Sashe 75
Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta fada a ranta tana mutsika masa ido tana masa alamar yadda zai gane. Shi dai kam be fahimci komai ba hakan yasa ya maida hankalinsa gurin Liya.
“Ina magana tana magana saboda an daure mata ta yi yadda take so a masarauta, mi zai saka na fadi abun da ba shi ba a gaban Shugaba? Ya zama lallai sai kun san kowa a garin nan ba, amman lallai ne kowa ya san ku�
Ya fada da yarensu yana watsawa Liya wani mugun kallo. Hannu Sarki ya daga sai tsohuwar taja baya ta nufi wani guri daya fi kama da bukka a cikin fadar, bata dade ba ta fito rike da ture wanda ke dauke da soyayyen nama, ta mikawa Zainab.
“Ci�
Ta fada da yarensu, Zainab ta kai hannu ta dauki yanka daya da sauri ba dan ta san abunda ta fada ba, jiki na rawa ta kai bakinta ta tauna ta hade, daga lokacin ne gaban Liya ya fadi ganin ba tai komai ba. Tsohuwar ta matsa da naman kusa da Fadime.
“Ci�
Tana fadin haka Fadime ta kalli Wasim da sauri, sai ya amsawa tsohuwar da yarensu.
“Bata cin nama�
“Na yau ne kawai, kuma umarnin Shugaba ne, ci�
Ta karasa tana kallon Fadime, da sauri Fadime ta kai hannu ta dauki yanka daya tana kuka ta kai bakinta, bata ko tsaya tauna shi ba ta hadiye. A take ta ji wani abu ya taso mata tun daga cikin cikinta ya nufo makoshinta, wani irin kaikayin bala'i ne ta ji a makoshinta, daga Wasim har tsohuwar da Sarkin da Liya kallonta suke.
“Wacan ta mu ce wacan bare ce�
Tsohuwar ta fada tana nuna Fadime, tana yin baya-baya, wani irin ihu Fadime ta saka ta rike makoshin tana kuka.
“Wayyo kaikayi wayyo Allah kaikayi�
Da sauri Wasim ya maida ita bayansa, yana kallon Mahaifinsa, Zainab kam mutuwar tsaye tai a gurin ganin ita ta ci be mata komai ba, amman ga Fadime rike da makoshi wasu yawu masu yauki na mata zuba kamar kubewa sai kuka take tana wani irin tari, tana yagar wuyanta da yatsun hannunta. Murmushin jindadi ne ya fadada kansa a fuskar Liya tana kallon yadda Fadime ke tari tana susar wuya cike da shauki.
“Errugabea da, nire errua da ez dakiela ezer, tira egin nion�
“Bata da laifi, laifina ne bata san komai ba, ni na janyo ta�
Ya fada yana ta kokarin tare Fadime daga kallon da Sarkin ke mata. Hakan da yai kadai ya isa ya karantar da Sarkin cewar son ta yake.
“WASIM...!�
sarkin ya fada yana gyada kai a hankali tare da kara hade rai kamar bakin hadari, Fadime kam faduwa tai a gurin hankalinta na kokarin bacewa saboda kai kayin bala'i da take ji a makoshinta, Wasim ya duka da sauri ya rike ta. Zainab na tsaye a gurin tana shafa wuyanta ba dan tana jin komai ba sai dan tambayoyin da take da su.
NANA POV.
Wani irin murmushi take tana kallon kanta a madubi, ita kanta ta san ta yi kyau matuka red gown din dake jikinta ta haskata, daman can Nana ba mace ce mai son doguwar kwaliya ba, hoda ce kawai a fuskarta sai jan baki data shafa. Mikewa tai tsaye ta dauki purse dinta ta saka takalminta sannan ta nufi kofa tana takawa kamar wata Amarya. Ko da ta fito babu kowa a falon Ammy hakan kuma ba karamin dadi yai mata ba, sai ta nisa ta hanyar da Ammy take hana ta fita, da sauri sauri ta rika tafiyar gudun kar ta hadu da Ammy ta hana ta zuwa budan kan. Tana isa cikin fadar Ammy ta bude kofar ta baya ta fita. Daidai kofar AA ya faka motar, daman tun 7:40pm ya iso ya aika wata Hadima ta fada mata ya iso sai ta umarce hadimar ta fada masa ya dawo ta kofar fadar Ammy. AA na ganin Nana ya fito daga motar yai tsaye yana kallonta, gaba daya ta sake ta masa mugun kyau kamar ba ita ba, abun ka da marar jiki sai sigar ta kama jikinta kamar wata yar tsana. Ita kanta kallonsa take domin yayi kyau fiye da kullum ba zaka ganshi ka ce direba ba ne dan masu kasa haka ya fito. Murmushi ta sakar masa ganin yadda yake kallonta, sai shi ma ya mayar mata da murmushin ya bude mata gidan baya, saukowa tai a hankali ta shiga motar sai ya rufe ya bude mazaunin direba ya shiga ya zauna, sai ya samu kansa da rashin natsuwa har sai da ya juyo ya kalleta, be taba ganinta da kwaliya ba sai a yau, ashe haka take da kyau? Ya raya a zuciyarsa.
