← Book details Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 172

Sashe 57

Fulani Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amo kallonta kawai take, kamin ta mike tsaye ta shige bukkarta, tukunyar tsafinta ta dauko ta sake turawa Fadime wutar sannan ta fito ta zauna tana kallon yadda Fadime ke alwala hankalinta kwance ita kuma tana jinya. Sai da Fadime ta gama alwala sannan ta mike tsaye tana yar waka kamar ba alwala tai zata yi sallah ba, da gangan take yi wai domin Amo ta kara jin haushi, dan ta yi arba da irin hararar da Amo ke watsa mata. Dakinsu ta shige ta shimfida buhu ta soma rama azahar sannan ta gabatar da sallah la'asar. Tana gamawa bata ko tsaya yin addu'a ta cire tufafin jikinta ta dauko na gadonsu ta saka ta fito tsakar gidan ta dauki tulu.

“To Allah ya tsare ya miki albarka kuma ya shirya na natsar dake�

Inna dake aikin wanke hannu ta fada, sai da Fadime ta kalli Amo sannan ta amsa da amin, sai kuma ta aje tulun ta shiga dakin ta bude ladar kazar ta dauko cinya daya ta boye a zanenta ta fito ta dauki tulun ta fice.
Amo na ganin ta fice ta unkura cikin zafin ciwon da karfin hali ta shiga bukkarta ta dauko wani magani mai kamar laya ta saka a baki ta tauna, sannan ta fito.

“Kar wanda ya shiga bandaki ina ciki�

Ta fadawa Hajjo sannan ta sabi buta ta shiga bandaki. Ba komai za tai ba so take ta bi bayan Fadime ta ga abunda take idan taje diban ruwa da kuma yadda wutar take barin jikinta. Tana shiga bandakin ta fara karanta wasu abubuwa tana karkada halshe ta birkice ido, a nan da nan jikinta ya fara gashi sai ta fadi a kasa ta kafa hannayenta da kafa kamar yadda dabbobi suke, cikin kankane lokacin gashin kyanwa ya maye jikinta gaba daya sai ta soma kankancewa ta zama bakar mage sai jajayen ido. Tsalle daya tai ta tsallake zanar ta dira waje, ta bi hanyar dajin tana tafiya daker dan ba karamin duka ta sha ba jikin kuma be isa saki ba, tafiyar ma kadan kadan take yinta.

Fadime tana tafe tana tunanin abunda Amo ta fada cewar sai ta fada masa halinta.

“Ai daman yace ya fasa, shikenan sai na tsaya a dake ni gashi nan ma ana mata tausar tuwon kasa, waya sani ma ko mayyar ce da gaske�

Duk taji haushin abun da faru gaba daya, Ra'ees yace ya fasa gashi kuma Amo tace zata kara lalata abun, idan ma ta tuna da Wasim sai ta ji haushinsa dan shine yasa muryarta ta yi katuwa har suka gudu ba dan shi ba da yanzu komai be faru ba. Allah ya gani kazar nan ma ba dan tana son masa kuri ba da ba zata je da ita inda zai gani ba, amman tana son nuna musu kazar shi da Ma'u dan su san ba wai farinjini ne bata da shi ba.
Sai da ta fara isa gurin ruwan ta fara ciko da zimmar idan ta cika sai ta je gurin duwatsun tai magana da shi, sai jin takunsa tai a bayanta kasancewar gurin babu mutane domin yamma ta yi kuma ana fadar dibar ruwan yamma da kuma rana tsaka be da kyau. Da sauri ta juyo sai ya sakar mata murmushi, mikewa tai tsaye tana kallonsa.

“Munje birni dazu�

Jin be ce mata komai ba sai kallonta yake yasa ta cigaba.

“Na hadu da wani saurayi ya siya min kaza�

Hannunta ya rika sai dai be yarda ya taba tafin ba, yaja ta suka zauna kan wani karamin dutse dake gurin.

“Fada mim yace yana son ki?�

Ta yi shiru sai ta ciro naman kazar ta mika masa.

“Ga shaida nan ka gani�

Dan murmushi yai ya bude mata bakinsa.

“Ba ni na ci�

Ta zare ido.

“Kai idan aka gan ni ina baka abinci sai a fadawa Bappa, gashi nan kuma baka da riga sai ace wani abu ne�

Murmushi yai gyada mata kai, can kuma sai ta waige ta ga babu mai ganinsu ta balli naman ta kai masa a baki. Bude bakin yai ta saka masa babu wata kyama duk kuwa da irin kyamar da yake da shi, sai ya fara tauna naman sannan ya kai sannunsa ya cafko wutar bayanta.

“An sake saka miki wutar nan�

Fadime ta waiga da sauri ta kalli hannunsa dake ci da wuta, ba shiri ta jefar da naman hannunta ta mike tsaye.

“Kai ne dai kake saka min ita�

Ya kalleta da fafaren idanuwansa ya jefar da wutar.

“Ba ni ba ne�

“To waye? Miyasa ake saka min ita?�

Mikewa yai tsaye ya shafa kanta da babu dankwali.

“Saboda karki yi albarka, wannna wutar ta maita ce�

“To minene ma yasa mayun suke bina suna saka min wutar ne?�

Murmushi yai ya kai dayan hannunsa ya shafi gefen fuskarta, sai kallonta yake kamar zai cinyenta.

