saboda za a hada auren yarta da Shattima ne ta mutu. Ammy ta kusan awa daya a dakin kamar mai kunyar fita, tana tunanin mikewa tsaye ta fita sai wayarta dake gafen gadon tai ringing, Hannu ta kai ta dauka ganin number Mama Fulani be bata mamaki a tunaninta ko zata sake wata maganar ko kuma ta fada mata cewar tana tafe.

“Ammy...! Yarinyar ta fada miki abun da ta fada min?�

“Kamar na me?�

Mama Fulani ta labarta mata kadan, sai Ammy ta sauke ajiyar zuciya.

“Ta fada min�
Chapter 138 · 0% Book details