Sashe 68
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Anjima idan Ammy ta shigo, zan sa ta duba maka takardun wasu filaye da gidajen da baka san da su ba, akwai kuma takardar da nai rubutu na wadanda nake bi bashi da kuma wadanda kasuwanci ya hada mu, zan hannata maka su ka aje inshallah�
Uffan Shattima be ce zai iya kara cewa ba ya mike tsaye.
“A tashi lafiya Mai Martaba�
Ya fice daga falon da sauri kamar zai tashi sama, be taba daukar haka wasiya take da nauyi ba sai a yau. Gaba daya jin yake duniyar na juya masa, ta ina zai fara ina zai sauke why mai martaba yai masa wannan wasiyar a yanzu.? Why him? Har ya iso bangaren Ammy kirjinsa be daina nauyi ba, ga zuciyarsa sai bugawa take kamar zata fito, nauyin ba kirjinsa kadai yake ba har a kansa ji yake kamar Mai Martaba ya dauki wani katon dutse ya dora masa a kai. Sai ya samu kansa a falon Ammy sannan ya soma tambayar kansa abun da ya kawo shi a falon, but he need to see his mother maybe ko zai samu saukin abun da yake ji. Hakan yasa ya nufi dakin yana kokarin tura kofar dakin ya shiga ya ji muryar Nana.
“Ni sai na tafi�
“Nana kina ganin rashin kunyar da kika min zai barki ki rayu in peace, kina min tsawa your own biological mother�
Tsaye yai jikin kofar yana kallon Ammy dake zaune kasa ta jingina da gadonta tana kallon Nana kamar Nana ce uwar ita ce yar.
“What is happening?�
Nana kamar mai jira ta juyo gurinsa da sauri ta soma masa bayani kamar zata yi kuka.
“Ya wai bikin yar Farin gida da ake wai Ammy ba zan je ba, kuma Amal kawata ce ita ce ta gayyace ni ita kanwar Amarya ce class din mu daya�
“Yaushe ake bikin?�
“Yau ake budar kan Amarya, kuma ba cikin manyan zan tsaya ba, ni gurin su Amal zan tsaya�
“Shikenan je ki fara shiri tun yanzu, zaki je anjima�
Da sauri ta rumgume shi tana murna.
“Thank Youu Ya I love you�
Ta sake shi sannan ta fice daga dakin cikin murna ranta fes tun da Shattima yace zata je. Sai da ta fice sannan ya nufi inda Ammy take ya zauna gefenta sai shi akan gadonta ya zauna tsabanin ita data ke kasa zaune.
“Ammy why kika hana ta zuwa?�
“Bata son makaranta, duk abun da aka ce tai ba zata yi ba, sai kuma a rika bin ra'ayinta ana mata yadda take so?�
Shiru yai yana kallon yadda idon Ammy ya cika da hawaye, sai ya ji tausayinta ya rufe masa zuciya.
“Amman idan kina irin kalaman nan marar dadi a gareta wani abu zai iya samunta, kuma still mu ne zamu shiga matsala, she's still young�
“Like a baby?�
Ta tambaya hawaye na sauko mata.
“Ina jin kamar ace Nana tana da wata uwar ba ni ba, da yanzu na maida ta hannun mahaifiyarta na gaji da wanne zan ji�
Ta fashe da kuka. Hakan yasa Shattima yaji damuwarsa ta karu, ya mike tsaye jiki ba kwari ya fice daga dakin domin ko kadan baya son jin kukan mahaifiyarsa. Dakin yaransa ya nufa or maybe zai samu peace of mind a can, Luma kadai ya samu a dakin tana ta bachi, kusa da ita ya zauna ya shafa fuskarta a hankali yadda ba zata tashi ba, sannan ya mike tsaye yana sauke ajiyar zuciya ya nufi gurin windows dakin wanda ke saiti da Garden din bangaren Ammy, tsaye yai jikin window yana kallon itacen dake garden din wani iska mai dadi yana bugunsa, hannayensa ya dora jikin window wanda hakan ya bashi damar hango Falmata dake zaune a garden din tana ta kallon wani gurin na dabam kamar mai tunani. A inda take tsaye na kasa baya iya hango na sama sai dai na sama ya hango na kasa.
Hango Sirleem da tai tafe yasa ta mike tsaye tana jiran ya karaso kusa da ita, tun daga nesa yake sakar mata murmushi har ya karaso.
“Naje daukarki Momy tace tasa Ameer ya kawo ki, na shiga bangarenku n karbi takardar maganin wata hadima tace min kina Garden�
“Eh ta bani maganin ma�
“Oh Momy akwai karamci sai da ta siya maganin ma�
Ya fada yana murmushi domin kadan daga halin Momy ne taimako da karamci ga tausayi da son mutane.
Ya kai hannu ya karbi maganin yana dubawa.
“Ta fada miki yadda za ki yi amfani da shi?�
“Eh ina son sai na je gida sai na fara idan zan kwanta�
“Amman dai yau ba zaki kai dare kamar jiya ba ko?�
“Sai yaran sun yi bachi tukuna�
Ya mika mata ledar maganin yana fadin.
“To ya kamata ki samu Mai Napep din da zai rika kai ki ya dawo dake, zan biya shi�
Kallonsa kawai take baki sake tana mamakin yadda yake da karamcin da son taimako har haka. Kamin tace komai yace.
“Ba ki ba ni labarinki ba fa�
Ta yi kasa da kanta, ba dan bata ji domin duk maganar da yake mata yan mata ne cikin daga muryar ta yadda zata ji, ba ita kadai ba har wanda ke kusa da su ma zai iya ji.