“Kin yi kyau�
Ya furta a fili yana jin wani irin girmanta na kama shi, duk sai yaji ta zame masa kamar ba ita ba ya ji nauyinta na sauko masa.
“Na gode kai ma ai ka yi kyau�
“Thank Youu, ina zamu je?�
“X&L Hotel�
Ya juya yana shakar kamshin turarenta daya cika motar ya bata da na shi karamin turaren. Madubin motar ya saita ya juya ta inda zai rika ganin fuskarta sannan ya kunna wutar motar ya kunna ac. A hankali yake ta tuka motar yana satar kallon Nana ta madubin motar, a duk lokacin da suka hada ido sai ta saka masa murmushi. Daga ita har har shi babu wanda yai wata magana har suka isa.
X&L Hotel babbar Hotel ce a garin Yola, wanda manyan mutane suke zuwa yin taro ko biki ko sauka idan ta kama, ko kuma shakawatawa.
A harabar Hotel din ya faka motarsa sannan ya fito ya bude mata ta fito.
“Zaka shiga ciki?�
“Ana bari a gashi?�
“Yes zan ce kai bodyguard dina ne�
“Okay�
Ya rufe motar yana jindadi, daman can ya dade yana son ya shiga gurin domin ya dade yana jin labarin Hotel din sai dai be taba zuwa. A maimako tai gaba ya bi bayanta sai ta tsaya ta jera tare da shi, yadda ya ci ado ita ma ta ci sai abun ya bada kala kamar saurayi da budurwa, a tare suka doshi wata karamar hanya da aka kawata kamin su karasa wani saurayi ya kira sunan Nana, da sunan da Zainab take kiranta da shi.
“Baby�
Nana ta juyo tana arba da saurayin ta washe hakora ta doshi inda yake, AA kuma ya tsaya a gurin yana kallonsu, side hug tai masa suka gaisa.
“How are you?�
“I'm fine, kai ma ka zo biki�
“Yeah friend din mu ne zai yi aure, amman mu ba ciki zamu shiga ba, waya kawo ki Sirleem?�
Juyawa tai ta kalli AA a ganin be cancanta ta kira direbanta ba a yadda ya ci gayun nan.
“No wani ne�
“Okay sai mun hadu ciki�
Ya fada yana sannan ya nufi hanyar shiga gurin. Ita kuma ta juyo ta dawo gurin AA.
“Mu tafi�
“Ba zamu je din ba�
Ya fada yana watsa mata harara.
“Me akai?�
“Ya zaki rumgume wani kato da ba muharramin ki ba�
“To ai cousin dina ne�
“Ba cousin ba kwarkwata, bari na sake ganin kin rika hannun wani sai na fasa miki kai�
Ya karasa da kwafa ita kuma ta turo baki.
“To Wallahi zan ma koreka daga aikin�
Ya kwaikwayi muryarta yana yatsina fuska.
“To Wallahi zan ma koreka daga aikin�
“Kuma karka bi ni ciki, ba zan shiga ba�
“Wallahi sai na biki, sai na shiga, kuma muna shiga ciki kika ga wani kika masa magana sai na bata miki rai�
Ya fada with serious face, yana kara hade mata rai kamar irin shi ne boss ita take aiki karkashinsa. Tana yin gana ya bi bayanta sai ta juyo tana turo baki.
“Ka daina bina�
“Sai na biki kuma ki kaiwa wani namiji magana sai na bata miki rai�
Wani irin abu taji kamar ta saka kuka, sai kuma ta juya ta cigaba da tafiya yana binta bayanta har suka isa gurin. Bata nuna gate pass din ba sai kawai ta fada masa sunanta.
“Nana Aisha Abdallah Jari�
Da sauri ya bude mata kofar ta wuce AA ya bi bayanta yana fadin shi bodyguard dinta ne. Kato dakin taro ne da aka kawata da ado na zamani ga haske ko'ina kamar rana, mutane ta ko'ina kana ganin bikin kasan na manyan mutane ne. Kusa da kofar AA ya tsaya Nana kuma ta fara raba ido tana kallon mutane, ta nan ta hango Hajiya Babba cikin matan manya sai far'a take ana ta fira, can kuma ta hango kawarta Amal, da sauri ta nufi inda suke Amal din na ganinta ta rumgume ta tana murna kamin ta ja mata kujera ta zauna, duk abun da suke idon AA na kanta ita a tana yi tana satar kallonsa, tana son ta bar kujerar ta koma wata inda take hango wasu friends nata, da zarar ta mike tsaye sai AA ya bata mata fuska na babba da yaro sai ta koma ta zauna tana watsa masa harara tana turo baki. Sai da ya tabbatar ta natsu sannan ya fita daga gurin ya koma cikin motar ya zauna.
Kari aka fara yi ma Amarya wanda hakan yasa su Amal din tashi ita da kawayenta, suka nufi gurin Amaryar aka bar Nana ita kadai, wata kawar Amal din ce mai suna Rukayya ta dawo gurin ta aje handbag dinta ta cire sarkarta ta zinari ta saka a jakar.
“Sis dan Allah zan bar jakata a nan ki kula min, sarkar tana damuna ne