“Ana sakawa mutum ita ne saboda kar yai albarka, komai kike samu ko kika rika sai lalace, idan kana makota da maye ko kuma ya saka maka ido, to zai saka mata wutar ne tai ta binka tana cinye duk wani abu da ka mallaka, idan kuma be saka maka wutar ba zai saka maka ciwo har dukiyar dake tare da kai ta kare, shi ma idan ya gagara cinka ne, mayu suna da hassada basa son su ga wani yana samun wadata saboda mafi akasari su matalauta ne, masu siyar da kurwa ne kawai suke arziki wadanda basa ci sai dai su siyar ko kuma suna ci suna saidawa, ko baiwa ko basira maye ya gani a tare dake zai kwasheta ya jujuta miki kwakwalwa, idan maye ya ci mutum dubu sai ya zama sarkin mayu, daga lokacin ne mayen baya iya sake cin mutun sai dai su koma bada maganinsu saboda sun san lagonsu, mugun ya san makwancin mugu, idan kuma maita mutun ta gawurta, ko dabba ya kalla ya kwallafa rai zata mutu, ko gini kai idan maye baya so yana kallon ginin zai zube sai idan ka gagareshi, idan kurwarki tana gurin maye zai ta miki waibuwa yana saka ki kalar mafarkin da kike so, idan kuma suka aje miki aljani a daki to zasu rika jin inda kike neman magani da inda kike ajewa sai su bata shi ya gagara yi miki amfani�

Tun da ya fara bayani Fadime take masa kallon tsoro idonta a waje.

“Kai ma maye ne?�

Ya girgiza mata kai yana sake kai hannunsa ya shafa gashin kanta.

“Mu garin mu ba a maita, sai dai muna tsafi sosai, amman ba mu yarda da ayi maita ba, saboda ba ma yarda mu cutar da yan'uwanmu, idan mutum yai mata korarsa ake a garin ko da shi din sarkin garin ne, mayu har yayansu suke badawa saboda ana adashe tsakanin junansu, idan aka ci dan wannan idan za ayi kwasa na wani za a ci, duk irin son da kake ma dan dole ka bada, idan kuma aljanin maita ya bukaci ɗan ka da kansa dole ka cinye danka ko da kuwa kana kana son shi, mayu basa son tsagera, sun fi son matsoraci da mai yawan kyautata musu, matsoraci kurwarsa tana kwantawa ne guri daya har su samu nasarar kamawa babu wata hala, kama ma mai yawan kyautata kusu kullum yana tare da su, kamar kaza ne a cikin keji idan ka tashi yankawa cirota kawai zaka yi, tsarega kam yana musu wahalar kamu saboda kurwarsa bata zama a guri daya kuma baya shan inuwa daya da maye, wani mai aljanu ma wanda aljanunsa suka fi na maye a take zai tona musu asiri, sannan maye be son tsarguwa, idan kika matsa masa zai tashi ya bar miki guri, idan har makocinki ne, ko kuma ya baki maita ki ci a asirce bani sani ba ki kamu da ita, kowa kuma da yadda yake kama kurwa, wani lasowa yake, wani sai ya miki kyaface da hannu wani sai jikinsa na taba naki, wani sai ya baki abu kin ci, wani sai ya shiga innuwarki, wani sai ya baki abu kin karba ko kuma kin bashi a lokacin ne zai samu damar jan kurwarki izuwa gareshi, wani sai ya miki magana kin amsa, wani kuma da ido zai janyo kurwarki, akwai wadanda basa gashi, amana basa tsawa soyawa ko gasawa, irinsu sun fi hadari su da masu saidawa domin idan sun sayar yana da wahala wanda aka saidawa ya dawo da ita duk kuwa da irin azabar da za ayi ma wanda ya kama kurwar, wanda baya gashi kuma take daya kama yake yankewa ya cinye mutum ya mutum, irin su idan suka kama ba zaka wuce kwana daya ba ko wuni wani ma awanni zaka mutu�

Gaba daya jikin Fadime yai sanyi, tun dai tana gane bayanin nashi har kwakwalwar kanta ta fara kwancewa yanzu kam jinsa kawai take bata gane komai ba, sai dai abunda ya faru a dazun da Amo ya dawo mata a rai wata kila da gaske Amo mayya ce.

“To ni wa yake saka min wutar? Minayi?�

“Baki yi komai ba, ban fada miki maye yana da hassada ba? Idan ma suka gagara cin kurwarka suna mata duka su daddake ta mutun ya koma musaki ko mahaukaci ko wawa ko kuma ya koma kwance da rashin lafiya, amman daga yau ba za a sake saka miki wutar maitar ba, ba zan sake bari a cutar da ke ko yatsa ba zan bari wani ya nuna miki ba kowa kuwa�

Ya fada yana kallon cikin idonta fuskarsa na nuna alamar babu wasa a maganarsa. Juyawa yai baya ya kalli wata bakar mage dake labe cikin itatuwan masara tana kallonsu sai ya nufi inda take Fadime dai binsa kawai tai da kallo.
Amo na ganin ya nufota hankalinta ya tashi tana son ta gudu ta kasa, sai ta ji kamar ma yana kiranta yana nufota tana tunkararsa har ta kai kanta gurinsa ta duka ya kamata ya birkiceta ya nade hannunsa ya sakar mata kulli a ciki sannan ya saketa, kasa tashi magen tai a take ta fara aman jini Wasim na ganin haka ya juyo ya dawo inda Fadime take tsaye.

“Wannan magen ina ganinta idan ina kiwo tana bibiyata, har a mafarki wani lokaci ina ganinta�
Chapter 57 · 0% Book details