“Hey....�
Ya fada yana leken fuskarta. Sai ta dago ta kalleshi, ta sake maida kanta kasa.
HAJIYA BILKI POV.
Hajiya Bilki ta sauke ajiyar zuciya jin abun da Aminiyarta kuma matar Waziri wato Hajiya Talatu take fada.
“Wallahi kuwa�
“Ki ce kina cikin tashin hankali, to wai Waziri lafiya yake kuwa?�
“Ni ina na sani, sai wani fadar yake duk na sake yi ma dan da'uwansa kazafi a bakin aurena, ina zaman zamana zai dauko min wata masifar, wannan duk na Ammy na na sani, shi kuma baya iya musa mata tun da ta shanye shi, daga ni har Maijidda jiya ba mu runtsa ba, kuka kawai take�
“Ai dole tai kuka za akai ta ga halaka, yarinya tana zamanta za a aura mata mutuwa, Wallahi ki tashi tsaye karki yarda sam a kai ki a baro�
“Ai ba zan yarda ba, sai dai ayi wacce za ayi, amman ba zan Waziri ya aurawa Shattima yata ba, ko ana zaune kalar ai ba zan yarda ba balle kuma mutum ya zama maye, idan dama ta ki hagu zan koma, idan ta gwada be yarda ba be janye maganar ba, garin su mutanen nan zanje ayi masa asiri ya janye�
“Ai haka ya dace gaskiya, sai muje tare, kaji min tashin hankali�
“Wai sai fdar yake indai ba Shattima ya fasa ba Wallahi ba za a fasa auren ba, so yake yana aura masa ita ta mutu, waya sani ma ko Ammy ce take cinye masa mata, ko kuma can garin tsafe tsafensu suka kwaso wani mugun abu�
Hajiya ta dade tana magana da Hajiya Talatu kamin ta katse wayar shi M saboda shigowar Nana.
NANA POV.
Tana Fita daga dakin Ammy ta nufi bangaren Hajiya. Tana tura kofar dakin ta shiga sai Hajiya tai wa Hajiya Talatu sallama ta kalli Nana tana murmushi.
“Daughter�
“Na'am Hajiya dan Allah wayarki zaki ara min na kira driver na�
“To gashi�
Ta mika mata wayar, Nana ta kai hannu ta karba ta fice daga dakin tana nemo line AA call list din Hajiya domin bata yi saving number ba. Bugu daya ya dauka.
“Hello�
“Sardauna�
“Na'am�
“Ka shirya anjima da 8 ka zo ka kai ni gurin budar kan Amarya�
“Okay�
“Karka wuce 8pm�
“Okay�
**
Ya amsa mata tare da sauke wayar tare da saka ta aljihu sannan, ya marasa cikin gidan yana nade wandonsa.
“Anti wanki da yamman nan�
“To kayan sun yi datti, kai kuma ba zama kake ba�
Hannayensa ya jefa cikin ruwan ya soma taya ta wankin, daman can idan tana wanki ya kan taya ta ko kuma yai mata, kayan su Khaleel da Aymana duk shi yake wanke wa, har girma yana mata idan yan kwarai na saman kai, ko kuma ya mata rabin girkin ita kuma ta karasa. Sai da ya fara dauraye tufafin yana shanyawa sannan ya dauko mata wani labarin.
“Anti ina tunanin komawa makaranta fa�
“Makarantar lafiya? Ni ba ni da kudin biya maka makaranta yanzu, kai kuma ba aikin wahala kake so ba balle ka taimaki kanka�
“Ai wani aikin zan samu mai soka soon, zan gyara gidan nan na masa fenti na saka masa tayis na siyo miki gas, ke har makka sai na kai ki na siya miki mota, su Khaleet na saka su makarantar kudi, komai zai zama normal...�
Kallonsa tai.
“AA baka rabu da yarinyar nan ba ko? So kake ka jefa kanka a matsala ko?�
“Ni fa na rabu da ita bana tare da Ita sam sam sam�
“Ya dai kamata ace idan nai maka magana ka ji, idan na ce ka bari ka bari, ba ka da wanda ta fini a yanzu, baka da gata sai ni, kasan bamu da kowa sai Allah, idan ka shiga wani hali aka kama ban san ya zan yi ba, aje min wankina�
Ya kalleta a sanyeye.
“Ba maganar yarinyar nan ba ne Anti�
“Ni dai ka aje min wankina�
Ya cire hannunsa ganin da gaske take domin babu alamar wasa a maganar ta balle kuma a fuskarta. Wannan abun yake tsoro ya dade yana son labarta mata ko kuma sammata wani abu amman yana tsoron abun da zata fada, domin shi kansa ya san ba shi da gatan daya wuce Antinsa a yanzu, ita ce uwarsa ita ce ubansa ita ce komai nasa.
“Ka rika taka tsantsa da rayuwa AA, neman kudi ba hauka ba ne bana son ka jefa kanka a matsala, na rasa uwa n hakura, na rasa uba na hakura, na rasa miji na hakura, yanzu kam bana jin idan na rasa ka zan iya rayuwa, kai kadai ka rage min, ni ma ni kadai na rage maka, ya kamata ace idan na maka magana ka ji, ka san irin wahalar da muka sha kamin mu kawo yanzu, kasan irin fadi tashin da nai kamin na samu na gina kaina, muna zaune cikin rufin asiri kana kokarin jefa mu a hadari?�
“Idan akan yarinyar nan Allah ya min arziki, ba fa akanta ba ne